← Book details Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 24

Sashe 16

Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai mujaheed yake zubawa daddy godiya, ragowan keys din daddy yadaga yace "wan nan kuma makullan gidan safiyya ne dazata tare gobe insha Allah kuma acanne za ayi walima ta karshe amika amare dakinsu wan nan gida daga yau yazama mallakin safiyya ita kadai Ga wasu karin shedun ma a rubuce" dakanshi yaje ya danka mata takaddun gidan ta da mukallan sannan yabawa muhammad nashi takaddun gidan daki fah ya kacame kowa jinjinawa daddy yake da godiya a garesa kowa zuciyar sa ta mamaye da farin ciki Da wannan abun al khairi din da yayi....

TAKU A KULLUM NANA BMB

08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: ❣ RABON KWADO....!!

BOOK 3

NA NANA BMB

GARKUWA WRITTER'S ASSOCIATION
{ Marubuta masu garkuwa da alkalami domin fadakar da al'ummah }

page 43 - 44

WASHE GARI

Alhmdlh jikin safiyya yayi normal ta tashi garau, hankalin daddy yakara kwantawa shiko takan Dr bayabi kogidan yaki komawa sabgarsa kawai yake,
Harseda rana tafito tukunna amarya tasoma motsawa alamun zata tashi, to motsin da takeyi ne yasa muhammad farkawa shima, ahankali ta bude idanunta tasaukesu kan faffadan kirjinsa, hakanne yasata fiddo idanuwa waje tana kokarin mikewa sedai tsam hannuwan sa suna ta bayanta bahalin mikewa, koda yabude idonsa ya kalleta ganin abinda take shirin yi, idonsa ne yakai kan time yaga 8 ma ta gota zaro idanu yay yamikar da ita, ganin babu sutura ajikin tane yasata sakin kara tai kasa tana kare kirjinta, haushi hakan yabawa muhammad kawai ya harare ta yashige bathroom yana cije baki sauri sauri yayo alwala yazo ya tada sallah ita kuwa tana zaune gefen bed din ta nade jikinta da blanket koda ya idar yajuyo yana kallonta diriri cewa tayi saboda tayi tunanin zece ta tashi tayi sallah ne, murmushi yayi yace." Ay nasan bakyayi kwantar da hankalinki bacewa zanyi jeki sallah bah " meenal koda tajee haka wata irin kunyace takara lullubeta hakan ya sa ta shigar da kanta cikin bargon, sam batayi tsammani ba taji ya jaye bargon gaba daya daga jikin ta bayan ya zare jallabiyyan dayasa, takuwa rintse idanun ta ta cukurkude guri daya sunkuyowa yayi yana kare mata kallo yace." Sweety banace kidena jin kunyata bah, banason hakan" sam kasa tanka masa tayi ko idon nata takasa budewa.

" ' Hmmmm! bazaki dena bah kenan, to bari kigani"

Ay kafin ta bude baki tayi magana ta sureta ya azata a gado, cikin kwalalo idanu tabudi baki zata kumayin magana ya cafke lips din nata da nashi, sotake kawai takwaci bakinta takasa hakanne ma yasashi zura hannu ya balle bra din tata sakin bakin dayayi ne tasoma maida numfashi cikin sauri murya na rawa tasoma cewa." pls ya muhammad" magiyan ne bayason jima yasa hannunsa kan bakin nata ko ina najikinta yake kai bakinsa mussam man breast dinta daya kusa zautashi,

Sam besan iya adadin lokacin daya daukaba yana sarrafata son ranshi, tukunna ya barta yamike yashiga bathroom abinsa donyin wanka, ita kuwa luff tayi taname zubar hawaye don haryanzu takasa yadda ya muhammad din tane yake mata haka, yajuma a bathroom din tukunna yafito daure da dan guntun towel yazo har inda take cak ya dauketa izuwa bathroom din ya ajeta yana murmushi ganin takama idanu ta makale yace." To sarkin kunya ayi wanka a fito koh"

Juyawa yayi yarufe mata kofar yasoma shiryawa harya gama shirinsa yafita takasa fitowa yana sane da ita yafice kawai abinsa, tanadena jin mitsinsa kuwa tafito cikin sanda tana leke don batajin zata iya hada ido da ya muhammad din nata yanzu,shikuwa koda yashiga gidan nasu yata rar 'yan tafiya anata shiri, bakaramin farin ciki yayiba ganin auntie safiyya anata hada hada da ita, hasana ya tambaya ina hasan da usain ne? take shaida masa ai nasuma tashiba, Da mamaki ya jinjina kai yace." Lallai ne yaranne dole"
Yajima yana knocking kafin su bude masa kofan, yana zura kai yaga usain a tsaye daganin shi yanzu yatashi, haba ya rike yace." dakyau 'yan hutu ayse a tashi haka koh, anata shiri ku kuma kuna nan kun jibge"
Hassan nadaga kan bed yajiyo maganar ta muhammad, yana murmushi yace." Ay dole tunda ango yatashi yanzu kowama zai tashi" tura kofan yakarasa yi yashiga yay kanshi hassan yamike da gudu yashige bathroom yana dariya, usain yace." mara kunya da katsaya babban yaya yayi maganinka," murmushi kawai yay yafita yabasu guri, suna azune a parlour anata hira lokacin nana tafito itama, har tazauna muhammad yana kallon ta muryanta ma baya fita sosai data gaisheshi,

" Zonan nana" shine kawai abinda yace da ita, kanta a sunkuye ta taso tazauna gefensa koda yarike hannunta zafi yaji sosai a hannun nata tausayin tane yakara kamashi murya a sanyaye yace

"Kinason yin magana da auntie ne?" hawaye ne suka zubo mata ta girgiza masa kai, hannun nata kawai yarike suka mike tsaye yana cewa "tashi muje" saurin kallon sa tayi amma se bekula taba har suka kai bakin kofah sukayi karo da safiyya,da mamaki take kallonsu tace "ina zaku haka" dan guntun murmushi yayi yace.
" Zata gana ne da mahaifiyar ta kafin a kaita gidan miji kada zafin yamata yawa" saboda duk abinda ke wakana tsakanin ta da yousep yana gani,
" Yayi kyau hakan sosai, ay nayi magana da yousep din yace yau da yamma ze turo a tafi da ita, yanzu dai rakitomin wani abu nasaka mutafi don bazan bari ku tafi ku kadai bah"
Sakin hannun nana yayi yakoma palour din sam barka yana shiga yaci karo da wani hijab yadauka abinsa yaje yakai mata suka shiga mota suka tafi su ummi basusan meke faruwa bah,
Abin mamaki suna shiga gidan suka ganshi dankam da mutane har sama suka haye safiyya kuwa tasha nuni aka fara nunata, daddy da kawu musa suka gani a bakin kofar dakin na Dr sunata bugunta amma ko gezau kofan yakiyi, da kallon tuhuma daddy yasoma binsu amma se sukayi kasa da kansu don karma su hada idanu, 'yan uwan Dr kowa yana zaune jugum jugum, cikin ikom Allah da muhammad ya tayasu bugun kofan da temakon wani karfe kofan ya budu, suduka tsayawa sukayi kallon dakin nata yadda yayi kaca kaca da glasses komai an hargitsa shi haka suka kutsa kansu ciki can gefen bed suka hangeta wanwar a kasa kamar matatta, ga ciwukan dake jikin ta jini dukya bushe, sungumar ta daddy kawai yay suka sauko kasa kowa ya hangosu se salati dakifah ya kaure wasu na kuka wasu na salati safiyya kuwa tasoma shan zagi ay matar sace tajawo ibar albarka iri iri sedai bawanda yabi takan suma nana kuwa kankame safiyya tayi tana kuka me tsuma zuciya har suka fita motar su daddy na tafiya safiyyan tace da muhammad su bisu kawai, yadata mota kuwa suka rufa musu baya, sunjima a wajen hospital din tanata kallon shi abubuwa da dama suna dawo mata, lokacin da fahaifi meenal a cikin sa itama a hankali hawaye yasoma bimata fuska kafin sushiga ciki, a office din Dr bello suka sami daddy yana masa bayanin akan halinda auntie take ciki, shigowansu ce tasashi dakatawa suna kallon su,magana zeyi tayi saurin cewa" pls kabarmu kodan nana mah" dauke kansa kawai yayi don beso zuwan su hospital din bah, zama sukayi jikin safiyya a sanyaye ta kalli Dr din tace." Ya jikin nata yanzu Dr meke faruwa da itane haka?"
Kallon daddy Dr bello din yayi, shikuma yay masa a lama daya cigaba da magana kawai,

" Maganar gaskiya tabbas Dr maryam tana cikin hadari sosai da alamu akwai abinda yamatukar firgita mata rayuwa harya so taba mata kwakwal warta domin har zuciyan ta tana cikin hadari Allah ne yay da tsawon cin kwanan ta a gaba zuciyan ta bata bugaba gaba daya, a takaice dai yanzun bazan iya shaida muku yanayin dazata farka bah zata iya yiwu wa hankalin nata ya gushe, so amma indai aikin da mukayi mata anyi nasara zata tashi lpy dayar dar Allah"
Kuka safiyya tafara tana share hawaye tana cewa " Allah sarki wlh danasan abinda ze faru dake kenan sam da bandawo Nigeria bah, duka nice najawo miki wan nan bala in" mikewa daddy yay yakamo hannun ta seda sukazo bakin kofa tukunna ya kalli muhammad yace." Taso ka kaita gida, bakuma nasan hakan yadaga miki hankali don banason wani abu yasame ki koda wasa kada nakara ganin hawayen ki a kan wan nan abinda yake faruwa"

Jikin muhammad a sanyaye yazo yakama mata hannun suka fita taname zubar hawaye, nana kuwa tana zaune hawaye ne kawai ke silalowa daga idanunta ko baki takasa budewa tayi kukan ma.
Koda suka koma gida ummi harda hara rar safiyya saboda takira muhammad yagaya mata komai dake faruwa magun gunan ta ta dauko ta bata tasha ganin yanayin da take ciki cikin damuwa tasoma cewa." Haba safiyya akanme zaki sawa kanki damuwa akan waccan azzalumar matar akan me ma zaki damu, ay dole dama bazata gama da duniya lpy bah, somin tabine wan nan bataga komai bama" da mamaki muhammad yake kallon ummi irin kalaman dake fitowa daga bakinta tun anan yasan tafi auntie safiyyan su zafi,koda mujaheed yaji abinda ke faruwa shima jikin sane yay sanyi nan danan gida kuma ya dauka da maganar,
Safiyya bata dena hawaye bah har daddy yadawo daga hospital din,anan yake shaida musu duk wanda yakeson zuwa bauchin ya shirya a tafi dashi saboda anfasa kai nana yau sakamakon abinda yafaru da mahaifiyar ta, ada yadda aka tsara biyu aka raba abin wasu suje kai nana wasu kuma suje kai mimi, kiran safiyya yayi ya kwantar mata da hankali sosai san nan tadan sami nutsuwa,
Hassan da usain da nabiha daddy cayay sutafi gidan muhammad su zauna kafin sudawo kada kuma su kuskura su sanar mata abinda yake faruwa,
Biyu da wajan rabi aka dunguma 'yan tafiya akayi bauchi bayan angama shirya amarya tsaf tanata kuka mimi domin ganin abin dai yi za ayi suka dauki hanya,da iyalan sameer dasu innah da mummy se 'yan adamawa amma badukan suba ummi da safiyya, yanata musu Allah kiyaye don shi bandashi za ayi tafiyanba,
Chapter 16 · 0% Book details