← Book details Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 24

Sashe 6

Rabon Kwado Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

NA NANA BMB.
🤍❤️🤍❤️
page 12- 13
Suna tun kararta tana jadabaya cikin firgici numfashinta yan shirin daukewa saboda tsoro tana girgiza kae tana cewa baze yiwuba impossible meyake shirin faruwane? dakkyar take iya fusgo numfashinta motan data cikaro da itane ta baya yasata tsayawa taname dafe zuciyanta,
Cikin tsananin mamaki meenal tariketa tana cewa auntie lpy meyake faruwa dake haka?Ummi batabi takan yanayin da auntie tashigaba saboda itama a kidime take hannunta zata rike aikuwa tafasa wata irin kara taja gefe, cikin zubar hawaye ummi tace mekikeyi haka ina mahaifiyarta take kugayamin don Allah,jiki asan yaye meenal tace Ummi, itace mahaifiyata fah! mekike tunani akanta meyake faruwa? naga auntie kamar bata cikin hayyacinta,
Da mamaki Ummi take kallon meenal,tace itace mahaifiyarki fah kikace!meenal tadaga mata kai cike da mamaki,sam Ummi batasan sanda ta cakumi auntie bah cikin kuru kuru da idanu tace, bazan yardaba karyane,wlh bagaskiya bane sekin fadamin inda 'yar uwata take bake kika haifetaba karya kikeyi sekun gayamin gaskiya yau, saboda meenal jini nace ita zancenku karyane cikin hargowa take magana da fitar hayyaci tuni auntie tadade da sumewa, tayi yaraf kan mota din amma dukda haka Ummi jijjigata take tana cewa karya kikeyi kitashi sekin gayamin gaskiya zan kyaleki,
Kuka meenal tafashe dashi jin wani batu daya daure mata kae, alokacin abbansu yakaraso, inda Ummi taketa faman yagulan auntie yasoma kokarin janyeta daga jikinta, sedae bakaramin riko tayiwa Dr bah 😄😄😄, cincin karfinsa yasa ya bambare hannunta ajikin auntie yana gama janyeta kuwa tafi jikinshi ba alamun numfashi atare da ita,
Gaba daya mutanen gurin nan mamaki da al ajabi ne suka hanasu koda motsi bare suyi yunkurin temakon auntie, seda abbansu yayi magana tukunna kowa yayi tamaza kuma, akazo aka tattaro auntie akayi cikin gida,
TOme karatu gidan fulani ya yamutse.
Cikin dan kankanin lokaci aka hada babban meeting kowa ya hallara, mujaheed kuwa dole yabaka tausayi idan kakalli fuskansa saboda halinda yashiga, meenal da mimi su akasaka agaba kowa yana furta albarkacin bakinshi akansu, Ummi tana jikin hajiya mahaifiyarsu inbanda kuka babu abinda takeyi kankameta,
Auntie kuwa koda Dr dinsu yadubata yace babu wani matsala tsananin firgitane datayi,amma zata iya farkawa akowani lokaci,
Cikin wani wani irin yanayi mimi ta tashi tazaiyano duka abinda yafaru, kowa se salati da sallallami ana zubawa meenal odanu, ita kuwa tayi sukui da ita azaune se aikin raba idanu,
Seda ta kammala tukunna, aka nemi jin tabakin mahaifin na meenal wato daddy,
Yakuwa mike yasoma zaiyanomusu abinda yasha kansu da mamaki zuwa haduwarshi da safiyya irin abinda take fiskanta gurin imam dasakin daya mata dakuma zaman datayi agidanshi harzuwa lokacinda allah yay mata rasuwa sedae bata taba fada masa inda danginta sukeba tace ita marainiyace wannan dalilinne yasa yarike meenal amatsayin 'yar cikinsa saboda kada tafuskanci halin rayuwa,
Sosae muhammad yakejin tsananin tausayin meenal azuciyansa saboda dole yasan zata shiga cikin mawuyacin hali dawannan bakon al amarin datakeji,
Sosae ta kankame mimi tana kuka metsuma zuciyan mumini tamkar numfashinta ze dauke tunowa da irin abubiwan da auntie keyi mata, nana ma hawaye kawae take sharewa saboda tausayinda meenal tabata,
Haka ummi tamkar zatayi bori tana cewa wlh safiyya bata rasuba bazan yardaba wlh data rasu datuni bana duniyar nan nima su sukasan inda suka kaita bazan yardaba ace tamutu,
Cikin wani irin yanayi yaya babba tamike tasoma ibar albarka,
Haba koda naji ashe wannan yarinyar ba jikatace bace bajinina vace dole tayimin ibar albarkar datayi awashegarin data dawo gidannan ashe 'yar gidan sallamammiyace dole zatayi abinda yafi haka, badole safiyya taga karshenta arayuwaba ay wlh dama bazata taba samun farin cikiba,
Jin hakanne yasa hajiya takama Ummi sukabar gurin su daddy kallon mamaki kawae suke wa yaya babba jin furucinda takeyi akan safiyya, seda gwaggo ta tasoma tasoma sauke mata ruwan bala ei tayi shiru,
To kowa da abinda yake furtawa agurin nan shikuwa mujaheed ko kalma daya takasa fitowa daga bakinsa saboda irin zafin dayakejin zuciyansa tanayi masa su meenal kawae yake kallo, abbansu meeanal cikin farin ciki ya rumgume daddy yana godiya ga ubangiji,
Seda aka kira sallan magrib taro yawatse domin yin sallah....

TAKU A KULLUM NANA BMB.

08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: 🤍💞🤍💞
RABON KWADO....
BOOK 3
💕💕💕💕💕
NA NANA BMB.
🤍❤️🤍❤️
page 9
GIDAN FULANI
Menalce kwance adakinta tana kan gado hawayene kawae yake bimata fuska dukta rame saboda ta tashi hankalinta sedae jikinta yayi suwae har kyalli yake da gashinta sunsha gyara fuskarnan tayi suwait tayi kyau sosae tana cikin wannan halinne aka buga mata kofa tanadaga kwancen tace "enter" hasana ta turo kofan tashigo tazauna gefenta taname cewa yayarmu banason kullum ina ganinki cikin wannan halin kinji yau saura 'yan kwanaki yakamata ki fawwalawa allah komae meenal bata tankataba don ita seyanzun take bakin cikin yin shiru datayi tunfarko datayi bayani komae dahaka bata faruba hankalinta gaba daya yana gidansu, tana daga kwancen tace hasana inason muyi magana nidaku baki daya harda abbanmu idan yadawo kije kihayawa ummi,hasana cikin fargaba tace wani magana yaya badae cewa zakiyi kinfasa aurenba cikin fushi meenal tace ina ruwanki da abinda zan fada kije kigaya mata, jiki a sabule hasana tace to ay itace ta turoni nakiraki masu kunshi suna jiranki tundazu tace kifito yanzu, kafin takarasa magana meenal tamike tanufi hanyar fita hasana tace pls yayarmu kigyara fuskarki kada kifito ahaka kinji, fita tayi tabata guri ita kuwa dama ta kudurce aranta komene zefaru sedae yafaru don tabbassa kafin a daura aurennan setabar gidannan,
Koda hasana zasanarwa ummi sakon meenal setayi murmmushi tace aydama nayi shirune inji ta ina gaskiya zatayi halinta dole nasan taga za ayi auren nan tafadi gaskiyar al amari irin wannna kudira ta ubangiji, cike da mamaki hasana tace bangane ummi kinsan abinda zata fadane meke faruwane wae, ummi takalleta tace anjima kibari zakiji komae ay dakanta zatayiwa kowa bayani,
Kunshi tsan tsararre ake yiwa meenal nagani nafada sedae sam hankalinta baya kansu, wayan ummi ce tashiga ruri wayar na hannun hasana tana daga kwance tace ummi ana kiranki da bakuwan number, waca number ce? hasana takaranto number din meenal koda taji number dinda hasana ta karanto zuciyanta tai wani irin harbawa jin an ambaci number irin tata hankalinta inyay dubu yatashi ummi harta share sekuma tace kawomin wayar koda ta amsa kiran ya tsinke se ta aje wayan abinta, allah allah meenal take acire mata kunshin ta dauki wayar umman nasu gashi sun tsaya mata fi ili turaruka kala kala akewa kunshin tana jikuwa kamar tashakesu 😄
bayan tafitone awanka tazauna gaban mirror tana kallon kanta ita har mamakin kanta take yadda takoma ayanzun ga girmann data kara seda karewa kanta kallo tashirya sboda sauri ko dankwali bata dauraba tarikoshi ahannu tafito, sam bata kulada bassam ba a parlour sejitae yace Wooow my meems narasa wani irin kyaune wannan kike karawa haka tubar kallah batareda tajuyoba tasoma tura baki tabude dankwalin nata tarufe kanta, kallonta kawae yake da mamaki shi yarasa meyasa meenal takeyi masa haka yanzu insuna cikin jama ah tayita zuba masa surutu amma idan sukadae suka kasance ko maganar 'yan mintuna bata bari suyi tunda tadawo,murmushi yayi azuciyansa yana cewa komadae meye kinkusa zama tawa komae yazo karshe ay,
{KOMAE YAZO KARSHE KUWA TUNDA GAME ITANAN ZUWA!}
tana shirin wucewa ne tajiyo rurin wayan ummin taso ashema ta nan parlour din dasauri kuwa tajuyo zuwa inda take alokacin kuma ummi tasauko itama, tace wake kirana? koda meenal taji haka jikinta a sabule tadauko wayan takawo mata ganin nunbern din nan dae tadazu yasata daga wayan tana me neman guri tazauna, tome karatu koda ummi taji me magana tacikin wayan tamike tsaye cikin bakon yanayi da al ajabi tace MIMI! juyowa ummi tayi takalli meenal dakyau kawae tahaye sama, jiki nabari meenal tamike zata biza bassam yace no mimi kada kiyi haka, damamaki takallesa jin yakirata da mimi abinda bata tabajin yayiba sedae yace meems, dole takoma tazauna jiki bakwari....

TAKU A KULLUM NANA BMB.

08147110349
[8/31, 3:39 PM] Nana BMB: 🤍💞🤍💞
RABON KWADO....

BOOK 3

💕💕💕💕💕

NA NANA BMB.
🤍❤️🤍❤️

page 14
Tsegumi kuwa kowa da abinda yake furtawa akan su mimi, masauki na musamman aka bawa su daddy abinci da abinsha kala kala sewanda suka zaba ga wata lafiyayyar fura da nono nata zuba kamshin ayaba da kwakwa cikin kwarya an aje musu tanata nason sanyi,seda kowa ya kimtsa tukunna aka azauna aka soma maida magana kuma,muhammad yana sane da halinda mujaheed yashiga amma seya shareshi betanka masaba abincinma kasa ciyayi dayawa fuskarnan tamau da ita,
Hakima Dr kuwa har kawo i wannan lokaci taki farkawa tana room dinda aka shimfideta ita kadae
meenal tana jikin mummy takoma abar tausayi haryanzu kuka take idanunta duk sun kumbure don bakaramin girgiza tayiba wae daddy ba mahaifinta bane ganin abin take kamar a drama sunyi rarrashin harsun gaji takiyin shiru, su daddyn kuwa abbansu mimi ne da alhj aliyu mahaifinsu ummi, se kakan bassam sune sukaje suka samesu daddy suka fahimtar dasu tun silsila abinda yafaru da safiyya,
Daddy kuwa ya girgiza dajin labarin safiyya,azuciyansa yake magana.lallae seyanzu ya yarda da wannan kalmar ta bahaushe dayake cewa "RABON KWADO... Baya hawa sama" donkoyaje zefado yasameshi, tabbas imam kayi asarar rayuwarka dakayiwa safiyyar irin wannan sakayyar lallae kayi kuskure kuwa wanda ahalin yanzu nasan kana kan gani, Allah me iko kenan meyanda yaso dabayinsa,
Koda yakara gwada musu hoton safiyya anan suka kara gasgata al amarin sede jikinsu duk yay sanyi saboda safiyya bata raye, muhammad mamakine yahanashi furta komae yana tunanin to a ina daddy yasami hoton auntie safiyya? sosae kanshi yakulle akan wannan al amari,
Ummi tana kwance kusada hajiya abin duniya ya isheta inbanda aikin kuka babu abinda takeyi dakyar suhajiya suka rarrasheta domin ta dage setaje tasamu auntie ay ita tasan inda
'yar uwarta take, su hasana da twins suna gurinsu mummy da mimi wadda zuciyanta take cike da fargaba ganin yanayin gogan nata datayi babu annuri,
Chapter 6 · 0% Book details