← Book details Rabon Kwado Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 20

Sashe 8

Rabon Kwado Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

page 19-20
Tana tafiya cikin sanda harta isa inda yake tasa hannu tarufe masa idanu tana bayanshi sedae mujaheed bakaramar tsorata yayiba addu ah yasomayi ba kakkautawa ita kuma jin yadda yake jero addu o ei yasata fashewa da dariya tajanye hannayenta dariya harda tafa hannu tana nunashi koda yabude idanunshi suman zaune yayi yana kare mata kallo ay yau ganiyay tamafi koyaushe kyau yadda take dariya kamar sakarae yake kallonta seda takare dariyar tata tace kae yayana haka kake da tsoro dama sam bemaji metake cewaba saeda takae hannu ta dungure masa kae sannan ya lumshe idanunsa tana murmushi tace kunya kakeji nabaka tsoroko,
Bude idanunsa yayi dasuka soma sauyawa wayarshi yadauka yaga time har kusan biyu saurama ya jinjina kae ya aje wayan bazato taji yajawo hannunta yana daga zaune tana tsaye harseda ta dsngane daga jikinshi kirjinta yasauka akan fuskarsa yasauke ajiyan zuciya dakyar ya iya furta my dear kinbani tsoro over mekikeyi anan bakiyi bacciba shirun datayi masane yasashi dagowa yana kallonta suka hada idanu yadda nashi yacanzane bazata iya jurewa kallonshiba ta sunkuyar dakanta kasa tace nayi bacci farkawa nayi,sukayi shiru nadan lokaci sannaa taji numfashinsa awuyanta yana cewa nimafa sena rama tsoron dakika bani kishirya jinsa yanzu ato,bata fahimci meyake nufiba sema rintse idanunta datayi tana murmushi hakanne yabashi damar karewa kirjinta kallo gaba daya rigan ta zanzare dan kadan tarufe mata kirji bakin cikine yakamashi ganin karcewar datayi haryanzu akwae shatinta,hannu yasa yadan shafi gurin,habawa aykuwa kamar an tsikareta tabude idanunta tana kokarin kawcewa seyanzun ta tuna ayadda tafitoma don manni irinna mimi takasa kwacewa don riko mekyau yamata kuma yaki dena abinda yakeyi mata haushi sosae yatiketa takae baki tacizar masa hannun dole yasaketa tajuya dasauri zatabar gun tabdi tana juyowa taga yama cimmata saboda tsoro takife agurin ido kawae take kwalowa tana bashi hakuri cikin shan kunu yace tonima wayace ki tsoratani,ganin abin nashi gabama yakeyine yasata sakin kuka tana ture hannunshi tana cewa nika kyaleni banaso kukan tane yasashi tattaro hankalinshi yacire hannunshi cikin rigarta tamike asukwane kuwa tanufi cikin gida tana hawaye masu zafi koda tashiga dakin nata tasake fashewa da kuka tafada kan bed tana jin zafin mujaheed sosae azuciyanta donme zetaba mata jiki ita ba matar saba kuma ba ita yakesoba meenal yakeso ziyi mata haka, shima mujaheed kayanshi yatattara yakoma daki yanajin haushin kansa abinda yayiwa mimi,seda taci kukanta takoshi sannan bacci yadauketa,
WASHE GARI
Da wuri mimi ta tashi tayi wanka tashirya ta tasa kayan meenal agaba tanata kallo natafiya tana tunowa da muryar auntie takejin zuciyanta na harbawa tanajin fargaba dukda batasan gidanba amma zuciyanta bata kaunar tafiya gidan,tare sukayi breakfast dasu auntie saratu banda mujaheed donbe shigoba kallo daya sukayi mata sukasan tayi kuka sekuma basarwa take don karsu gane wani abu, daddy yana shirin fita aikine nujaheed yashigo yana waya seda yakammala sanan yagaida iyayen nashi mimi nagefe tanata zumburar baki ita ala dole anmata badae dae bah beko kulataba dasu mummy kawae yake hira har suka fita zata raka daddy din bakin gate suna fits yatashi yaje yazauna a dining yasoma breakfast dinsa beko kalli inda mimi takeba,seda daddy yashiga motan yarufe kofan sannan mummy taruza kanta tana masa magana cewar kajawa danka kunne yafaja girmansa meenal yarinyace tsaf zata rainashi kana ganidae yau kogaisawa basuyiba zuba mata ido daddy yay yana murmushi harta kare maganarta,sannan yace niba abinda zancewa dana kema idan kika gaya masa ay yayi,mujaheed yasan abinda yakeyi saedae ita meenal daganin wannan yarinya zeyi fama da ita itazakiyiwa fada kada ta lalatamin yaro,hade rae tayi tace kaedama indae akan mujaheed ne kada sonkanka dayawa goyon bayanshima kake kamar batare dakae muganshiba jiya a garden yanama 'yar mutane ayka aika,kace zata lalata wancan katon yaron duka nawa take metasani mah katseta yayi dacewa aydama ku mata haka kuke kuyi tsokana kuma kuce anmuku ba dae daeba inbanda jiya kintaba ganinsa yamata wani abu nifa bazanga laefin danaba wani kinibibinne yafito da ita daga dakinta cikin wannan dare tasameshi har inda yake kuma babu shiga ta mutumci itacefa takae kanta don dana ba dutse nahaifa bani,so kigaya mata taringa suturta jikinta harsuyi aure kada kada ta lalatamin tarbiyarr yaro da ace dakinta yabita ne wannan to zega abinda zefaru kuwa to amma yanzu laifi na 'yarkine,duka meenal matasani arayuwarta dazata iya wannan aikin,dariya yayi sosae sannan yace ki kyale zanceb kankanta duk inda mace take to macen ce so kidena yimata kallon karama aynazu akama 'yar can aure seta zauna harda murnarta kike abinki keni koyanzu my son keson yin aure yimasa zanyi donnaga 'yar takima kila setafiki iya rike miji! dama yatada motansa kafin takuma magana yaja motansa yana dariya yana cewa sekun dawo matafiya agaidasu Dr maryam sun saba mummy da daddy irin wannan drama din soyake dama yakunnota kan yafita,
Seda yagama breakfast dinsa sannan yadawo kusads ita yazauna zumbur kuwa tamike cikin fushi yarike hannunta tajuyo cikin tsiwa suna hada ido tayi lakwas da ita rae abace yace baki iya gaisuwa ba koh cikin tura baki tace ina kwana yadda tayi masa maganar ne yasa ranshi yakuma baci kawae yasaki hannun nata yamike yafice daga parlour din tabishi da harara harda murguda masa baki,yana fita mummy tashigo tace meenal kingama hada kayankidae koh anjima zamu tafi kamar tayi kuma ta daga mata kae seda tazauna tace meyake damunkine kika shiga damuwa tundazu bakomae mummy, tomeya hadaki dayayanki nanma shiru batace komaeba, mummy tasauke ajiyan zuciya tace aduk sanda zakiji gurin yayanki kiringa suturta jikinki kafin kije kinga ba aure kukayiba saboda gujewa hudubar shedan, ay zuciyar mimi tsinkewa tayi tana kwalo idanu kardae mummy tagansu jiya dakyar ta iya daga mata kae alamun to don takasa dagowa, yawwa meenal allah yayi miki albarka kije kirasa kimtsa kayanki koh, tamike jiki asanyaye tanufi dakin abin duniya yaymata yawa tarasa abinda yake mata dadi tanajin wayar meenal tanata ringing amma taki kulata sotake taga mujaheed amma ko motsinshi batajiba har karfe biyu tayi narana sosae take kuka tunda tafito awanka tamakasa shirin daga ita towel tana haka taji ance kukan me kikeyi?tayi saurin dagowa suka hada ido kunyace takamata tasunkuyar dakanta kasa cikin tura baki tace to ay bakuka nakeyiba kaenane yake ciwo,betankataba yajuya zefita yace kitashi kishrya kifito mutafi kemuke jira zamu gidansu inna dagacan muwuce rintse idanunta tayi don sam tamace batasa kayaba ga towel din dukya tattare ganin zefice ne sayata saurin saukowa tazura hijab tace yayana cikin sanyinta, ay zuciyar mujaheed tawani harba jin muryar meenal dayayi tacanza wanda bakowane zefahimci hakanba takowa tayi har inda yake tazagayo tatsaya agabansa idonta tafda kwallah tace sokakeyi natafi nabarka nifa banason tafiyar nan kagayawa mummy tabarni banason tafiya nabarka nafison kasancewa dakae koda yaushe bazanyi farin cikiba indae kayarda aka maedani gida kuma sena dena yima magana, tana kuka tamatsa ta dora kanta kan kirjinshi tana kuka tana cewa pls yayana pls....

TAKU A KULLUM NANA BMB.

08147110349
[7/28, 8:20 AM] Nana BMB: 💝💖💝💖
RABON KWADO....
BOOK 2

NA NANA BMB
Chapter 8 · 0% Book details