← Book details Rabon Kwado Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 20

Sashe 10

Rabon Kwado Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

page 21-22
Sam mujaheed besanda sanda yamata kyakkyawan rumguma yanadan yasunkuya saitin kunnenta yana cewa am sorry my dear zanyi kewanki matuka but iyayenki ne suke bukatanki kusadasu bamuda iko akanki nidake seyadda sukayi damu kwaedae meenal in dae kina sona kina kaunata dayawa kina gama secondary school kibari amana aure hakan shine ze bamu damar rayuwa atare harzuwa karshen rayuwarmu,bugun zuciyartane yakaru tana tunanin taya zatayi aure bada sanin iyayentaba?
Dan matsatan dayayine yadawo da ita tunanin data lula tayi saurin janye jikinta takoma bakin kofa tace to yayana nayarda kafita nashirya sedae gani tayi yakara matsota sosae harsunajin numfashin juna yace kinutsu meenal bawani abu zanyi mikiba bazan kara aikata abinda nayimiki a garden bah nasan ban kyautaba kiyi hakuri kawae yajanyeta gefe yabude kofan yafita suna paulour suduka suna jiranta sauri sauri tashirya takwaso kayanta tafito suka kaemata mota suka nufi gidansu su innan sukayi musu sallama sannan suka dauki hanya kuma mimi ansami abinyi abinda take so kallon duniya idanunta nakan hanya,
GOMBE
Meenal ce kwance kan gadon asibiti gefenta kuma wata matace azaune tazuba mata ido ba tsammani taga meenal din tasoma bude idanunta tanadan motsi harta bude idanunta tangaran matar kuwa tadurkusa ta rungume meenal tana kukan dadi tasoma magana sedae me? sam bahausa matar takeyiba fulatanci take yarawa tana mika godiyarta ga ubangiji daya tashi kafadun yarinyarta,tamkar zuciyar meenal zata fito waje haka takeji duk abinda yafarune yashiga dawo mata sedae tunaninta yatsayane atime din da mutuminnan yake bata ruwa sedae tafarka taganta anan yanzu matar tana dagata tajuya suka hada idanu komae na na tunaninta yatsaya saboda tsorata ita kanta matar seda tafuskanci hakan karkashin zuciyan meenal addu ah take sosae saboda wannan matar tarike fuskanta itace take yawon zuwa mata a mafarki tana kuka tana mika mata hannuwa rintse idanunta tayi tana cewa dama mutuwa nayi kenan gashi naga wannan matar shikenan nabar gidamu har abada tana wannan tunanin ne muryar wata yarinya tadoki kunnenta wadda tashigo yanzu bazata wuce shekara shadaya da rabiba sewasu twins yara maza dasuka biyota abaya kyawawa dasu masha allah sukuma bazasu wuce shekara 7 bah zuwa 8 yarinyar tana cewa UMMI! wae haryanzu yayarmu bata farkaba jin yarinyar tayi hausa yasa meenal saurin bude idanu tana kallonsu ganin hakanne yasa yarinyar farin ciki mara misaltuwa taje takwanta akanta tana murna kamar me yaryarmu munyi kewanki kullum cikin kuka muke munrasa inda zamu tsoma rayuwarmu ina fata babu abinda azzulam can sukayi miki koh, shiru meenal tayi musu taki tankawa kowa sedae ido kawae datake binsu dashi jikinta asabule tamike tsaye tana kallon yayar tasu kamar tayi kuka takalli matar tace UMMI meyasamu yayar mune bata magana hannunta tariko tace hasana kiyiwa yayarku uzuri bata gama dawowa dae daeba bata juma da farkawaba twins suna gefe sunzuba mata idanu suma, idonta tafda kwalla tace allah sarki yayarmu allah yasaka miki yabaki lpy kokarin mikewa zaune take ummin ta temaka mata ta tashi tasa mata pillow abayanta tazuba mata idanu ko kiftawa batayi hasana takalla tace kira abbanku kisanar masa yayarku ta tashi bamusu kuwa tadauko waya cikin jaka, ummin mamaki take yadda meenal take kallonta haka hannunta tariko sosae tana cewa kiyi hakuri MIMI kinji kinriga kindawo gida kiwantar da hankalinki babu abinda zesameki,wata faduwar gabace tasami meenal jin an ambaci mimi seyanzu komae yadawo mata tuni tafara ambaliyan hawaye tana girgizawa matan kae ita yanzu taya zata ganar dasu ba ita bace mimi seyanzu ta tuna itace matar datakejin kukanta awaya yanzunkam mamakinta yakare ta tabbatarda ba mutuwa tayiba to amma wacece wannan matar rarrashinta ummin tasu tashigayi dakalami da dada masu kwantar da hankali itama hassana gefenta tazo tazauna tace sorry kinjee yayarmu nakira abbanmu yanzu zezo kidena kuka kinji tasa hannu tana share mata hawaye haka twins kafafunta suka rike suna cewa pls yayarmu karkiyi kuka, tunda meenal take bata tabajin nutsuwar zuciya da farinciki irin wannan bah ganin ita kadae sukema wannan rarrashin ga nuna kauna da kalawa hakanne yasa hawayenta kin tyayawa duksetake ganin abin wani iri yau ana mata irin wannan rarrashin bandaki tace musu zata shiga don haka ummin tasu ta rakata bakin bayan tatsaya daga kofa tana jiranta,
Tana cikin bandakin abban nasu yashigo da sallamarsa kana ganinshi kasan yana cikin farin ciki suduka sukayi kanshi cikin fillacin yasoma magana shima cayake ina mimin take ummin tanadaga bakin bayin tayi masa nuni da hannu alamun tana ciki hasana tace abbanmu yayarmu ay bata magana,itama fulatancin tayi masa magana,meenal tana daga cikin bayin tana jiyo yadda suke magana sedae sam ko kalma daya bazatace ga abinda suke tattaunawaba don sun juye harshensu tuni idanunta yadinga tsiyayar hawaye tagama abinda takeyi amma takasa fitowa kamar tasa kuka catake ya allah wani irin mutanene wadan dan ka kawoni cikinsu bansan mesuke cewaba ganin batada mafitane yasata dole bude kofa tafito, ummin takamota har kan gadon tazaunar da ita, sannan tayi mata hausa tace mimi inane yakemiki ciwo yanzu,girgiza mata kae tayi alamun bakomae, abban nasu yace to alhmdlh 'yata tadawo gida lpy makiya kuma sedae suji kunya ankusa kama wadanda sukeda sa hannu a saceki mimi alkawari nayi bazan taba kyale kosuwa sukayi mana hakaba wlh, kuma tunda allah yanufa kin farka ayau zamu koma gida bazaki kara kwanan hospital dinnan bah duka gaba daya gari yadauka 'ya ta tadawo so nan babu wani tsaro gara mutafi gida acan hankalina zefi kwanciya sam umminsu batayi masa musuba yana maganar tana hadawa meenal tea mekauri a cup tabata tasha takoshi sosae taji kwarin jikinta dama ga drip ansa mata ba iyaka,
GARIN KANO
koda suka isa janbulo gidan alhj abubakar horn biyu gateman yabude musu gate suka shiga gidan bayan sungaisa da megadin, nana tana kwance tadora kanta akan cinyar auntien tasu ita kuma auntien tana karatun jarida,koda suka shiga parlour din nana tamike cike da mamaki tana kallonsu sunshigo bawani hayaniya, aduk sanda meenal tayi dawowa irin wannan tunkan motansu ta tsaya zata fita aguje tayi ciki tana kwala musu kira sallamar dasukayima kasa amsawa nana tayi saboda mamaki se auntie ce ta aje jaridar ta amsa musu,koda suka hada idanu da mimi zuciyar tace tawani irin jarbawa saboda yadda tayi mata kwarjini ga girman dataga takara dakuma cika ido babu fuskar data fado mata seta safiyya,hakadae ta daure aka gaggaisa mujaheed yana dariya yace nana yadae meenal din taki tacanza mikine kikayi poster haka kina kallonta da mamaki nana tace sosae makuwa tacanza ya mujaheed wannan ba halin meenal bane akwaedae wani abu ganima nake kamar ba itaba shida mummy sukasa dariya kana yace lallae nana abinnaki aziminne toke meenal kinji mimi nazaune tadanyi guntun murmushi don ita tunda suka shigo tajee mutanen basuyi mataba duk zuciyanta acunkushe yake mussam irin kallonda dataga auntien nayimata, nandanan aka cikasu dakayan ciye ciye mimi ruwa kawae ta iyasha saboda bata yanayi me dadi nana kuwa takasa dena kallon mimi saboda mamaki auntie duk wannan baragadar babu komae kasa jurewa nana tayi tace waike meenal lafiyanki kalau kuwa suduka kallo seya koma kanta murmushi tayi mata again tace lafiya kalau fah ba abunda kedamuna tafiyan nance tasa kaina yana ciwo ko magana banasonyi amma bawani abu mekika gani,wlh ban yardaba shine abinda nana tace kawae, sosae auntie take mamaki yadda mimi take magana da aji cikin yauki amma saboda abindake cimata zuciya ko kulata takiyi hirarsu suke da mummy ita kuma nana sunayi da mujaheed hakanne yasa mimi juyawa takwanta akan kujera ta lullube fuskanta da mayafinta,
Suna cikin fira munaheed yakira muhammad vidio call yana shaida masa aysun iso aje wayan yayi yadda zega kowa suna gaisawa mummy ce tafara tsokanarshi tana cewa kadae zama dan can can ho dae ko muhammad kememe kodan hotunma kaki zuwa kamana,mujaheed yana dariya yace lallae mummy ina zedawo bakisan yadda kasar nan take gara masabane kilama acan zesamo muku sirika yajuya ya kannewa muhammad ido yana dariya,mummy tace a ah wlh allah karya biye bakinka bakada kirki allah yatsaremu duka takae masa yagoce, auntie ma tayi dariya tace tomeye aciki kae muhammad kataho tasu inyaso shima mujaheed kataho masa datasa kuyi anko bashikenanba, yakuwa gimtse dariyarsa yace haba auntie wlh allah yakiyaye ni inada wadda zan aura,ay nana kamar an mintseleta tamike tazauna gefenshi tana cewa wow ya mujaheed wacece wannan fadeta naji don allah,hararnta yayi yace to uwar gulma bangayawa su mummy bah seke muhammad yace aikin banza to kada kafada mana,mummy tace shakuriminka muhammad aynama santa ko ince munma santa, dasauri mujaheed yace pls mummy kiyi shiru mana, muhammad yace aishikenan kuma munma dena damun kanmu tunda munsanta abinda zamu ganta meye nadamuwa kada kafada kila bata azziki bace kake hana musani mudae indae batayi manaba dole acanza, dariya sosae mujaheed yayi yace bakasan kowaceceba zaka fara yimata rashin ta ido inda kuma kanwar kacefa? nepar kan muhammad ne yadauke haka itama auntie dakyar yatattaro nutsuwarsa muhammad yace banganeba,
Zaka gane nan gaba kadan cewar mujaheed.
Tambayarsa yayi yace ina meenal ne nibanjita tunda muka fara waya, tana kwance mimi tana kunshe dariyarta don bakaramin dadi hirar tasu takeyimataba, kallonta mujaheed yay yana murmushi yace kaganta tana hutawa takwaso gajiya murmushi muhammad yay metarin ma ano ni dayawa yace to nunamin ita nagani waca irin gajiyace haka dazatasata shareni,
Wayan yadauka ya isa inda take kwance tanajinshi tarufe idanunta ya yaye mayafin fuskanta tabayyana kafansa yadora kan tata yada yatsansa babbashi yana mata susa a tafin kafan nata tanata mamar mamar da idanunta kana gani kasan ba bacci takeyiba dariya take shirinyi saboda abinda yakeyi mata tasaki murmushi har dan dimple dinta ya lotsa abinda muhammad yakeson tabbatarwa dama kenan wani irin gumine yake tsatstsafo mishi mikewa tayi tari kafan nashi tace kae yayana kaga katasheni ina bacci tayi maganar cikin shagwaba shikuma yarankwafo saetin kunnenta yace baki gaisheda yayankiba yay maganar harda dan cizar mata kunne muhammad ya lumshe idanunsa time din tadago tace yaya ina wuni, bekara bari yaji mezata ceba yakashe wayan....

TAKU A KULLUM NANA BMB.

08147110349
[7/28, 8:20 AM] Nana BMB: 💝💖💝💖
RABON KWADO....
BOOK 2

NA NANA BMB
Chapter 10 · 0% Book details