← Book details Rabon Kwado Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 20

Sashe 16

Rabon Kwado Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

page 35-36
Zuwa yanzu su meenal anzama 'yan gari a gidan fulani koya yanzu yasaba da surutun meenal kuma ana magana akan canzawarta lamarinta kamar asiri yanzu ta dawo saurarar bassam wanda hakan bakaramin farantawa abbansu rae yayba ummi kuwa yau lpy gobe babu kullum cikin ciwo take tunanin 'yar uwarta take akowani time makarantar da aka canzawa mimi yanzu babu wanda yasan inda takoma saboda tsaro daga ummi se abbansu kadae suka sani saura 'yan watanni tayi candy,
To su nana suma yau sukusa watanni uku danyin cabdyn su itada mardy damuwan nana takaro saboda rashin ganin yousep abin kaunarta wannan dalilinne yasa yanzu nana kullum setabi driver dauko mimi a school shikuwa yousep yana zuwane don babyn shi meenal sam auntie batasan cakwakiyar dake faruwaba mardy ma dae hakan take kullum cikin ddamuwa saboda mimi tacanza mara tanata zarya gidansu amma abanza dama nana bata shiga sabgarsu,
Yau friday takama yau daddy yadawo daga dubai se dare ya tattara iyalan nashi a parlour seda yayi gyaran murya tukunna yace shin nana kinada saurayi tsayayye ne wanda kikeso bata taba tsammanin tambayarba cikinta kuwa yabada wani kara mimi kuwa addu ah tafara azuci allah yasa kada nana tace tanason yousep suduka ita suka zubawa idanu seda daddy yakuma maimaita tambayar sannan tafara i nda inda takasa magana ma auntie tace wani irin shirmene wannan nana ana miki magana kina kame kame hannu yadaga mata daddy yace kyaleta ay abin bana fada bane idan batadashi ayba matsala bane karatu zatayi dama kada natauye mata hakkine ko aure takeso yanzu shiru takumayi auntien takuma cewa kinaji to kinyi shiru kanta a sunkuye tace zancigaba da karatun daddy inada wanda nakeso yatafi karatune shima bedawoba cikin gamsuwa daddy yace to allah yasa haka shiyafi alkhairi, sosae auntie takewa nana kallon mamaki shin wanene nana takeso batasaniba? kallon mimi yayi yace ke kuma meenal inaso kimaida hankalinki kan karatunki kawae banason shashanci kiyi iya abinda yake gabanki kawae kanta asunkuye tace insha allah daddy, idan mimi tana magana cikin sanyinta daddy seyay ta mamaki yadda meenal tasauya haka, sanya musu albarka yayi suka tashi suka nufi makwanci zuciyar nana cikeda fargaba tana tunanin yadda zata bullowa lamarin kota wani haline kuwa setasan yadda taraba meenal da yousep tunkan asan suna soyayya,
GIDAN FULANI
Zaune suke a parlour suduka hasana tana koyawa twins homework ita kuma meenal tana kishingide tana karatu a book dinta don saura 3 days takoma school ummi nadaga gefensu tayi zurfi cikin tunaninta meenal tana kulada yanayinta tanason tambayarta damuwarta amma bahali meenal yanzu angirma anzama cikakkun 'yan mata takara girma kamar ba itaba tazama 'yar gayu kullum kara kyau take makeri nakara kerowa fata natasheki tajee hutu,itama tunanin talula na yadda zata koma gida amma tarasa taya zata fara kullum intayi yunkurin yin maganar seta kasa saboda tsananin tausayin ummi datakeji kamar tayi kuka intana ganinta cikin damuwannan shiyasa takasa tabuka komae amma zuwa yanzu ruhinta yayi gida mussam dataji tanayin candy bajumawa za ah musu aure itada bassam iya yanzu kuma tasan ya muhammad dinta yakusa yadawo wa gida bawan allah kowani hali yake ciki tana cikin wannan tunaninne taji twins sunfado kanta suna kikkifta mata idanu alamun tabasu satar amsa sam batasan mesukeyi bama mikewa hasana tayi tana cewa wlh yaya tagaya muku kunfadi murmushi tasaki don ganin irin kallonda twins suke mata se suka bata dariyama kiri kiri kuma hasana tahanata magana suna cikin wannan drama din abbansu yadawo yauma fuskarsa dauke da tashin hankali yayi sama batareda bata lokaci ba kuwa ummi tabishi, sosae ta girgiza dajin kalamin bakinsa cewar jami ay sungano cewar harda sa hannun 'yan gidansu a sace mimi da akayi yanzu su ake lalube zaha gano kusuwaye sunjima suna tattaunawa kozasu san suwaye amma tunaninsu be basu kowaba har lokacin sallan ishah yayi yafito suka tafi masallaci shida twins itama umman tasu fitowa tayi sukayi sallah taredasu meenal koda suka idar sukayi addu ah suka shafa sannan ummi tariko hannunsu dukansu tajawota kusada ita sannan tace yaku diyae na yau zan sanar daku abinda kullum kuke burin kusani akan abinda yahaifarmin da ciwo mimi kullum kina tambayata damuwata amma ina miki shiru to yau zancireku aduhu baki dayanku,
TUSHEN LABARIN

TAKU A KULLUM NANA BMB.

08147110349
[7/28, 8:20 AM] Nana BMB: 💝💖💝💖
RABON KWADO....
BOOK 2

NA NANA BMB
Chapter 16 · 0% Book details