← Book details Rabon Kwado Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 20

Sashe 17

Rabon Kwado Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

page 33-34
Zamanta kenan a parlour takira mimi awaya tashaida mata sun iso gata a parlour mimi jitae kamar tasa kuka haka ta daura dankwalinta tafito tana rike da wayarta tana saukowa daga steps idanunta nakan nadiya haka itama da mamaki take kallon mimi zama tayi gefenta tana mata murmushi cikin sanyinta tace sannu dazuwa sam mamaki yahana nadiya magana kallon jikinta tayi taga me nadiya take kallone haka amma bataga komaeba zuciyanta ce tasoma shiga rudani daganin kallonda nadiya take mata,
Ahankali takae hannunta tarike nata cikin mamaki tace auntie wow haka kika koma masha allah mimi tayi murmushi tace keda ya yousep dinne kukazo nadiya tadaga mata kae tace kuma baki kirashiba auntie bayan gawayan ahannunki yana cikin wani hali sabodake ke naga babu abinda yadameki kodae kindena yinsa yanzu kinyi new catch ne wayar nadiya ta ansa tace bari naga abinda yasami wayan, ga mamakin mimi kawae segani tayi tacire pin din wayar nandanan dadi yakamata ganin numbers dinda tadanna,messeges dinda nadiya taganine bata budeba tace yanzu auntie meyahanaki bude sakon yayana haka nifa amma bari dae nabude sakon naga meya kunsa, saurin fisge wayar mimi tayi tana fara ah tace meyasa zaki ganemin sirri, nadiya tace sokike nagani dama tunda kika ki budewa nibasena bude mikiba, wai ina yayane? kanta rufe baki taga nana n nasaukowa daga steps tana mata fara ah har takaraso tazauna taname cewa nadiya kun iso kenan,eh yaya munsameku lpy? nana tace lpy kakau yajikin yayan naki, dasauki yaya kinga yanzuma ina mata maganarshi tana shareni nana takalli mimi wadda tayi zurfi cikin duba sakonnin wayar duka na yousep ne sena nana guda daya se sakon muhammad daya daga mata hankali se miss calls data gani ciki harda sunayen mutanen dabata saniba wato su mardiyya dube dubenta kawae take awayan tamantama da nadiya gurinta tazo koda tayi arba da hoton meenal zuciyanta bugawa kawae take tana matukar mamaki dole baza ah ganetaba kuwa,
Tuni ran nadiya yabaci ganin irin wulakancin da mimi ke mata abinda bata taba yimata bah da nana kawae suke hira harta gaji tace wae auntie wani irin wulakancine haka kikemin tunda kika zaune kike basar min kamar bakisa dani agunba meyake faruwane, mimi ta aje wayan tace sorry nadiya kinji bawulakanci nayi mikiba naga kuna magana da yayane, nadiya tana shan juice dinda aka kawo mata tace to ya yousep fah ke yake jira tunda nashigo bazaki gunnashiba harsena yi magana shirunda tajine yasata dagowa taga ashe mimi tacigaba da danne dannenta awaya bakin ciki ya isheta kawae tamike tadauki jakarta tace yayarmu bari natafi bazan iya jure wannan wulakancinba gaskiya allah yabamu alheri zuciyar nana kal da farin ciki tace tsaya nadiya nazo nawa yayan naki sannu nana tamike tabi bayanta,
Dole mimi batasoba ta aje wayan tabi bayansu har tashige gaban motanma yousep yana hango mimi yasauke ajiyan heart sedae fuskarsa babu fara ah ganin nana dayayi daga cikin zuciyanta mimi tace kaene ya yousep din kahadu babu karya dole meenal tasoka seda takarasa gaban motan tarusuna tace ya yousep ina wuni cikin sanyin muryanta shikuwa kasa magana mah yayi yazuba mata idanu nana kuwa jitake kamar ta galla mata mari don ganin irin kallonda yousep kemata jin baze amsataba yasata kallon nadiya tace sorry sis love banyi haka donna bata miki raeba, caraf yousep yace no nadiya tanada gaskiya baby dole tayi fushi yanzu kin watsar damu baruwanki damu, cikin marae raece fuska tace ya yousep bahaka bane kufahinceni kajee sauke ajiyan heart yayi yace baby indae kinason nafahimceki toki bari iyayenmu sushiga lamarinmu,
koda nana taji haka batasan sanda tafisgi hannun mimiba sukayi ciki tana cewa sorry kwayi waya ya mujaheed ne yake kiranmu idonta tafda kwalla tayi maganar yanzu da biyu dama yousep yay maganar seguwa gashi yaga abinda yake tunani kuna zuciyarshi tashigayi yana tunanin mezewa nana yahuce shikuwa haka yafigi motan yay gaba nadiya na mamaki,
Yinin ranar gidan fulani sunyishine cikeda mamakin sauyawar mimi surutu kamar aku kowa bashi labarin irin azabar datasha take ko ina agidan yadauka abinda meenal tayiwa yaya babba kowa yaji dadi sam meenal takasa tantance iya adadin al ummar dake wannan gida dataga wannan taji sunansu zata kuma ganin wasu har zuwa dare suka koma bangarensu shikuwa bassam mahaifinsa yay masa kiran gaggawa bedawoba har wanna lokaci ummi sama tahaura donyin wanka sukuwa su meenal suna parlour sunata hira dadi yacika su hasana yau yayarsu tabasu lokacinta,
Suna cikin hira se ganin abbansu sukae kamar daga sama dukansu kuwa suka tsorata da ganin fuskan abban nasu babu alamar annuri atare da ita ciki ciki ya amsa musu sannu dazuwan dasuke masa ko twins be kallaba ya haura sama, yana shiga bedroom din ummi tafito daga wanka tana daure da towel ganin yanayinshine yasata tsayawa tace lafiya kuwa, dogon tsaki yaja jikinshi har rawa yake yake saboda bacin rae yasoma cire rigan jikinshi yana cewa sumaya bansan mezanwa imam inhuceba arayuwar nan, cikin firgici ta dafe kirjinta tace wani imam kake nufi?cikin cije baki yace imam dae mijina safiyya, habawa tuni takaraso kamar zararra tarikeshi hannuwanta na kerma hawaye wani nabin wani tace ina 'yar uwata take ina yakaemin ita meyake faruwa da ita?
Iska yafitar dags bakinshi mezafi sannan yajawota jikinshi yarumgumeta yaname cewa am so sorry sumaya imam yaci amanar mu ya yaudaremu yasaki safiyya ahalin yanzuma besan inda takeba harma yaje yayi wani auren se ayau da dubunshi tacika allah ya hadani dashi yanacan nasa a kullemin shi sakin jikin dayaji tayi masane ajikinsa ya tabbatar da tariga tasume cikin kidima kuwa yadagota amma ina sam bata numfashi jijjigata yake yana kiran sunanta amma ina hankalinshi atashe yakwantar da ita kan bed yadauki wayanshi dakyar ya iya lalubo number din doctor yakirashi bugu daya yadaga wayan bejira komaeba yace jikin sumaya yatashi doctor nan da mintina biyar tayimaka a cikin gidannan ya yanke waya, yadebo ruwa a bowl yanata shafa mata ajiki kozataja numfashi amma abanza dole jiki asanyaye yadauko kaya yasaka mata, yasoma sintiri adakin, bajimawa doctor yakirasa yabasa umarnin shigowa ayyada su meenal suka ganshi sumasan ba lafiyaba yasharbe da gumi sosae dagani bakaramin azababben sauri yashaba yawucesu,
To numfashin ummi be daedaetaba harzuwa 11 sedae koda ta tashi kara daga musu hankali tayi kuka take tamkar ranta zefita tana kiran sunan safiyya seda doctor yamata alluran bacci tukunna aka sami salama,su hasana suna parlour hankalinsu yamatukar tashi tasan jikin umminsune yamotsa tunda sukaga shigan doctor, se bayan tafiyan sane abban yake shaidamusu suyi hakuri suje su kwanta jikin ummine ya motsa amma dasauki ranar dae suduka gurin meenal suka kwana suna cikin jimami,
Tome karatu haka rayuwa tacigaba da gudana tsakanin gidansu mimi da gidansu meenal wani irin kauna meenal takewa su ummi dakuma tausayinsu da kulawanda suke bata hakanne yasa takasa bayyana musu gaskiya tana jin tausayin ummi batasan halinda dazata shigaba kullum tana tunanin ina mimin take shin mafarkinta da takeyi tana ganin auntie nadukan mimi gaskiya tana gidansu a matsayinta, idan suna tare da bassam masoyinta take tunawa yousep haka zataci kukanta takoshi sam batada mafita ayanzu sosae meenal take mamakin rayuwarta itadae kullum cikin addu ah take allah yakawo mata mafita a rayuwarta tana tunanin 'yan uwanta wani hali suke ciki ayanzu tawani bangaren tana mamakin yadda ummi take kamata da wasu alamomi amma tayi kamar bata ganiba, tasha yimata fulatanci amma takasa maida mata martani haka idan da fulatanci suka hadu suna hira sedae tayi shiru tana saurarensu,
To mimi kuwa harkawo iyanzu sunkasa daedaeta kansu da nadiya kullum cikin mita take mata yanzu shareta takeyi batason yimata magana haka suke kullum a school zuwa yanzu ta diga ayar tambaya akan auntie tana tantama akan ba itace tahaifi meenal bah saboda irin muguntar da takeyi mata abu kadan tahau sharara mata mari kuma tashanye don acewarta allah ne yakawota wannan rayuwa shiyasa tayi tawakkali garesa take jure duk wata wahala tawani bangaren kuma soyayyar mujaheed tagama kasheta hartanajin bazata iya komawa gida batare data aureshiba don tasan mezataje ta tarar soyayya suke zubawa abinsu haka yousep ma don acewarta meenal take riritawa soyayyarta, NI NANA NINAGA ABINDA YAGIRMI KAENA WANNAN KWADON BAKA KENAN, mimi tanason sanin halinda mahaifiyarta take ciki amma bahali tasaba da kowa agidan haka suma sunsaba da shiru shurunta yanzu magana seta gadama tana waya dakowa harda mardy sedae ita sosae taga canji hakan kuma beyk mata dadiba ko maganar muhammad mimi batason tayi mata shiyasa abin yake damunta sosae bata iya kiran muhammad mugun jin tsoronshi take ko sunanshi suka ambata se heart dinta taharba bare yakira awaya abata jikinta har bari yake saboda kallon da yake mata me tarin ma a noni dayawa komae ya ajeshi agefe seya dawo tukunna don saura 5 mount yadawo kenan kullum mimi cikin addu ah take allah yabaiyyana meenal tabar gidannan kafin yadawo cikinsa....

TAKU A KULLUM NANA BMB.

KUYI HAKURI DA RASHIN TYPING DINA SOSAE AIKI NE YAKEMIN YAWA.

08147110349
[7/28, 8:20 AM] Nana BMB: 💝💖💝💖
RABON KWADO....
BOOK 2

NA NANA BMB
Chapter 17 · 0% Book details