← Book details Rabon Kwado Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 20

Sashe 5

Rabon Kwado Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

page 11 -12
Koda suka karasa gidan kowa yanata shirin tafiya gida abinsa ita kuwa mimi tayi lamo tanata kallon gidan don yau ta taba zuwansa seda su zara suka gama shirinsu sannan tazauna gefen meenal tace to meenal zamu tafi sae allah yakaemu naki bikin muzo musha shagali,murmushi mimi tay batareda tadagoba tace hmmm,inty ma murmushin tayi tana kallonta,sosae tafiyar su zara tasa sukaji babu dadi ga mimi bata wani magana sedae kallo kawae gidan yayi shiru bakaman jiyaba wayar meenal inty tadauko tace meenal gawayanki koda naga miss calls dayawa sena kashe miki wayan tunda ya mujaheed yace bayason asan bakida lpy,murmushin karfin hali tayi mata ta ansa tana godiya tasoma juya wayan ahannunta yinin ranar inty tafuskanci meenal tacanza sam batason magana ko ana hira sedae tai murmushi, kasa jurewa tayi tace pls meenal menene yake damunkine sam bakyason magana yanzu murmushi tamata tace wlh babu abinda yake damuna, to ko inkira miki ya mujaheed?setabawa mimi dry tagirgiza mata kae tace a ah, tom shikenan muje mukwanta kikara hutawa anjima gidan ya sameer zamuje ku gaisa da amarya don shima yace gobe zaku wuce gida,
tunda mimi ta anshi wayan meenal takeson ganin abinda yake cikin wayan amma da security awayan dole takashe wayan ta ajiyeta,bayan ishah su inty suka tafi gidan sameer mujaheed yana driving dinsu mimi nagefenshi se inty abaya suna ta fira har suka karasa bakarya kam gidan sameer yahadu haka auntie salma matarsa tanada kirki sosae se nan nan take dasu tanatama mimi sannu don sameer yabata labarin komae koda yatambayi salma ina sameer tashaida masa ay yana bedroom dinsa, kae tsaye yawuce dakin nasa sukuma ancikasu dakayan ciye ciye,
Akwance yasamu sameer yana danna laptop dagashi se boxer murmushi yayi kawae yazauna kusa dashi yakae masa duka abaya kamar yasani kuwa yazille, yajuyo yazuba masa uwar harara,dry mujaheed yay donya fahimci abinda sameer yake nufi,hannunshi yahade guri daya yarike baki yace oh ni mujaheed shin sameer duka yaushe kasan zakin amarcin nan ne dazaka dinga turomin baki harda hararata munzo mun katsema jin dadi koh inkayi hakuri dagayau bazaka sake ganinaba dakudi seka nemeni,
murmushi sameer yay mesauti yagyara kwanciyarsa yajuyo yana kallonsa yaharde hannayensa abayan kansa yace mujaheed bazaka ganeba ne yau nakeson fara cin amarcina amma don iskanci irinnaka karasa sanda zaka kawomin su inty seda daddare don mugunta irintaka duka sameer yakae masa saboda dariyar dayakeyi masa dan iska ainasan dama dabiyu kaimin haka,saeda nujaheed yay dariyarsa son ransa sanaan ya tsagaita yace kace amarya wanaka takeyi shiyasa naganka duk ba adaidaeba,kallon kafafun sameer yasomayi har zuwa sama,yakuwasa hannu yature masa fuka yace munafiki mekakeson kallone juyawa yay yakifa akwance abinsa yana dariya shima,
Jinjina kae mujaheed yayi yace tabdijan babbabar magana dole ka kasa fitowa kagaisa dasu inty wlh amarya tarufawa kanta asiri tabada kae bori yahau,mintsininshi sameer yafara yana cewa allah yashiryaka mujaheed bansan sanda ka kara zama hakaba duk jarabata ay ban kaekaba tundani bana rawar sanyi dashan magani ehe! kamakalewa 'yar yarinya ai meenal zatae fama da ..... Saurin toshe masa baki mujaheed yayi yace to mara mutumci naji bari nabarma dakin kasan yacca zakayi wlh kafito don bayanzu zamu tafiba, cije baki sameer yay yana girgiza kae yace habawa mujaheed zan ramane,
Mujaheed yana fitowa yasamu salma takunna musu TV sunata kallo abinsu inty tana ganinshi tace kae ya mujaheed harka fito badae tunyanzu zamu tafibah, girgiza mata kansa yayi alamun a ah yana murmushi haka salma itama murmushin jin dadi tayi jin bayanzu zasu tafiba mujaheed na ankare da ita azuciyansa yana cewa habawa yarinya zakiyi bayani ne,fitowansa da dan jumawa sameer yafito shima yazumbula babbar rigarsa ta daurin aure se muzurae yake yazauna kujeranda mujaheed kezaune wanda yaketa faman dry kasa kasa, gaisawa sukayi yanata ma mimi sannu da jiki yalura da dariyar da mujaheed kemasa matsawa yafarayi kusa dashi mujaheed namatsawa shima yana kara matsawa harya kureshi akarshen kujeran seya seya mike yay waje yana murmushi yasan yanzu ze iya kunyatashi gaban kannensa,
Duka hankalinsu nakan TV basusan mesukeyiba sameer yay dry yamike yabi bayanshi yana cewa karamin dan iska dakatsaya kaga meze faru,haka kawae kazomin gida kahanani sakewa,
Awaje suka cigaba dahirarsu gwanin burgewa har lokaci yajama basu saniba intyce tafito tanata kwala musu kira takuwa hangosu zaune saman mota kiran da take musune yasa dukansu suka zuba mata idanu tayi tace ya mujaheed mom ce tace mutaho gida dare yayi,
Cikin masifa sameer yace wani irin shashancine wannan zaki dinga yimana irin wanan kiran ni nazacima wani abune yafaru wlh sim sim itadae takoma ciki, murmushi mujaheed yay yazo dafda kunnensa yace kwantarda hankalinka aibacazatai dakae wani abu yasamu amaryaba daze hanaka cin amarcinka yau bare kasauke mata kwandon masifa yana gama fadin hakan yay saurin dirowa akan motan yay ciki tunkan sameer yay magana, kwafa yayi kuwa yabishi abaya kayan azziki salma tahadawa su inty suna shirin tafiya sameer yace wae meenal meke damunkine naga kinyi shiru kawae abinki, caraf inty tace ay tunda tadawo haka take bamagana gida takeso ay,kallon inty tayi tace allah sis bagida nakesoba kawae maganan ne baya kaena,sameer yay murmushi yacewa mujaheed to inkun koma yaushe zaka maidata gidannasu kenan,ay mimi tanajin haka taji cikinta yabada wani kara jin ashema ba agidansu ya mujaheed takeba, tabdijan babbar magana!
Maganar mujaheed dinne ya katse mata tunani yana cewa muna komawa bawani jumawa zamu tafi ay hutun nasu yakusa karewa sunkusa komawa school don muhammad ma yanata azalzalata,lebe sameer yarike a ah kaji masu kanwa fah jarababbe yanzu dae munji sit abinmu tunda yabar kasar saura shekara nawa yadawone,mujaheed yay dariya yace kaidae bari masifaffen bah saura shekara daya da rabi yadawo, time dinda yashekara biyu ba irin faman dabanyi dashiba yadawo gida yay hutu amma yaki yace wae inya dawo baze kuma komawa ba,sameer yace to kada yakoma mana shifa yayiwa kanshi ay muma hutunmune sosae magan ganunsu suke daurewa mimi kae, ahaka sukayi sallama suka tafi gida zuciyanta cikeda tunani kala kala....

TAKU AKULLUM NANA BMB.

08147110349
[7/28, 8:20 AM] Nana BMB: 💝💖💝💖
RABON KWADO....
BOOK 2

NA NANA BMB
Chapter 5 · 0% Book details