← Book details Rabon Kwado Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 20

Sashe 20

Rabon Kwado Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

page 45
Abinda muhammad yace tayine tasa mujaheed yayi cewar yasanarwa su daddy yana sonta se aureta,mujaheed yayi mamaki dajin wannan furucin daga bakinta haka da wuri beyi mata musuba ya amsa mata zeyi domin baya shakkar tunkarar kowa indae akantane, to haka yadawo parlour yanata tunani yakasa aiwatarwa don kalamin yamasa nauyi kusada muhammad yakarasa yazauna yafada masa abinda mimi tace yakuwa saki kayatatccen murmushi yana kallon mujaheed yaname kara mamakin yadda idanuwan mujaheed suka rufe haka daya kasa fahimtar abinda yake faruwa koda yake kauna dole yamasa uzuri tarufe masa idanuwa, gyaran murya yay yace tome kazauna jira kaje ka aiwatarmana time yana tafiya,mujaheed yarike hannunsa yace pls muje karakani nagaya masa cikin shan kunu yace indae sedani ne to kafasa bama son abin kakeyi bah kenan,mujaheed gajiya yayi yatashi yanufi gurinsu daddy suna zaune da nashi daddyn sunata fira tunda ya tashi muhammad yake kallon ikon allah sosae yakejin zuciyansa tana dancing, koda ya karasa yazauna agabansu kamar me neman gafara yasunkuyar dakansa kasa zuciyansa tana wani irin bugu haka meenal shikawae tazubawa idanu,haka suma su daddy shi suka gubawa idanu ganin irin usmanda yayi agabansu cikin ladabk yace daddy dama inada maganane, kallon juna sukayi su daddy don basu san cikinsu dawa yakeba dagowa yay yakalli daddy sannan yakuma sunkuyar dakansa hakanne yasa yatabbar dashi yake,seya gyara zamansa yace to mujaheed ina saurarenka kaf dakin yadauki shiru kuwa aka zubawa mujaheed idanu, Dama maganace....Mujaheed yay shiru secan yakuma cewa dama maganace akan meenal daddy, tunda yaji ya ambaci meenal yarintse idanunsa cikin wani irin yanayi don yasan meze furta ayanzu,
Dama ina sontane daddy kuma itama tana sona iname rokonka daddy kabani auren meenal tazememin abokiyar rayuwa ta har abada,
Wani krin takaecine yacikawa auntie zuciya jitake kamar ta harbe mujaheed kallon kuma seya koma kan daddy ana tsumayin hukuncin daze zartar, muhammad jiyay kamaryashige huciyan daddy yaga wani hukunci zeyanke ne?bude idanunsa yayi sannan yay gyaran murya yace
Mujaheed!
Na am daddy
Mujaheed inason kasani yadda nadauki muhammad haka kake agurina babu bambamci komene ne kakeso agareni indae dayiwuwarsa to bashakka sena yimaka, to amma batu akan meenal inason daga yauma kasoma kokarin cireta azucinka saboda abinda kukeda muradi bame yiwuwa bane....

TO ME KARATU MUHADU A BOOK 3 INME DUKA YAKAEMU DONJIN YADDA ZATA KASANCE!

SHIN MEYASA DADDY YAHANA MUJAHEED AUREN MEENAL?

TAKU A KULLUM NANA BMB.

MASOYANA INA MIKA DUNBIN GAISUWATA AGAREKU DA GODIYA TA MUSAMMAN.

08147110349
[7/28, 8:20 AM] Nana BMB: 💝💖💝💖
RABON KWADO....
BOOK 2

NA NANA BMB

page 43-44
Meenal ce kwance a kan bed tayi lamo inbanda tunani babu abinda takeyi abin duniya gaba daya ya isheta tarasa mafita kullum cikin damuwa take harta soma ramewa, tayj zurfi cikin tunaninta tajee ana knocking seda ta gyara kwanciyarta sannan tabada izinin shigowa, hasana tashigo dauke da cup ahannanunta tana murmushi tazauna gefenta tana cewa yayarmu tunda kika gama school damuwanki takaru kullum bakida sukuni kuma ummanmu tace ki kwantar da hankalinki akan aurennan naku keda ya bassam nasan bakya sonsa kawae kinawa abbanmu biyayyane kuma baze taba canza maganaba kinsani so kiyi hakuri kada kisa damuwa aranki tadameki ko bakomae ya bassam yana matukar kaunarki zakiji dadin zama dashi kema kuma nan gaba zaki soshi,
Hawaye meenal tafara don yanzu ba abinda tafi tsana samada ai mata maganar aurennan danasani kullum tanayinta dabata yimusu bayani tunfarko kota wani hali kuwa bazata bari ta auri ya bassam be kome zefaru sedae yafaru yayanta kawae yake fado mata arae tasan yanzu yadawo gida saboda bata taba bata a lissafintaba tunda yatafi,hannun hasana tariko tace hasana ina cikin wani hali bazaki ganeba nasa yadda zanyi da rayuwata, jikin hasana a sanyaye tace kiyi hakuri yayarmu ki fawwalawa allah komae tamika mata cup din tace gashi ummi tace kisha akae mata cup din,ran meenal yakara baci saboda bata kaunar irin abubuwan nan da ummi take bata tunda aurensu yakusa fuska adaure ta anshi abin cikin cup din tshanye tabata cup din, hasans tafito cike da tausayin yayar tasu kods tasauko tasami bassam azaune suna hira da twins da ummi cikin cukurkude fuska tanemi gu tazauna cikin ko in kula yace ke jeki kiramin yayarku, hasana ta tabe baki itama tace yayarmu tayi bacci,
Bai kukalataba yadauka wayansa yacilla mata yace jeki kaemata inason muyi magana ne nakira ta ta wayan akashe cikin tura baki tadauki wayan kuwa takoma gun yayar tasu sam itama bataji dadin kawo wayanba don sabodashi takashe wayanta seda suka gama wayan tabawa hasana wayar tamayar masa koda tasauko twins kawae tasamu a apalour din ummi tana dakinta shikuma yafita answer waya da dayan wayan nashi hakanne yabata damar zama tasoma bincieke awayan tana shiga inda ranta yamata tana cikin kallon pictures a wayan taganowa kanta abinda yadaga mata hankali tamike dasauri tashige dakinta tacigaba da kallon hotunan jikinta har bari yake saboda tsoro duk rabin hotunan bassam ne shida mata fitsararru babu kayan mutumci ajikinsu wanda dasuma gara babu wasu sun makale masa ajiki hawaye kawae taji yana bimata ido,
Koda bassam yadawo yace wae twins hakasan bata sauko bane haryanzu suduka sukace tasauko mana tundazu tashige bedroom, jiyay wani daram kirjinshi yaharba inibin dayake shirin kaewa baki ya saki tsam yamike ya nufi daki, kallonta kawae take tana hawaye tana cewa allah ya isa ya bassam wlh yau allah ya toni asirinka bazaka taba auren yayarmuba ashe kae dan iskane dama tokuwa sena kaimata taga abinda kake aikatawa yaudararta kakeyi tanata masa ibar albarka, tadagowar dazatayi taganshi jingine a kofanta yana kallonta saboda firgita tamike batasanma tasaki wayanba tasaka kuka tana cewa kuma wlh kome zakayimin sena gayawa yayarmu don bazan bari ta auri dan iskaba hakanne yasa yasoma nufuta ahankali tanaja baya fuskarsa babu alamar rahamar annuri atare da ita seyanzu yake danasanin bawa hasana wayarshi dayay don yamanta ba security, harseda tadangane da jikin bango yazo dafda ita ya nunata da yatsa yace kewacece dazaki hanani auren my meems yarinya duk duniyar nan babushi sannan kuma wayace kiyimin bincike awaya?cikin zafin rae tadago btace saboda allah yatoni asirinka wayanka tazo hannuna yau tasss bassam yadauketa damari tasa hannu biyu kuwa tadafe fuskannata tana kuka cikin bakin ciki yace ke wace irin dakikiyace saboda kinganni da mata zaki kirani dan iska saboda bakida kwakwalwa mekyau kisake gangancin cemin dan iska kiga abinda zanwa shegen bakinnan naki mara kunya, hasana takuma kulewa cikin rashin tsoro tadago tace ayba karya naiba anfada din yayarmuce kuma daga yau kasa aranka bakae ba ita donsena tonama asiri katafi can kasamo matarka amma ba ah gidanmuba,
Cikeda mamaki bassam yake kallon hasana yarasa meyasa hasana batajin tsoronsa koda kuwa meze mata bata shakkar yimasa rashin kunya tunani yayi tabbas yakyale yarinyar nsn wlh seta ballo masa ruwa yanagani burinshi yakusa cika so dole yadauki mataki, murmushi keta yasaki sanan yakara matseta abango yay mata rumfa ko kyallinta ba ah hange yarufeta seda suka kwashi mintina ahaka ba umm ba um umm sannan yadago fuskarsa daukeda kaya tatccen murmushi yajuya yadauki wayanshi data yar yatafi seda yabude kofa zefita yajuyo yace no problem ayanzu zaki iya fadin abinda kikeso nima nasami nawa abin fadan so ki gwada kiga meze faru, yay ficewarsa yabarta ajiki bango hawaye shabe shabe zuciyarsa kuna kawae takeyi tafada kan bed tasoma kuka me cin rae,
WASHE GARI
Tunda su mummy suka tashi suka soma shirin tafiya mimi kuwa tunda ta tashi tarasa sukuni har sukae breakfast mujaheed yana kula da halinda take ciki sam muhammad ko inda takema be kallaba hakanne yakara tabbatarwa daddy da akwae matsala bayan gamawarsune suna parlour nana ta dafata tace meenal wae meyake damunkine nigaba daya natasa gane kanki yanzu wlh, zuciyan mimi bugawa kawae take tarasa ta ina zata fara tana cikin tsaka me wuya tanason mujaheed matuka kuma ayanzu idan tafurta to nana tasmmu abinyi zata kwacewa meenal youseep "NIKUWA NACE HMMMM" ganin tarasa mafitane yasata hayewa sama takira mujaheed koda yaga haka yasan akwae magana mikewa yay yabar palour din don answer wayan muhammad nakula dasu yana murmushi kawae soyake kafinsu daddynshi sutafi ayi komae yau ayita takare yau zefadima kowa yasan cewa wanann ba ita bace meenal....

TAKU A KULLUM NANA BMB.

08147110349
Chapter 20 · 0% Book details