← Book details Rabon Kwado Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 20

Sashe 3

Rabon Kwado Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

page 7-8
Yana gama fadin haka yakashe wayansa yadaga mata kafa takuwa sa hannu biyu tarike kafan tana matse inda yataketa, da razanannar voice dinsa yasunkuyo yafara cewa saura kadan ubanki yayi abinda mukeso daganan zan turaki kiyama natura masa da gawarki kada sam kisa aranki zaki zaki fita darae a dakin nan sam bazaki kubuta ahannunaba bantaba sace mutumin daya bani wahalaba kece wadda kikafara samun daman guduwa keme wayau hukuncin abinda kikayi kuwa dama mutuwa kuma daga yanzu bake babu cin wani abu harzuwa lokacinda zan harbeki,
Tuni meenal tamanta ma dawani ciwon kafa jin kalamansa gaba daya tafice ahankalinta cimimiyo masa riga tayi tana cewa nashiga ukuna don girman allah kayi min rae kayarda dani wlh bani bace wadda kuke nema karka kasheni ni sunana meenal ba mimi ba,sosae yakara kufula ganin irin raenin hankalinda zatayi masa garikon datayi masa yadda tadimaucema seta bashi dry koyaushe tasoma tsoron mutuwa haka,cireta kawae yayi awuyansa hannu biyu yasa yadamki wuyanta cikin karaji dazare idanu yace idan kika sake cemin bake bace mimi sena markadaki digi digi zanyi dake yarinya babu abinda nafi tsana sama darainin hankali to amma kigwada kigani yarinya idan zaki kuma kwana aduniya kinji menace ay,saurin daga masa kae tayi tana numfarfashin suma,sakinta yay tazuve agurin tasoma tari kaman zata mutu ido yay tulu tulu,abinda yadaure mata kae shine ganin bango datayi yabude wannan mutumin yafita yakuma dawowa yakoma ganin hakanne yakara sawa jikinta yin sanyi datsinkewa da wannan al amarin duk addu ar datazo bakinta yitakeyi tama kasa kukan sabida tashin hankali tana cewa meyake shirin faruwa danine ya allah,
BAYAN KWANA 2
Takama ranar daurin auren sameer kenan mom tazama busy sosae saudaya take samu tazo hospital shima seda daddare kullum dabakin dake zuwa haka suma su sameer din sae sun dage suke zuwa asibitin sau biyu,sunata saukan bakinsu suma jikin mimi yayi sauki sosae se 'yan raunikanta dabasu gama warkewaba wannan dalilinne yasa mujaheed sakewa sosae ana shagalin biki banda zara da mimi suna asibiti abinsu zara hartama saba darashin maganar mimi yanzu don semagana takamata dole takeyinta,suna zaune sunacin abinci ko ince zara kadae tunda ita mimi juya spoon din hannunta kawae takeyi bataci,kallonta tayi tace wae meenal meyasa yanzu bakyason magana sedae kiyi shiru kowani abun yana damunkine gaba daya kin canza,mimi tae murmushi tace zara bakomae maganarne banajin yinta kawae,jinjina kae tayi tace tom shikenan kici abincin koh kidena juya spoon din din haka,ajeshima tayi tamike takoma kan bed tana cewa no nama koshifa,damamaki zara tace mekikaci dazakicemin kinkoshi kinga kisauko kici abinci sarae kinajin abinda nurses suka ce akanki koh kidena zama da yunwa yanzu cikinki zefara zafi kada kizauna jiran ya mujaheed domin yau busy dinsu yafi nakullum balallae suzo da ranaba sezuwa dare nasan zezo seya baki nadaren kici abinda kikeso dae kenan koh, donhaka kisauko yanzu kona kira miki mom nasanar mata,
Turo baki kawae mimi tayi jin zara ta ramfota ga haushinda yacikata sam bataga mujaheed ba yau dukse takejin haushi,kamar tayi kuka tace nifa nakoshi kawae nidae ki kiraminshi awaya,sakin baki zara tayi tana kallonta sannan tace wlh bazan kirashi yanzuba suna tsaka da tarbar mutane sedae nakira miki mom barima kigani wayanta tadauka tayi kiran ganin dagaske take yasata saukowa tasoma tsakuran abincin tana hararan zara takasan ido, ita drym tabata ana daga wayan tayi sallama takuwa marae raece fuska tace pls zara bagashi inaciba kada kigayamata,murmushi tayi mata tacigaba da maganarta tace sis yataron biki andaura aure yanzu koh,inty tashaida mata andaura komae lpy, to masha allah yasanya alkhairi yabasu zaman lpy ya albarkaci rayuwar aurensu,tace ameen
Zara ina mutuniyata i hope dae tanajin sauki sosae zara tasaki murmushi mesauti takalli mimi tanata juya spoon din hannunta alan dole ita abinci takeci,sannan tace inty mutuniyarki lafiya tananan tanata zuban rigima harda harara naki kira mata mutumin,kinsan yau basu zoba,dariya inty tayi sosae tace kema laifinkine waya gayamiki ana shiga tsakaninsu zaki iya ganinshi yanzun nan kuma kiji kunya,haba zara tarike tace wlh sister naga alama domin mitanen nakifa ana zazou segodiyan allah,murmushi tayi tace wlh ni wlh burgeni sukeyi sosae meenal da ya mujaheed suka dace dajuna inason meenal dayawa jinake dama inbiyoku hospital dinma,murmushi maryam tayi tace a ah kitaho kuma kiyi yaya dabakin namu bari dae nabaki ita kuyi magana,mika mata wayan tayi ta ansa tana tura baki suka gaisa yacca take mata maganarma suduka setabasu dariya,inty tace meenal kada kidamu kinji yanzu zannemo miki ya mujaheed dinki yazo gareki kokyadena fushin nan ay kuwa mimi tasaki murmushi tace to nagode tamikawa zara wayan sukae sallama suna dry.
Suna zaune tayi jugum shi kawae takeson gani duk haushi yacikata saboda yaki zuwa itakuwa zara charting take abinta suna haka,yaturo kofan yashigo da sallamarsa tayi saurin daga kanta kuwa suna hada ido tasauke ajiyan zuciya because yayi kyau matuka yasha kananun kaya abinshi bakake tuni yacire manyan kayan na dauren aure saboda zafi hannunshi dauke da juice dayan hannun kuma wayanshice yarike murmushi kawae yake zuba mata harya karaso yazauna gefen bed dinnata, sam beji sallamar da zara take amsa masaba ma,ko ina kamshinsa yagauraye room din sosae farin ciki yallubeta naganinshi datayi, amma seta turo baki itafa anbata mata rae se atime din yajuya suka gaisa da zara tacigaba da danna wayanta haka shima ya aje juice din yana danna tashi wayan, habawa takaeci kuwa yacikata tasa musu kuka,
Hanzarta ajiye wayar yayi yakamo hannunta yana cewa sorry my dear meyay zafine haka nazo ko kulani ma kinkiyi,kara tunzura baki tayi tace to bakae bane kaki zuwa inda nake kuma kazo shine kashareni,hadiye dariyarsa yayi is ok sorry kinji kinsan yadda aiki yamana yawa yau yanzuma nikadae ne bazan iya jurewaba na aje komae nataho sameer yanacan yacedae namiki sannu, ina fata dae kinci avinci baki zauna dayunwaba?
Shiru tayi masa, zara tace inafa kaema kasan bazata ciba tunda baka zoba tundazu nake fama da ita takici wae saina kiraka, saboda nakine tundazu aketa antayamin hararan kasan ido,wani farin cikine yaziyarci zuciyansa yasaki lallausan smile yace aida kinkirani zara don meenal tafi min komae agurina ay, murmushin jin dadi kuwa mimi tayi har beauty point dinta suka lotsa wanda sam bekae na meenal ba ita intana magana har bayyana suke,amma sam bawanda ya ankara acikinsu gwalo tajuya taewa maryam alamun an gwaleta, bani abincin zara yanzu zataci kuwa takoshi mikewa tayi tadauko abincin tabashi tafita abinta domin answer waya,bata abincin yake cikin nutsuwa tana karba harta kusan cinye abinci tashagala da kallonsa hankalinshi yanakan abincin koda yadago zemata magana yaga yadda takafeshi da ido shima kanshi yana mamakin yadda meenal kemasa irin wannan kallon haka murmushi yaymata ya hura mata iska a fuskanta yace yadae,murmushin kawae tayi tasunkuyar dakanta,meenal yanzu kinacin abinci sosae nagode allah sosae su mummy nasan zasuji dadin hakan seda takoshi kadan yarage abincin,sannan yasoma bata lemun daya shigo dashi tanasha wayarsace tafara ruri alamun ana kira kallon wayan yayi besaniba yasheka mata ajikinta jin saukan ajiyan heart dinta yayi lemun dasanyi gashi yana ratsata,dafe goshinsa yayi yace sorry meenal tissue yaciro yasoma goge mata lemun dadan sauri sauri yakeyi don kiran yakara shigowa besaniba yagoga maga kan kirjinta gurin ciwonta tasaki siririyar kara, koda yakkalleta yaga idonta tafda kwalla yamutse fuska yay cikin tausayi yace ya allah wlh namanta kinada ciwo duk muhammad dinkine yarudani kwana biyu yahanani sakat sena hadaku awaya so banason kowa yasan abinda yafaru shiyasa banbashi ke kunyi maganaba, yanzuma ina rokonki idan kunyi magana kada kigaya masa kinji kisaki jikinki sosae kada yagane,ay mimi cikinta wani kadawa yayi tana masa kallon rashin fahimta zuciyanta nabugu to waye kuma muhammad....

TAKU A KULLUM NANA BMB.

08147110349
[7/28, 8:20 AM] Nana BMB: 💝💖💝💖
RABON KWADO....
BOOK 2

NA NANA BMB
Chapter 3 · 0% Book details