← Book details Rabon Kwado Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 20

Sashe 4

Rabon Kwado Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

page 9 -10
Koda yadago yana kallonta yaga yadda tazuba masa idanu cikeda tsoro setaso bashi dry ma hannunta daya matsane yasata dawowa cikin tunaninta,murmushin karfin hali tamasa yace yadae kada nakirashine kasa bashi amsa tayi tanadan kallonshi kamar mara gaskiya tambaya yajeho mata wae ina kikasa wayankine agidansu inty koda ita kika tafine tafadi ahanya, yace yanata kiran wayanki akashe haka su aunty suma,dan saisaeta kanta tayi tadukanda kanta don tarasa bakin magana,yana sauke idanunshi kan kirjinta yaga dan jini yabata mata saman rigarta kadan dake milk ce cikin damuwa yace hasbinallah meenal haryanzu baki warkeba agurinnan kallonshi tae taga meyake magana akae taga yana kallon kirjinta tayi ssurin maida kanta kasa kuwa, bazato ba tsammani taga yakae hannu kan kirjin nata gefen rigar yadan janye yana kallon karcewar da tayi yana yamutsa fuska kanar zeyi kuka yanzunma dayatsansa daya yadan shafi gurin yace ina maganin dakike shafawa agurin?lumsassun idanunta tabude tayi masa nuni da inda inda suke a ajiye yadauko yazauna kuwa dakanshi yasa tissue yagoge mata gurin yashafa mata maganin harya gama idanunta yana lumshe, gyara zamansa yayi sannan yakira muhammad koda yakara waya akunne yace sorry muhammad gata ay yanzu nashigo ne,mika mata wayan yayi ta ansa hannunta narawa tamkar anmata dole tace hello! cikin fada kuwa yace wae baza ah bawa meenal wayanba ne bae rufe bakiba yaji tace ina wuni,bae amsataba kawae yace bawa mujaheed wayan mika masa wayan tayi jikinta asanyaye,tsaki yay ya anshi wayan yace to meye kuma,mujaheed nizaka rainawa hankali ina meenal take,da mamaki mujaheed yace bangane ba ayni haka raenawa hankalin bagata tanama maganaba kace tabani gata ni cikin haushin yamika mata wayan,koda takara wayan akunne sunan daya kirata dashine yasa zuciyarta rudani sweety yakara kiran sunanta, cikin sanyin muryanta tace na am dan shiru yayi sannan yace meyake damunkine kifadamin gaskiya,babu komae babu abinda yake damuna dama yamata tambayarne donyakarajin muryanta,bashi wayan shine kawae abinda yafurta tabashi wayan kuwa ta lula duniyar tunani shin towaye wannan kwalla taf a idanunta,yankewa tunaninta yayi jin mujaheed yayi sama da ita abakin kofa yasauketa yasaurin zura mata hijab dinta na sallah yakama hannunta suka fita harcikin mota yasakata sannan yakuma kiran muhammad amma vidio call ya aje mata wayan kan cinyarta yazauna gefe shima yazuba mata ido, ya allah koda suka hada ido tacikin waya kasa kuma kallonsa tayi dagashi se gajeren wando iya gwiwa,dakyar ta iya kakalo murmushi tace sannu yaya kana lpy baima jitaba saboda irin kallonda yake mata,cikin tuhuma yace ina wayanki kika kaeta?tayi shiru cikin jin haushin hakan yace badake nake maganaba ne, yaya bansan inda takeba wlh,yayi kyau bakisan inda takeba sam babu abinda yadameki saboda kinsamu freedom na yawo ko bakidamu da halinda zamu shigaba kullum zuciyata cikin fargaba take da tunani marasa dadi akanki daddy yakikkira kinki daga wayan karshe wayannaki akashe su nana harsun gaji dakiranki ma, ko awayan mujaheed base ki kiramuba wani irin haline kikeson daukane yanzu?
Kayi hkr yaya bazan sakeba tayi maganar idonta tafda kwallah zatayi kuka har mujaheed seda yayi mamakin yadda takewa muhammad magana,MEENAL! yakira sunanta zuciyarshi tabda tambayoyi kala kala, meyake damunki?yanzunma bata dagoba tace bakomae,sosae tabashi haushi kawae yakashe wayanshi ma,
Da mamaki mujaheed yace meenal meyasa zakiyi masa magana ahaka ne sokike yagane bakida lpy,tagirgiza masa kanta,to kada kikuma amsashi awannan mood din pls kisaki jikinki,yanzunma kae kawae tadaga masa yakama hannunta suka koma cikin hospital din se kallon ko ina take harda wae waye saboda time dinda aka shigo da ita cikin asibitin bata hayyacinta sun shiga room din datake zara tana zaune tayi tagumi tana ganinsu kuwa tasaki murmushi tace ya mujaheed ina kukajene ina nan har tsoro yasoma kamani,murmushin yamata shima yace nakaeta motane tayi waya da yayanta kinsan basusan abinda yafaruba bawanj guri tajeba ay, wae zara kinsan inda wayan meenal takene,tagirgiza masa kae alamun a ah, bewani zaunaba yay musu sallama yatafi don jiranshi su sameer sukeyi,
Tana kwance duk ta rame tabushe dakyar take bude idonta haka zama ma gagararta yakeyi saboda yunwa ta dagazata ruwane kawae take iya samu tasha abayi,numfashintama dakyar yake fita bata kara ganin mutuminba tundaga ranar hawayene kawae yakebimata fuska data lumshe idanunta lapiyayyaen abinci take hangowa tana hadiyar yawo,cikin wahalalliyar muryarta take cewa ya allah kadauki raena kozan huta dawannan ukubar sun tafi sun barni da yunwa ko kukama kasawa tayi,baccin wahale yadauketa kamar amafarki kuwa taji shigowan mutumin tabude ido ahankali taba wanan gardin mutumin shine dae yadawo hannunsa daukeda bindiga dakuma cup tayi saurin tashi zaune cikin tashin hankali take kallonsa harya karaso ya tsugunna agabanta, batare dayayi maganaba yamika mata cup din hannunsa, bamusu kuwa ta ansa fresh milk ce aciki batajira meze ceba takafa baki tas tashanyeta dataga hakan bematabama tasa hannu tana lashe kofin, yadda takeyi nema tabashi dry yay murmushi,cup din ya anshe yamika mata waya takuwa ansa takara akunne dukda hankalinta yanakan bindigar dayake nunata da ita,hello! tacikin wayan kuwa taji kukan wata mata tana cewa mimi ina fata dae basuyi miki komaeba nakasa bacci diyata narasa inda zan tsoma rayuwa, shiru meenal tayi saboda yadda kukan matan yake taba mata zuciya basuyimin komaeba tacewa matan, to nagode allah mimi kiyi hkr kinji allah ze kubutar dake kullum cikin addu ah muke yimiki, kasancewa meenal ba itabace mimi yasa hawaye zubuwa daga idanunta masu zafi kafin tayi magana kuwa ya anshe wayan yakashe tasoma binsa da kallon tsana,da murmushi yamike yace madarar dakikashace tasaki jin kwarin gwiwar yimin rashin kunya kiyi kome kikeso duka kwana nawane yarage miki aduniya,ficewa yayi abinsa,tabishi da harara sam tadena tsoron mutuwar ma ko kadan muryan matarne kawae yake mata yawo ajiki, mikewa tayi tayo alwala tazo tasona sallah abinta don ayanzu itace mafita agareta, tana idarwa tasoma rero karatun Alkur ani,
washe gari
Su sadiyane sukazo yiwa meenal sallama zasu tafi gida domin biki yakare jiya anmika ango dakinsa,duka dasu mom akazo da inty, gashi harda zara za ah tafi hakanne yasata samusu kuka wlh ita se ansallameta, mujaheed azuciyansa yace daman nasan za ah rina haka, lallabata yasomayi cewan tabari tadan sami sauki,mom tace a ah mujaheed kira doctor dole amata abinda takeso aitamayi har aka gama biki tana asibiti,zara tayi dry tace kinji mom itama banata bikin takeyi anan bah suduka sukasa dry kuwa banda mujaheed dayayi murmushi kawae yana kallonta ta tura baki gaba tana hararan zara,sunsha hira sosae sanan doctor yasallamesu suka tafi gida da murnarta se kallon gari take abinta. ...

TAKU A KULLUM NANA BMB.

08147110349
[7/28, 8:20 AM] Nana BMB: 💝💖💝💖
RABON KWADO....
BOOK 2

NA NANA BMB
Chapter 4 · 0% Book details