Sashe 9
Nihad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A wani zamani mai tsawo da ya shuɗe a cikin ƙasar Sin an yi wata gagarumar bokanya mai suna Tazibul Luhucul. Masu harsashe a wannan zamani na ta babu wata 'ya mace mai yawan shekarunta a duniya,domin a ƙallah bata bar duniya ba sai da ta shekara ɗari da saba'in. Har ta mutu ba ta taɓa yin aure ba,kuma ba ta taɓa haihuwa ba. Tazibul Luhucul ta fara bokanci ne tun tana da shekara bakwai sa'adda ta yi ƙawa da wata aljana 'yar sarkin birnin Sin wadda ake kira Saubatul Azwas. An haifi Tazibul Luhucul da Saubatul Azwas shekara ɗaya, rana ɗaya,kuma lokaci guda. Tun sa'adda sarkin aljanun ya fuskanci baka sai ya ƙudure a ransa cewa sai ya haɗa ƙawance tsakanin 'yarsa da wannan bil'adama wadda aka haife su rana guda. Saboda haka tun Tazibul Luhucul ba tafi shekara biyu a duniya ba ya zamana ya buɗe mata idanu tana iya ganin kowanne irin aljani ba tare da ta tsorata ba. Kuma kullum sai ya kawo mata Saubatul Azwas sun yini suna wasa tare. Tun mahaifiyar Tazibul Luhucul ba ta fuskanci abin da ke faruwa ga 'yar ta har ta fara ganin abubuwan al'ajabi a tare da ita. Sau tari sai ta ga Tazibul Luhucul ta ɗauki abu mai nauyi wanda sai ƙarti arba'in sun taru za su iya ɗaukarsa. Haka kuma duk maganar da za ta yi sai ka ji cewar magana ce ta babbar mace mai hankali da nutsuwa. Daga nan kuma sai ta fara faɗin abubuwan da zasu faru a gaba a birnin Sin. Duk abin data faɗa kuwa sai a ga ya tabbata. Haka ma duk irin cutar da mutum ke yi in dai aka ɗauko shi aka kawo shi gaban Tazibul Luhucul a bashi magani take zai warke. Yayin da jama'ar birnin Sin suka ga baiwar Tazibul Luhucul ta yi yawa sai suka shiga girmamata ainun,har ta kai cewa ma ana bauta mata,kuma duk dokar da ta kafa kowa na binta,har shi kansa sarki Alyasil buhus wanda ke mulkin jama'ar kasar Sin gaba ɗaya a wannan lokaci. Lokacin da sarki Alyasil Buhus ya ga irin girmamawar da akewa Tazibul Luhucul ya zamana an bata matsayin abin dogaro sai hankalinsa ya dugunzuma ya fara tunanin cewa lallai da sannu wannan bokanya za ta raba shi da karagar mulkinsa. A bisa wannan dalili ne ya tara 'yan majalisarsa a ɓoye don su tattauna wannan matsala a keɓaɓɓen wuri. Bayan dukkanin 'yan majalisar sun hallara sai sarki ya miƙe ya gaishe su sannan yace, "Yaku 'yan majalisata kun sani cewa a halin yanzu wannan sarauta tamu ta shiga wani mugun hali na rashin ɗorewa domin kuwa yanzu talakawan mu basa jin maganar kowa face ta bokanya Tazibul Luhucul. Tabbas al'amarin wannan bokanya da ban tsoro yake,kun sani cewa ba zamu iya yin yaƙi da ita ba,kuma ba zamu iya korarta ba daga cikin ƙasar, yanzu mene ne abin yi? Ban tara ku anan ba dan komai sai don mu yanke shawarar da za ta fishshe mu don mu tsira da mutuncin mu,kuma mu tsira da mulkinmu." Yayin da sarki Alyasil Buhus ya zo nan a zancensa sai gaba dayan 'yan majalisar suka ruɗe, hankalinsu ya dugunzuma. Tsawon daƙiƙa ɗari da sittin ɗayansu bai ce uffan ba. Daga can sai waziri yayi gyaran murya yace, "Ya shugabana ka yi sani cewa idan har muna so mu tsira da mutuncinmu da mulkinmu dole ne mu cire tsoro daga zuƙatanmu,walau dai mu je mu zauna tare da wannan bokanya mu nemi sulhu ta fita daga ƙasar nan ko kuma mu yi tarar aradu mu koreta da ƙarfin tsiya,tun da dai bamu jarraba yin hakan ba mun kasa. Kasan ance a rashin tayi ake barin araha." Caraf sai Galadima ya tari numfashin waziri yace, "Haba waziri ya za'a yi mu yi irin wannan gangancin. Ai shi yaƙi ɗan zamba ne,idan har muna son haƙanmu ya cimma ruwa dole haɗa da yaudara. Tabbas za mu yi nadama idan muka ce za mu yi fito na fito da bokanya Tazibul Lubucul." Koda galadima ya faɗi haka sai sarki Alyasil Buhus yayi ajiyar zuciya,sannan ya dubi kowa yace, "Haƙiƙa kai ma ka zo da uzuri babba. To wai shin me zai hana mu je mu nemi sulhu da ita?" Kamar haɗin baki sai gaba ɗayan 'yan majalisar suka amince da wannan shawara ta sarki Alyasil Buhus,kuma aka tsaida magana akan cewa gobe da safe za su ɗunguma gaba ɗaya su je kogon tsafin bokanya Tazibul Luhucul don warware wannan matsala. Kash rashin sani yafi dare duhu. In da sarki Alyasil buhus da 'yan mjaitsarsa sun san abin da zai biyo baya da basu yanke wannan shawara ba. Kashe gari da hantsi sarki Alyasil Buhus da 'yan majalisarsa gaba ɗaya suka yi hawa suka tafi izuwa kogon tsafin bokanya Tazibul Luhucul. A wannan lokaci Tazibul Luhucul ba tafi shekara tamanin ba a duniya. Koda zuwan su sarki Alyasil Buhus bakin kogon sai suka ja dunga,suka yi crko-cirko,suna masu kallon kogon wanda ya kasance a rufe ruf babu wata ƙofa ko kafar shiga. Nan fa suka yi tsuru-tsuru suna kallon juna,suka rasa abin yi. Suna cikin wannan hali ne suka ji wata irin mahaukaciyar dariya ta cika jejin gaba daya cikin amo da amsa kuwa. Ba zato kuma ba tsammani sai ga wani murgujejen aljani mai ɗan ƙanƙanin kai da tsawo kamar shantu ya bayyana. Yana da faffaɗan ƙirji cike da gashi,mai faɗin kamu ɗari. Hannayensa dogaye ne zanƙala zanƙala,kuma sirara tamkar wuyan zalɓe. Ƙafafunsa kuwa guda huɗu ne murtuka-murtuka kamar bishiyar kuka. Saboda tsananin ƙarar dariyar wannan aljani sai da su Alyasil Buhus suka ji kamar kunnuwansu za su toshe. Ba shiri suka faɗo daga kan dawakansu suna masu tohe kunnuwansu da hannuwansu. Iskar bakin aljanin kuwa ta tashi hankalin komai da ke wajen hatta duwatsun wajen sai da suka kama girgiza. Lokaci guda aljanin yayi tsit, komai ya tsaya cak. Kafin su sarki Alyasil Buhus su buɗi baki su ce wani abu tuni aljanin ya feso musu iskar bakinsa,take suka rikida suka zama guguwa. Aljanin ya cire wata battar fata dake ɗaure a ƙugunsa ya buɗe sai guguwar ta shige ciki,sannan ya rufe. Kawai sai ya ɓace ɓat,bai bayyana a ko'ina ba saà a tsakiyar cikin kogon bokanya Tazibul Luhucul. Babu yadda za'a yi mutum ya tsinci kansa cikin wannan wuri ya yarda cewa a cikin kogo yake,domin kuwa gaba ɗayan wajen a gine yake da dutsen lu'u-lu'u. Kayan ƙawa kuwa gasu nan iri-iri birjik iyakar ganin mutum. Zaune akan wata karagar zinariya kuma riƙe da gajeriyar sandar tsafi tsohuwa Tazibul Luhucul ce. Tazibul Luhul ta kasance 'yar tsarmurmura kamar a hureta ta faɗi,duk da ta kasance tsohuwa tana da kyawun fuska,kuma babu wani abun muni a jikinta. Ko yaushe fuskarta a cikin annuri take kamar ta mai tausayi da imani,amma kuwa al'amarin ba haka ba ne,domin zuciyarta baƙinƙirin ce cike da mugun nufi da rashin tausayi. Koda bayyanar aljanin sai ya yi sujjada a gareta ya miƙa mata battar tsafin. Ita kuwa sai ta miƙe zumbur ta karɓi battar ta ɗaga ta sama,sannan ta kece da dariyar mugunta. Sai da ta jima tana dariyar sannan ta dubi aljanin tace, "Gaishe ka Haddagul Gubur. Haƙiƙa yau kayi mini kyakkyawan aiki." Haddagul Gubur yayi murmushi yace, "Godiya nake uwar bokaye." Ba tare da ta ce komai ba sai ta sake buɗe battar fatar nan. Tana buɗe wa guguwar ciki tayi fitar burgu ta zuba ƙas ta rinƙa katantanwa waje ɗaya. Tazibul Lubucul tayi nuni ga guguwar da sandarta ta tsafi,tana mai cewa, "Gaa ɗayanku ku zama naƙasssu masu mutuwar ɓarin jiki." Rufe bakinta keda wuya sarki Alyasil Buhus da 'yan majalisarsa suka bayyana gaba ɗayan su a kwankwance kowannansu rabin jikinsa a shanye. Koda suka dubi jukunansu suka ga halin da suka kasance,sai duk suka fashe da kuka suna masu tuba ga bokanya Tazibul Luhucul. Ita kuwa sai ta ƙyalƙyale da dariya lokacin da suke ta roƙonta. Lokaci guda kuma ta daka musu tsawa ta murtuke fuska tace, "Kaicon ku waɗannan sarakuna. Lallai ba zan taɓa yafe muku ba,domin kun kawo matuƙar raini a gareni. Shin kuna tsammanin har akwai wani abu da za ku ƙulla a sirrance wanda ban sani ba? Duk abin da kuka shirya a majalisa jiya na gani,kuma na ji. Ina tabbatar muku da cewa sai na nuna muku cewa ni Tazibul Luhucul nafi gaban raini. Kai bama ku ba gaba ɗayan manyan sarakunan duniyar nan kun jawo musu bala'i. Na rantse da darajar ƙarfin tsafina,duk wanà sarki mai ji da kansa dake cikin duniyar nan da 'yan majalisarsa gaba ɗaya sai na maishe su Naƙasssu kamar yadda na maida ku yanzu. Yayin da Tazibul Luhucul ta zo nan a zancen ta sai sarki Alyasil Buhus ya yunƙura da ƙyar ya jingina kafaɗarsa jikin wata kujera yana mai fuskantar Tazibul Luhucul yace, "Yake wannan matsafiya naji duk abin da kika faɗi,kuma na tabbatar da cewa ba za ki yafe mana ba,amna ina son na nemi alfarma guda biyu a wajenki saboda albarkar darajar ɗaukakarki da girmanki a wajen al'ummar ƙasar nan,ina son duk abin da za kiyi mana kada laifinmu ya shafi zuri'armu. Alfarma ta biyu ita ce ina son ki sanar damu yadda zamu samo maganin da zamu warke daga wannan cuta,don ya zamana koda ba kya raye a doron ƙasa zamu iya ƙoƙarin nemo maganin,duk da cewar kuwa mun san cewa ba za mu iya samo maganin ba,amma ai mai rai baya fitar da rai da samun rabo." Koda jin wannan batu sai bokanya Tazibul Luhucul ta ƙyalƙyale da dariya har sau uku sannan tace, "Yakai wannan sarki ka yi sani cewa ba'a taɓa neman alfarma ba a wajena na ƙi yi,face abin da dama na yi rantsuwa akan ƙin yinsa. Bisa wannan dalili na rantse da darajar tsafi ba zan taɓa cutar da iyalanku ba,kuma zan sanar da ku yadda za'a samo maganin da zaku sha ku warke daga wannan cuta gobe daddare,ku yi sani cewa bayann zai riskeku cikin gidajenku." Tana gama faɗin hakan ta dubi aljani Haddagul Gubur tace, "Maza ka kwashe su ka maida kowa gidansa,domin iyalinsu su cigaba da yin jinyarsu bisa wannan cuta ta ajali domin kuwa ita ce sanadiyar mutuwarsu. Tabbas babu wanda zai ƙara shafe sama da shekara uku nan gaba