← Book details Nihad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 20

Sashe 11

Nihad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fadar yana katantanwa a waje guda. Koda ganin hasken sai Tazibul Lubucul ta miƙe zumbur cikin farin ciki ta nufe shi. Kafin ta isa gaban hasken tuni ya rikiɗe ya zama wata kyakkyawar aljana wadda ke riƙe da sandar tsafi iri ɗaya da ta Tazibul Luhucul. Nan take wannan aljana ta rungume Tazibul Luhucul suka sumbaci junansu,cikin tsananin farin ciki. Aljanar ta dubi Tazibul Luhucul cikin murmushi tace, "Gaishe ki ƙawata,haƙiƙa duk abubuwan da na umarce ki da yi kin yi su daidai. Ina mai yi miki bushara cewa burin mu ya kusa cika. Tabbas idan muka sanya wannan cuta a jikin manyan sarakunan duniya na bil'adama zamu gano inda wannan sirrin tsafi guda ɗaya yake wanda ya gagaremu samu." Tazibul Luhucul ta yi murmushi gami da ƙyalƙyalewa da dariya, sannan tace, "Yake Saubatul Azwas ki yi sani cewa raina cike yake da farin ciki bisa wannan bushara da kika zo mini da ita,kuma dama ke nake jira ki iso,domin na tara dukkanin hadimaina gasu suna jira sai ki faɗa mana yadda zamu kai ga gaci. Koda yake kin san cewa hadiman nan nawa basu san ki ba ya kamata na gabatar dake a gare su ko kuma ki gabatar da kanki don ance waƙa a bakin mai ita tafi daɗi." Saubatul Azwas ta yì murnushi,sannan ta dubi hadiman Tazibul Luhucul waɗanda gaba ɗayansu sun kasance aljanu ne,kuma su talatin da bakwai ne. Guda talatin mata ne zallah, guda bakwai ne maza. Saubatul Azwas ta fuskance su tace, "Ni fitacciya ce a cikin al'ummar aljanu amma ba a sanni ba a fuska,domin ban yarda na bayyana kaina ba,tun ina ƙarama kawo iyanzu saboda wani buri dake cikin zuciyata. Yaku waɗannan hadimai ku sani cewa ni ce SAUBATUL AZWAS 'ya' guda ɗaya ga sarki Kalimul Ifwan." Koda jin wnanan batu sai gaba ɗayan hadiman nan suka yi sujjada ga Saubatul Azwas cikin girmamawa,ba su yadda sun sake haɗa idanu da ita ba,kuma take jikinsu ya kama ƙyarma,kamar a ce ƙyat su tashi su ruga. Ba wani abu ba ne ya sa waɗannan hadimai firgita face sanin cewa sarki Kalimul Ifwan shi ne sarkin da ya zamo abin tsoro ga dukkanin aljanun duniya a zamaninsa,domin ya kasance ƙasurgumin matsafi. Saboda tsananin ƙarfin tsafinsa idan zai yi yaƙi da wata ƙasar yana daga zaune yake yaƙin,kuma yana iya maishe da garı guda turɓaya har da komai na cikin sa,wato yana iya maishe da aljanu,dabbobi da komai na su ya zama turɓaya. Kuma wannan turɓaya zata cigaba da wanzuwa abadan-abidina. Har wannan sarki ya gama zamaninsa ba a taɓa samun wanda ya sami galaba akan sa ba. An sani cewa yana da 'ya' guda ɗaya kacal a duniya kuma kafin ya mutu ya bata gaba ɗayan sirrikan tsafinsa. Bayan ya mutu sai aka nemi wannan 'ya' tasa sama da ƙasa aka rasa. Yayin da Saubatul Azwas ta fuskanci cewar waɗannan hadimai sun tsora ta da ganinta sai ta daka musu tsawa tace, "Na umarce ku da ku iya bakinku,kada ku kuskura ku sanar da wasu cewar ina nan a cikin duniyar nan. Ku sani cewa a duk inda kuke ina tare da ku,kuma ina ganinku ina jin ku,koda kuwa kuna ƙarshen bangon duniya ne,ko cikin kuratandu. Ina son ku nutsu ku tattara hankalinku waje guda ku saurari jawabin da zan muku bisa gagarumin aikin da ke gabanmu. Idan har muka yi nasara gaba ɗayanku ku talatin da bakwan nan zaku zama manyan sarakai a cikin ƙasashen aljanu,kuma za mu ba ku dukiya irin wacce baku taɓa ganin mai yawan taba. Ina so ku sani cewa ni da ƙawata Tazibul Luhucul bamu da wani buri wanda yafi na mallakar duniya gaba ɗaya. Ni ina son na mallaki ƙasashen aljanu,ita kuma tana son ta mallake ƙasashen bil'adama. Lallai mu biyu kacal ba zamu iya wannan aiki ba,sai da taimakonku. Zan kasa ku gida biyu,kaso guda zai bini,ɗaya kason kuma zai bi ƙawata Tazibul Luhucul. Mataki na farko shi ne nan da kwana bakwai zamu tafi izuwa ƙasashen sarakan duniya mu zuba musu wanna cuta ta mutuwar ɓarin jiki. Wannan ciwo zai zame musu ajali,amma sai sun yi shekara uku suna jinya. Da zarar sun mutu zamu sace gawarwakin su mu zuba a cikin wani sunduƙi gaba ɗaya. Ina nufin gawar sarakunan aljanu da gawar sarakunan bil'adama za mu gwamutsa duka a cikin wannan sunduƙi ba zamu buɗe sunduƙin ba sai bayan shekara uku,idan muka buɗe zamu tarar ƙasusuwansu,naman jikinsu kuma ya gama ruɓewa ya zama tsutsa. Haka kuma zamu đebi ƙasusuwan da tsutsotsin mu zuba a cikin wata hodar tsafi mu dama,sannan mu zuba a cikin wata ƙatuwar tukunyar tsafi mu yi ta dafawa har tsawon shekara uku. Lallai dole ne ku yi ta gadin wannan tukunya tsawon shekara uku,don kada ɗigo ɗaya na abin dake ciki ya salwanta. Idan shekara ukun ta cika zamu buɗe tukunyar mu iske abinda ke ciki ya zama salalan tsafi. Zamu ɗauki wannan salala mu tafi da shi izuwa taskar tsafina. A can ne zamu haska madubin tsafina a jikinsa ya nuna mana inda sirrin tsafi guda ɗaya yake, wanda shi ne kaɗai sirrin da ban mallaka ba a duniya. Da zarar na je na ɗauko wannan sirri burinmu gaba ɗaya ya cika." Koda Saubatul Azwas ta zo nan a zancenta sai gaba ɗayan hadiman nan suka cika da mamaki. Ɗaya daga cikinsu wata mace mai ƙarancin shekaru ta dubi Saubatul Azwas tace, "Ya shugabata shin za ki iya sanar damu a inda taskar tsafinki take?" Koda jin wannan tambaya sai Saubatul Azwas ta murtuke fuska,sannan ta dakawa mai tambayar harara tace, "Wannan kuma wace irin banzar tambaya ce? Mene ne amfanin sanin wajen da za ki shige shi da ƙafarki idan har buƙatar mu ta biya." Mai tambayar ta duƙar da kai ƙasa tace, "Tuba na ke ranki ya daɗe ki gafarce ni." Wata tsohuwa ta ɗaga hannu tace, "Ranki ya daɗe a cikin bayaninki na fuskanci cewar sai mun yi shekara tara muna yin wannan aiki,kuma na ji kin ce dole ne mu yi gadin wannan tukunya don kada ɗigo ɗaya na abin da a ke ciki ya salwanta, idan ɗigo ɗaya ya salwanta me zai faru?" Saubatul Azwas ta yi ajiyar numfashi tace, "Ke dakata ki ji bama ɗigo ɗaya ba,idan muka bari ƙuda ya tsotsi ƙwayar zarra daga cikin wannan abu da muke dafawa a tukunyar,gaba ɗayanmu shirinmu ya wargatse sai dai mu dawo da baya mu fara sabon shiri,wato mu samo gawarwakin sababbin sarakunan duniya,mu sake ɓata wasu shekaru taran,muna haɗa wannan sinadari." Saubatul Azwas ta a cigaba da cewa, "Yanzu dai abin da nake so ku fahimta shine,dole ne ku kiyaye wasu abubuwa yayin da zamu je waɗannan manyan ƙasashen duniya guda biyar don yaɗa cutar mutuwar rabin jiki ga sarakunansu da 'yan majalisarsu. Ƙasashen nan dai da za mu je sune,Hindu,Rum,Ƙisra,Misra da Farisa. Ni ce zan je birnin Hindu,Rum da Ƙisra. Ita kuwa Tazibul Luhucul za ta je Rum,Ƙisra,Misra da Farisa. Kamar yadda na fada muku ɗazu,ku kuwa zamu rabaku kaso biyu. Kaso guda su bini,đaya kason su bi ƙawata Tazibul Luhucul. Ni da ita mune zamu je gidajen sakaruna,ku kuma kuje gidajen 'yan majalisarsu. Gaba ɗayan ku zaku tafi da wani bututun tsafi ne,wanda shi za ku hura iskar cikinsa ta zuba kan 'yan majalisar da zarar kun yi hakan take cutar mutuwar rabin jiki za ta kama su. Ni da Tazibul Luhucul kuwa zamu je ne da sandar tsafinmu kawai da zarar mun nuna su da ita za su kamu da cutar. Ku yi sani cewa babu inda zamu je sai da tsakar dare. Duk inda muka je muka tarar da cewar Sarakunan suna yin wani abu daya danganci tsafi ko bauta kada mu kuskura mu yi musu komai. Wanda kuwa ya bijirewa wannan doka take zai zama gunki. Ku sani cewa bai zamo lallai sai suna yin barci ba,amma babu lokacin da yafi kyau face lokacin da suke tarawa da iyalansu. Ina daɗa tunasar da ku cewa wanda duk ya manta ya kusance su a lokacin da suke aikin tsafi ko bauta zai zama gunki,idan kuwa ya zama gunkin ni kaina ba zan iya dawo da shi ainihin halittar sa ba. Da wannan batu nake muku sallama zan tafi ba zan dawo na ba sai bayan kwana bakwai,don mu ɗunguma mu tafi aikatar da wannan babban aiki." Koda Saubatul Azwas ta zo nan zancenta,sai ta juya ta fuskanci Tazibul Luhucul suka rungume juna đa sumbatar goshinsu suka yi sallama. Nan take Saubatul Azwas ta rikiɗe ta zama haske mai launin đorawa. Hasken ya disashe ya ɓace ɓat. Ba tare da ɓata lokaci ba Tazibul Luhucul ta ware aljanu goma sha đaya daga cikin waɗannan hadimai nata ta rarraba musu wasiƙa tace maza su je su kai gidan sarki Alyasil Buhus da 'yan majalisarsa a cikin wannan dare. Nan take hadiman suka tafi aiwatar da wannan umarni. Wannan shi ne abin da ya faru a fadar bokanya Tazibul Luhucul bayan ƙawarta aljana Saubatul Azwas ta kawo ziyarar bazata. A can gidan sarki Alyasil Buhus kuwa da kuma gidajen 'yan majalisarsa har yanzu hankali bai kwanta ba,domin yadda iyalansu suka ga rana haka suka ga dare,wato har dare ya raba basu rintsa ba. Ba zato,ba zammani sai su rinƙa ganin wasiƙu na dira,kuma ba'a ga wanda ya kawo ba. Lokacin da wasiƙar gidan sarki Alyasil Buhus ta faɗo a tsakiyar turakarsa iyalansa gaba ɗaya na zaune sun yi tagumi. Wasu suna kuka,wasu kuma suna juyayin wannan hali da sarki ya shiga rana tsaka. Cikin sauri da zafin nama yarima Sammaru ya yunƙura ya ɗauki wannan wasiƙa ya warware ta ya fara karantawa kamar haka:- "Daga uwar matsatan duniya Tazibul Luhucul zuwa ga sarkin birnin Sin Alyasil Buhus. Bayan gaisuwa a gareka gami da jajen wannan masifa da ta same ka ina mai farin cikin sanar da kai cewa idan har kana son ka warke daga wannan cuta dole ne aje taskar tsafina a deɓo ruwan tsumin tsafin da nake sha a baka ka sha. Da zarar ka sha wannan tsumi take za ka warke. Ka yi sani cewa taskar tsafina na cikin wannan kogon da ake kira MADDARUL IKISINA,shí kuwa Maddarul Ikisina na nan tsakanin duniya ta bakwai da ta takwas daga cikin duniyoyin ƙarƙashin ƙasa. Sa'a na ga mai rabo. Lallai
Chapter 11 · 0% Book details