← Book details Nihad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 20

Sashe 6

Nihad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuwa Bardil sai ya shiga nasa tunani. Jarumi Nazmir ya katse musu tunani da cewa, "Ba mu da isasshen lokaci na tunani mai zurfi. Ya kai tsoho Hamlabi me zaka iya cewa damu yanzu?" Hamlabi ya yi ajiyar zuciya yace, "Shawarar da zan ba ku guda daya ce kacal. Lallai kada ku je gidan sarki sai kun tabbata kun fara zuwa ɗakin bauta inda boka Sharmadu yake kun riske shi kun kashe shi. Muddin yana raye ba za ku iya kuɓutar da iyayenku da danginku ba daga gidan sarki. Ku yi sani cewa kashe boka Sharmadu daidai yake da neman jaki mai ƙaho. Babu wani abu da zan iya sake fada muku face na yi muku fatan samun nasara,kuma ina roƙo a gareku daku hanzarta barin gidana don kada ku shafa mini kashin kaji." Yayin da tsoho Hamlabi ya zo nan a zancensa,sai su jarumi Nazmir suka yi tsuru-tsuru suka hau duban juna. Bardil ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Haƙiƙa anan nahiyar bamu san irin ƙarfin bokaye ba,amma ga yadda nake samun labarinsu sun kasance ababan tsoro. Kai an ce ma idan boka ya bunkasa yana zama ubangijin mutanensa,saboda tsananin tsoro da girmamawa a gare shi. Ashe kuwa faɗa irin waɗannan mutane ba ƙaramin bala'i ba ne." Koda jin haka sai jarumi Nazmir yace, "Ai kuwa komai bala'insa ba zamu kasa tunkararsa ba. Ai dama yanzu haka rayuwarmu na cikin ɗaya-biyu. Kodai mu mutu ko kuma mu rayu. Tsakaninmu da sarki sai gaba,sai yaƙi. Ko dai yaga bayanmu ko mu ga bayansa. Ku tashi mu tafi ɗakin bauta don mu riski wannan shegen,tsinannen boka mu fara ƙaddamar dashi, sannan mu tunkari gidan sarki. Gimbiya Luzaiya kuma ba zamu bayar da ita ba face ɗayanmu baya numfashi a doron kasa." Jarumi Nazmir ya ɗaga takobinsa sama ya ce, "Waye zai bi bayana?" Take Bagwan da Bardil suka ɗaga nasu takubban suka kara a jikin takobin Nazmir. Cikin haɗin baki suka ce, "Muna tare da kai,komai wuya, komai dadi,mutuwa ce kaɗai zata raba mu." Sa'adda sauran baradan suka ga haka sai suma suka ɗaga nasu takubban suka yi iƙirarin abinda su Bardil suka yi. Nan take jarumi Nazmir ya wuce gaba ya kama katanga ya haura. Bardil,Bagwan,Luzaiya da sauran baradan suka yi yadda ya yi. Sannu a hankali su jarumi Nazmir suka yi ta kutsawa cikin gari,suna masu laɓe-laɓe su shiga nan,su fita can,har suka sami nasarar shiga cikin ɗakin bauta inda boka Sharmadu yake. Da shigarsu suka hau yin sanɗa da laɓe-laɓe,suna duddubawa don su yi masa kwaf ɗaya. Sai da suka duba ko'ina a cikin ɗakin bautar,amma ko ƙuda ba su gani ba. Al'amarin da ya fusata su kenan, kuma hankalinsu ya yi mummunan tashi. Ba zato,ba tsammani kuma sai suka ji an bushe da dariya. Dariyar ta cika ɗakin bautar gaba daya, babu dadin ji. Cikin fushi da kakkausar zuciya jarumi Nazmir yayi tsawa yace, "Yakai baƙin la'ananne in ka isa namiji ka fito fili mu yi gaba da gaba. Ai ba a san maza da ɓuya ba. Na rantse da darajar iyayena muddin za mu yi fito na fito sai na kai ka kushewa." Koda gama faɗin hakan sai aka sake bushewa da dariya. Lokaci guda kuma dariyar ta ɗauke,sai ga boka Sharmadu ya bayyana a tsakiyarsu jarumi Nazmir riƙe da wata isgar tsafi wadda aka yi da jelar zaki. Boka Sharmadu ya kasance matashi,ɗan kimanin shekara talatin da bakwai. Garjejen ƙato ne,mai ƙirar sadauki. Hannayensa biyu a cike suke da layu. A ƙugunsa akwai wani gurun tsafi ja,babu takalmi a ƙafarsa. A kansa babu gashi ko sili da ɗaya, kuma a aske yake ban da sheƙin salsal babu abin da kan ke yi. Idanunsa manya-manya ne,kuma ƙwala-ƙwala ababan tsoro. Bashi da gemu ko saje sai wani murtukeken gashin baki tamkar tsumma aka nannada masa. Yana da ƙaton hanci,mai faɗin ƙofofi. Bakinsa kuwa wangameme ne, cike da wargatsatstsun haƙora marasa kyan gani. Kai duk inda ake neman mummuna da an ga boka Sharmadu an gama neman,don shi ne ƙarshen muhawara. Sharmadu ya dubi jarumi Nazmir yace, "Kai samari iya bakinka kada kuruciya ta dubeka,ta ɗebe ka,ta jefa ka cikin bakin kura ka halaka a banza. Ka yi sani cewa nine boka Sharmadu shiryayyen da ya shirya tun masu neman shiri basu farka daga barci ba. Nine dodan mazajen duniya,kuma nine sa gudu maganu ƙi gudu. Nine ɗaya tamkar dubu." Nazmir ya sake daka masa tsawa yace, "Ƙarya kake ƙaramin barde yau ka hadu da gwarzo,ɗaya maganin gwarzaye dubu. Yau sai takobina ta sha jininka sannan ta je ta sha jinin mai gidanka,wannan azzalumin sarkin wanda ya daɗe yana cutar da iyayenmu da sauran talakawa." Koda jin wannan batu sai boka Sharmadu ya turɓune fuska, muninsa ya ƙaru kamar an shaƙe alade. Kafin wani daga cikin su Nazmir ya yi wani yunƙuri tuni Sharmadu ya nuna jarumi Nazmir da wannan isgar tsafi da ke hannunsa,kawai sai wata irin iska mai ƙarfi ta ɗaga Nazmir sama ta rinƙa makashi a jikin ginin ɗakin. Koda ganin haka sai Bardil,Bagwan da sauran barade suka ruga kan boka Sharmadu da nufin gididdiba shi. Kawai sai ya juyo ya dube su. Take wani haske ya fito daga cikin idanunsa ya buge su duk suka ƙame,suka zama gumaka. Sharmadu ya ci gaba da ƙyalƙyala dariya. Har a yanzu iskar nan bata daina gwara jarumi Nazmir ba a jikin ginin dakin. A wannan lokaci gimbiya Luzaiya na daga gefe guda a tsaye ita kaɗai tana ganin abinda ke faruwa. Koda ta ga halin da Nazmir ya shiga ya zamana kansa ya fashe jini na zuba kuma ya ji raunika a sassan jikinsa,harma hankalinsa ya fara gushewa sai hankalinta ya dugunzuma,bata san sa'adda idanunta suka cika da ƙwalla ba,ta fara kuka. Nan take ta tuna lokacin da jarumi Nazmir ya sallama rayuwarsa ya bita cikin ramin nan mai tsananin zurfi. Haka kuma ta tuna sa'adda ya ceci rayuwarta sa'adda kura ta kawo mata farmaki. Ta tuna da irin kulawar da yayi mata yayin zamansu a cikin jeji. Nan take gimbiya Luzaiya ta ji cewa duk duniya babu abin da take so sama da jarumi Nazmir. Cikin zafin nama ta daka tsalle ta dirga a gadon bayan boka Sharmadu ta ɗane wuyansa. Kawai sai ta kama isgar tsafin dake hannunsa ta matseta. Ba zato sai taga boka Sharmadu ya kurma ihu. Gaba ɗaya sassan jikinsa suka kama karkarwa ya hau layi kamar wanda ya sha gida ya bugu. Ba shiri ya ƙwalawa aljaninsa kira. Kawai sai Luzaiya taji an figeta daga kan wuyan Sharmadu an jifa da ita,tamkar tsakuwa aka wurgar. Luzaiya ta faɗi can gefe ɗaya sumammiya. Wani gabjejen aljani ya bayyana mai kama da goggon biri,jikinsa gaba ɗaya gashi ne mai kauri da tsini tamkar ƙayar bushiya. Kuma ya kasance baƙı wuluk,muninsa ya linka na boka Sharmadu sau ɗari. Boka Sharmadu ya miƙe tsaye da ƙyar yana tangaɗi,sannan ya dubi aljanin yace, "Yakai Dumudulmus na umarce ka da ka kwashe mu nan gaba ɗaya ka kaimu fadar sarki yanzu-yanzu." Dumudulmu yayi sujjada ga boka Sharmadu yace, "An gama sarkin bokaye." Kamar ƙiftawar ido,ya kwashe su gaba đaya ya ɓace tare da su. Bai bayyana a ko'ina ba sai a fadar sarki Fahalul Bahafus inda suka iske fada ta cika maƙil ana fadanci. Boka Sharmadu ya risina a gaban sarki ya kuwashi gaisuwa sannan yace, "Ya sarkin duniya ga masoyiyarka gimbiya Luzaiya,kuma ga manyan abokan gabarka na kawo maka kamar yadda na ɗauki alƙawari. Don haka sai ka gaggauta hallakar da su ta hanyar da na sanar maka." Koda jin haka sai farin ciki ya lulluɓe sarki Fahalul Bahafus. Nan take ya sa aka je aka fito da su sadauki Halufa,a cikinsu harda Muslaiya matar Bagwan da kuna Lamiz da sauran iyayen abokan nan su jarumi Nazmir. Koda Lamiz ta ga ƙyallenta a goshin jarumi Nazmir sai ta fashe da kuka don ta san cewa yayanta ya mutu. Shi kuwa Bagwan yaga wani kyakkyawan yaro a hannun matarsa Musalaiya. Da shi da yaron kamanninsu ɗaya tamkar an tsaga kara. Nan take farin ciki ya kama Bagwan ya yunƙura da nufin ya ruga wajen su amma damar hakan bata samu ba,don boka Sharmadu ne ya nuna shi da isgar tsafi. Take wata baƙar sarƙa murtukekiya ta ɗaure hannayensa da kafafunsa. Suma sauran iyayen abokanan su Nazmir da basu ga 'ya'yansu ba,sai suka fashe da kuka. Nan take aka tusa ƙeyar su jarumi Nazmir izuwa tsakiyar fada aka tsaida su gaban wasu manyan turakan gini inda aka saba kashe mutane waɗanda suka yi laifi ga sarki. Yayin da sadauki Halufa da jarumi Nazmir suka dubi juna sai Halufa ya murtuke fuska. Lokaci guda idanunsa suka ciko da ƙwalla ya dubi jarumi Nazmir cikin fushi yace, "Ya kai ɗana haƙiƙa kaci amana ta da kaje ka kashe mahaifin gimbiya Luzaiya don kawai ka biya buƙatar wannan azzalumin sarki namu. Kayi sani cewa har abada ba zan yafe maka ba,face ka hana auren sarki da Luzaiya,kuma ka kuɓutar da rayuwar mu nan gaba ɗaya." Yayin da jarumi Nazmir ya ji wannan batu daga bakin mahaifinsa sai ya durƙusa ƙasa da ƙyar bisa gwiwoyinsa sakamakon raunikan da ke jikinsa kuma har yanzu jini na zuba a kansa,kuma jiri na ɗibarsa. Cikin ƙarfin hali ya dubi sadauki Halufa a lokacin da idanunsa ke rufewa da buɗewa tamkar mai jin barci yace, "Yakai Abbana ka yi mini aikin gafara,ka sani cewa ban aikata wannan mummunan aiki ba bisa sani da son zuciyata. Lallai wannan sarki namu yayi mana dole ne kamar yadda ka sani idan kuwa muka saɓawa umarninsa rayuwarmu da taku na iya salwanta. To yanzu ma dai ga shi kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba,tunda dai mun sha wahala mun biya buƙatar tasa,amma kuma sakamakonnu shi ne kisa. Haƙiƙa wannan sarki ya cika azzalumi." Gama faɗin hakan ke da wuya sai ga sarki ya fito. A ɓangaren hannunsa na dama gimbiya Luzaiya ce a tafe ta sha kwalliya,kuyangi na biye da ita. A wannan lokaci duk 'ɗa' namijin da ya ƙyallara ido ya ga gimbiya Luzaiya dole ne ya ruɗe,ya ɗimauce saboda tsananin kyawunta da ya bayyana a fili ƙarara. Fuskarta na ta sheƙi da annuri,amma cikin zuciyarta baƙin ciki ne a lulluɓe, kamar zata fashe. Hawayen takaici yayi sintiri bisa kyawawan kumatunta,ta hanga, ta dubi inda jarumi yake
Chapter 6 · 0% Book details