Sashe 17
Nihad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
su luma sun kasance masu juriya da ƙarfin damtse. Duk da cewar yana saransu a sassan jiki jinı na zuba basu kai ƙasa ba kuma amma suma sun kasa kai shi ƙasan. Nan fa ya zame masu alaƙaƙai suma suka zame masa alaƙaƙai. Tofa! yau ga ƙarfi ya haɗu da naci,juriya ta haɗu da dakakkiyar zuciya kuma zafin nama ya haɗu da yawan aiki. Abin dai da yarima Sammaru ke gudu sai da ya faru domin sai da rana ta faɗi duhu ya soma ana wannan masifafen faɗa. Ana cikin haka ne wata ƙatuwar inuwa ta lulluɓe filin fafatawar gaba ɗaya suka ɗaga sama,cikin kaɗuwa 'yan fashin nan suka ɗaga kawunan su sama gaba ɗaya,ai kuwa sai suka yi arba da wata ƙatuwar halitta,wannan halitta dai ba komai bace face aljani Labagaza,zaune akansa yarima Yauhana ne da boka Karluz. Nan take aljani Labagaza ya sauka gefe guda,Yauhana da Karluz suka sauka daga kansa. Koda 'yan fashin nan su kaga cewar aljani Labagaza bai taso kansu ba sai kawai suka ci gaba da kaiwa Sammaru farmaki,cikin hanzari yarima Yauhana ya kai masa ɗauki aka ci gaba da fafatawa. Aljani Labagaza kuwa da boka Karluz sai suka zama 'yan kallo,yaƙi yayi yaƙi,gumu yai gumu kuma wahala tai wahala ya zamana gumurzun ya zama kare jini biri jini. Ko da ganin haka sai ran boka Karluz ya ɓaci,kawai sai ya dubi aljani Labagaza yace gama mini da waɗannan 'yan fashi domin suna nema su ɓata mana lokaci. Kafin Karluz ya gama rufe bakin sa Labagaza yasa yatsunsa biyar ya tsince 'yan fashin gaba ɗayansu su dubu biyar ya mutsitsikesu cikin tafin hannunsa. Kawai sai ya yarfe hannun ya zubar dasu ƙasa a rugurguje tamkar an dakesu a cikin turmi. A dai dai wannan lokacine yarima Sammaru ya dubi Yauhana da Karluz cikin ɗumbin mamaki sannan kuma ya dubi aljani Labagaza wanda babu abin da ya burgeshi da shi face tsananin girmansa da fadin tafin hannunsa,cikin yanayin mamaki Sammaru ya dubi Yauhana da kyau yayi nazarin suturar dake jikinsa ya tabbatar da cewa ɗan sarkine sai yace, "Yakai wannan ɗan sarki wane ne kai kuma ina dalilin taimakonku a gareni? Kafin Yauhana ya buɗe baki yace wani abu sai boka Karluz ya tari numfashinsa gami da shan gabansa sannan ya risina a gaban Sammaru ya kwashi gaisuwa yace, "Gaisuwa a gareka ya kai yarima Sammaru 'đa' ga sarki Alyasil Buhus na birnin Sin,kayi sani cewa wannan ɗan sarkin dake gabanka yarima Yauhana kenan 'đa' ga sarki Jamshul na birnin Rum. Ya kai Sammaru ka sani cewa bamu taimake ka don komai ba sai domin muna kan tafarki guda na buƙatar riskar boka Hulumul Makahur wanda zai samu akan turbar zuwa kogon Muddarul ikisina inda taskar tsafi take don deɓo tsumin tsafin da sarakunanmu zasu sha su warke daga muguwar cutar mutuwar rabin jiki. Ni da nake maka wannan bayani sunana boka Karluz,hadimi ga mutanen Rum." Yayin da yarima Sammaru ya jı wannan jawabi sai murna ta kamashi nan take ya miƙa musu hannu suka yi musabiha yace, "Ina murnar haɗuwa da abokan tafiya kuma abokan share hawaye tare,lallai ina mai yi muku bushara da cewar muna daf da isa wajen boka Hulumul Bakahur." Koda jin haka sai boka Karluz yayi murmushi yace, "Nasan da haka. Yakai wannan ɗan sarki zaifi kyau ka rabu da dokinka anan domin mu tafi tare akan bawanmu aljani Labagaza gashi tsaye yana jiranmu." Sammaru ya ƙarewa Labagaza kallo sama da ƙasa yace, "Haƙiƙa kaci sunanka don tun da nake ban taba ji ko ganin aljani mai girmanka ba sai yau." Labagaza ya ƙyalƙyale da dariya yace, "Haba yaro ai duniyar nan da faɗi take inda kasan aljani Shamharu shahararre da baka faɗi haka ba." Cikin mamaki Sammaru yace, "Wane ne kuma Shamharu shahararre?" Labagaza yace, "Ai wannan labarine mai tsawo sai dại ka nemi littafin tarihi mai suna KUNDIN TSATSUBA a cikin sane zaka sha labarin Shamharu shaharare. A taƙaice dai wani taƙadirin aljanine da ya gallabi duniya a zamaninsa ya zama alaƙaƙai ga komai da kowa." Yayin da aljani Labagaza yazo nan a zancensa sai boka Karluz ya daka masa tsawa yace, "Kai malam ba hira muka zo yi ba,maza ka đaukemu ka kaimu fadar boka Hulumur Makahur." Cikin abin da bai wuce daƙiƙa ɗaya ba aljani Labagaza ya suri Sammaru,Yauhana da Karluz ya azasu a gadon bayansa har ma yayi tafiyar zango biyu,sai gasu sun iso kofar kogon tsafin boka Hulumul Makahur. A hankali kuma a tsanake aljani Labagaza ya sauke su ƙasa. Koda suka dubi kogon sai suka ga ashe siffar mutumce dashi,wato mutum ne a zaune ya tanƙwashe ƙafafunsa kuma ya buɗe tafin hannayensa. Akan tafin hannunsa na dama wata farar kwatanniyace. Akan tafin hannun hagu kuwa jar kwatanniyace. Boka Karluz,Sammaru da Yauhana suka ɗaga kai sama suna kallon wannan gunki cikin al'ajabi da rashin gane ma'anarsa. Yauhana ya dubi Karluz yace, "Shin kuwa kasan ma'anar wannan kwatanniya guda biyu?" Karluz yai ajiyar zuciya yace, "Haba yarıma ya za'ai na sani ai munzo inda sanina bai kai ba. Kasan ance Baba da Babansa,haka kuma malam da malaminsa,ni kam almajirine anan,neman sani nazo biɗa." Karluz na gama faɗin hakan suka ji an bushe da dariya. Dariyar ta cigaba tsawon ɗan lokaci daga bisani ta ɗauke ɗif,kawai sai hannun daman mutum mutumin mai siffar kogon ya sauko ƙasa gabansu. Bakin mutum mutumin kuma ya buɗe yace, "Lale marhaban daku 'ya'yan sarakai ku sanya hannayenku a cikin wannan kwatanniya." Koda jin haka sai boka Karluz ya fara kai hannunsa zai sa acikin kwatanniyar,cikin tsawa mutum mutumin yace, "A kul kasa hannunka idan baso kake ya ruɓurɓushe ba. Domin wannan kwatanniyace ta 'ya'yan sarakai kawai." Cikin tsoro boka Karluz ya janye hannunsa jikinsa na karkarwa yaja da baya Yauhana da Sammaru suka sa hannayensu acikin kwantanniyar kawai sai suka zama farin haske suka ɓace. Mutum mutumin ya sake sauko da ɗaya hannun nasa na hagu mai jar kwatanniya yace, "Saka hannunka aciki ya kai Karluz domin wannan kwatanniya ta bokaye ce kaɗai. Lallai babu mai shiga wannan kogo face sarakai da bokaye." Cikin azama Karluz ya sanya hannunsa a cikin kwatanniyar take ya zama jan haske ya ɓace. A cikin wata ƙasaitacciyar fada mai ginin dutsen jauhar ruwan ɗorawa suka tsinci kansu. Komai dake cikin fadar akan iska yake yawo babu wani abu dake ajiye a ƙasa. Kai irin iskar dake kaɗawa a cikin kogon ma ba irin wacce mutum ya saba shaƙa da ji bace. Abubuwan al'ajabi kuwa gasu nan birjik kaka-kala irin wanda idanu basu taɓa gani ba ne. Nan fa Karluz,Yauhana da Sammaru suka zama cikakkun 'yan ƙauye kuma suka cika da al'ajabi domin su kansu yawo suke yi akan iska kuma tafiya ake yi dasu a cikin kogon ana ƙara nutsawa da su ba akai madakata ba. Har yanzu kuma basu ga mutum ko aljan ba. Babu komai face dabbobi iri iri daga irin halittun ruwa da kuma na jeji masu siffofin al'ajabi. Wani lokacin sai kaga mitsitsin kifi da ƙaton kai mai girman tsauni ko kuma kaga kazar ruwa mai kawuna dubu da silin ƙafa đaya. Haka dai suka yi ta ganin abubuwan mamaki har suka gaji da ganinsu. Ba zato ba tsammani sai gasu acikin wata fadar dabam wacce tafi ta baya kyau da tsaruwa sau dubu. A cikinta aljanu barkatai suna ta aiyuka iri iri na hidimar tsafi. Komai a wannan fadar ma akan iska yake yawo har su kan su aljanun masu hidima. Haka kuma abubuwan al'ajabin dake wajen sun ninka waɗanda ke fadar farko. A cikin wannan fadar ne boka Karluz ya cire rawaninsa ya sake shi don ya ga abin da zai faru Shin rawanin zai faɗo ƙasa ne,ko kuwa zai tsaya a cikin iska? Ai kuwa yana sakin rawanin sai ya tsaya a cikin iska,kuma yayi sama ya naɗa kansa akan boka Karluz. Take boka Hulumul Makahur ya bayyana a gabansu bisa wata karagar mulki. A kansa akwai hular sarki ta zinariya. Hannunsa na hagu na riƙe da farar sandar tsafi. Karagar zinariyar tana tafiya ne akan iska. Yana sanye da wata doguwar jar riga. A wuyansa akwai murjanai kimanin guda arba'in da bakwai,kuma kowanne đaya an yi shine daga abu dama,daga dangin zinare,sai lu'u'lu'u,jauhar, zubarjadi,demon,yaƙutu da dai sauransu. Wani abin ma ko sunansa mutum bai taɓa ji ba. Boka Hulumul Makahur ya dubi boka Karluz yace, "Iskar dake cikin fadar nan tamu ba irin iskar duniyar ku bace. Wannan iska mun samo tane daga duniyar wata." Hulumul Makahur ya waiga ya dubi yarima Sammaru da yarima Yauhana yace, "Ina yi muku barka da zuwa fadar sarkin bokaye. Haƙiƙa kun zo inda za'a share muku hawaye bisa babbar buƙatar dake gabanku,amma ku sani cewa za ku yi shirin nada gammo don đaukar abin da yafi duniyar nan da abin dake cikinta nauyi." Yayin da su Yauhana suka ji wannan batu sai hankalinsu ya tashi,gaba ɗayansu suka ƙurawa boka Hulumul Bakahur idanu,shima sai ya zuba musu ƙwala-ƙwalan idanunsa masu kama dana mujiya. Bisa mamaki sai suka ga ya tuntsire da dariya. Lokaci guda ya haɗe fuska,kuma sai ga hawaye daga cikin idònsa guda. Al'amarin da ya ƙara jefa su cikin fargaba da ruɗewa kenan. Yarima Sammaru ya dube shi cikin nutsuwa yace, "Ya kai wannan boka ina dalilin yin dariyarka,kuma ina dalilin yin kukanka?" Boka Hulumul Makabur yai ajiyar zuciya yace, "Ya kai wannan ɗan sarki kayi sani cewa yau shekarata casa'in da tara a cikin wannan kogo. A cikin nan uwata da ubana suka yi rayuwa,ina da 'yan uwa guda bakwai dukkaninsu mata ne,nine kaɗai namiji. Mahaifina gawurtaccen matsafi ne,ba wani abu bane ya zama sanadin aljalin mahaifina da mahaifiyata da kuma 'yan uwana face bincike akan yadda za su mallaki sirrikan tsafi guda miliyan dubu tara da casa'in da tara,irin wanda bokanya Tazibul Luhucul ta mallaka,kuma ta ɓoye su a cikin taskar tsafinta,wadda ke kogon Maddarul ikisina. Sun sha ƙoƙarin zuwa kogon Muddaril ikisina,amma da sunje gaban ƙofar kogon sai shiga ta gagarasu. Dawowa da baya ta gagara,anan suke rasa rayuwarsu. Ɗaya bayan ɗaya da haka 'yan uwan nawa bakwai suka rasa rayukansu. Ni kaɗai ne yanzu nayi saura. Daga tsawon lokacin mutuwar 'yar uwata ta ƙarshe,kawo iyanzu shekara arba'in kenan. Tsawon wannan lokaci bana komai face bincike da gano yadda zan iya shiga cikin kogon Muddaril