Sashe 14
Nihad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mafarkin kowa face na sa,don gudun kada mutane su kauce hanyar Allah su shiga saɓo. A wani dare sarki Usman na kwance yana barci sai yayi mafarki da wäsu irin baƙaƙen tsuntsaye guda talatin da bakwai suna shawagi a sararin samaniya,amma kuma wasu halittu biyu ne ke yi musu jagora. Halittun kuwa ɗaya mutum ce đaya kuma aljana ce. Tsutsayen da halittun suka rinƙa zuwa kan wasu manyan turakan gini guda shida suna watsa wata guba. Nan take turakan ginin suka rinƙa rugujewa suna faɗuwa ƙasa. Al'amarin da ya janyo rugujewar gaba ɗayan gidajen shida waɗanda ke ƙarƙashin manyan turakan nan har ma wuta ta kama gidajen zasu ƙone ƙurmus. Kawai sai sarki Usman ya tsinci kansa a gidajen guda shida. Koda yaga wuta na ƙoƙarin ƙone su gaba ɗaya sai ya fara ƙoƙarin kashe wutar dake cikin gida na ƙarshe,kuma yana kiran taimako cikin ihu da ƙaraji. Haka dai ya yi ta ƙoƙari bai samu mataimaki ba,har ya zamana wutar ta kama gefen rigarsa kafin ya ankara gaba ɗayan rabin rigar ɓangaren hagu ya cinye gaba ɗaya,amma wani abin mamaki shine ko kaɗan fatar jikinsa ba ta ƙone ba. Yana cikin wannan hali ne wata ƙanƙanuwar tsuntsuwa fara sol ta bayyana gare shi tace, "Ya kại adalin sarki na san cewa daga cikin abubuwan daka mallaka a duniya babu abin da ka fiso sama da wata kurciya guda ɗaya wadda ka keɓeta,ka hana kowa kusantarta,inda zaka saki wannan kurciya da ta zo nan ta kashe wannan wutar gaba ɗaya wadda ke shirin ƙone gidajen nan guda talatin da bakwai,sannan ta yaƙi masu yi musu jagora wajen aiwatar da wannan mummunan ɓarna ya zamana labarin suma ya gushe har abada." Farar tsuntsuwar na gama faɗin haka sai sarki Usman ya farka daga wannan mummunan mafarki mara kan gado,da wuyar fahimta. Gaba đaya jikinsa ƙyarma yake haka kuma fuskar sa cike take da zufa. Haƙiƙa sarki Usman ya razana da wannan mafarki. Nan dai ya karanta waɗansu addu'o'i ya koma ya kwanta da niyyar cewa da safe zai kira 'yarsa Fauwaza ya sanar da ita wannan mafarki don ta fassara masa shi. Kashe gari kuwa sarki ya aika a gayawa Fauzawa cewar yana gaiyatarta kalaci turakarsa. Al'amarin da ya matuƙar baiwa Fauwaza mamaki kenan,domin rabonta da barin ɓangaren da take an kai shekara huɗu. Kullum a tsare take kamar 'yar fursuna sai dai sarki da mahaifiyarta su kawo mata ziyara da kan su. Babu mai shiga inda take face barori da kuyangi masu yi mata hidima. Fauwaza ta fara saƙe-saƙe a ranta cewar anya kuwa ba batun aure sarki zai yi mata ba. Ai kuwa idan har bayar da ita za'a yi ga wani wanda bata taɓa gani ba zata kasance cikin tsananin baƙin ciki. Haka dai ta yi ta saƙe-saƙe a ranta,ta ƙulla wannan,ta kwance wannan,har aka turo 'yan rakiya suka shige gaba don kaita turakar sarki. Sarki Usman na zaune shi kaɗai a ƙasa, bisa wata ƙatuwar dadduma an ajiye kalaci a gabansa,irin wanda kowanne talaka zai iya ci a gidansa,sai ga gimbiya Fauwaza ta shigo cikin ɗakin da sallama. Cikin fara'a da murmushi ya ɗago kai ya dube ta yana mai amsa sallamar. Cikin ɗari-ɗari Fauwaza ta zauna tana mai fuskantarsa. Sarki Usman ya dubeta cikin nutsuwa yace, "Haba 'yata,ki saki jikinki mana ki tuna fa cewa nine mahaifinki,kuma babu abin da nake so a duniyar nan sama dake. Na unmarce ki da cin wannan abin tare da ni." Koda jin haka sai farin ciki ya lulluɓe Fauwaza domin tana jin daɗin kasancewa tare da mahaifinta,a kowanne lokaci. Nan take ta yaye ƙyallan da ya rufe mata fuska,kuma ta saki jiki suka fara cin abincin cikin kwanciyar hankali. Sai da suka sha ruwa,a sannan ne sarki Usman yayi gyaran murya yace, "Yake 'yata ki yi sani cewa ban kiraki ba nan domin komai sai don na labarta miki wani mafarki wanda nayi,ya firgitani kuma ya jefani cikin rashin fahimta da ruɗani. Ina son ki fassara mini wannan mafarki don na gane ma'anarsa." Ba tare da ɓata wani lokaci ba,ya zayyana mata wannan mugun mafarki da yayi. Bayan ya gama sai yaga gimbiya Fauwaza ta shiga yanayin damuwa cikin alamun karayar zuciya tace da shi, "Yakai Abbana ina son ka sani cewar fassarar wannan mafarki naka a bayyana take. Waɗannan baƙaƙen tsuntsaye guda talatin da bakwai daka gani ba komai bane face hadiman wata ibilishiyar bokanya,waɗanda duk sun kasance baƙaƙen aljanu,kuma kafirai marasa tausayi da imani. Waɗannan halittu biyu dake wa baƙaƙen aljanun jagora kuwa bokanyar ce da uwargidanta,wata aljana muguwar gaske. Wannan mafarki naka yana bushara ne da cewar waɗannan kafirai zasu jehowa manyan sarakunan duniya wata irin muguwar cuta. Sarakunan guda shida ne,kuma sune waɗannan turakan gini daka gani a cikin mafarkinka. Wannan guba wacce tsuntsayen ke zubowa akan turakan gini ita ce nuguwar cutar. Rugujewar turakan ginin da faɗuwarsu ƙasa na nufin cewa waɗannan sarakuna guda shida zasu kamu da ciwon ajali har ya kaisu ga kushewa,idan baka manta ba akwai gidaje guda shida ƙarƙashin turakan,waɗannan gidaje sune manyan ƙasashen duniya dake ƙarƙashin manyan sarakuna. Waɗannan ƙasashe sun haɗa birnin Sin,Hindu,Rum,Ƙisra,Misra da Farisa. A cikin mafarkin an nuna maka cewa gidajen shida sun ƙone ƙurmus,sakamakon rugujewár turakan ginin guda shida. Wannan yana nufin cewa da zarar cutar ajalin ta gama kashe sarakunan waɗannan ƙasashe shida za'a cisu da yaƙi gaba ɗaya. Kà tuna cewa wutar data kama gidajen ta kama rigarka har ta ƙone rabinta ɓangaren hagu,amma ko kađan bata ƙona fatar jikinka ba,wannà n yana nufin cewa babu makawa kaima sai kamu da cutar mutuwar ɓarin jiki,amna ba zai taɓá imaninka da addininka ba. Wannan farar tsuntsuwa kuwa data zo maka da bushara ba komai ba ce face Addinin Musulunci. A cikin wannan mafarkin naka farar tsuntsuwar data gaya maka cewa inda za ka saki wata kurciya guda ɗaya wadda ka keɓeta ka hana kowa kusantarta da fa kashe wutar dake ƙoƙarin ƙone gidajen shida kuma ta káshe baƙaƙen aljanun nan guda talatin da bakwai da iyayen gidansu. Wannan kurciya ba komai bace face ni ɗin nan gimbiya Fauwaza." Koda gimbiya Fauwaza tazo nan a zancenta sai sarki Usman ya cika da tsananin mamaki. Hankalin sa ya dugunzuma fiye da kowanne lokaci. Kawai sai yayi ajiyar zuciya ya dubi gimbiya Fauwaza cikin alamun karayar zuciya da sallamawa yace, "Yake 'yata haƙiƙa fassarar wannan mafarki ta tayar mini da hankali. Na sani cewa ba ki taɓa yin ƙarya ba,kuma duk abin da kika faɗi yana faruwa a zahiri. Lallai ni da sauran waɗannan sarakuna muna cikin mummunan tashin hankali. Tabbas ya zama wajibi in baki dama ki fita yin jihadi a doron ƙasa,domin kawar da maƙiya addinin Allah,kuma ki kawar da zalunci ki shimfiɗa adalci. To amma abin tambayar anan shine ke ba jaruma bace,kuma baki taba yin yaƙi ba,ta yaya zaki iya fuskantar waɗannan manyan azzalumai masu tsananin karfin damtse da ƙarfin tsafi?" Yayin da gimbiya Fauwza ta ji wannan batu na mabaifinta sai tayi murmushi tace, "Yakai Abbana ina son na tuna maka cewa wanda duk yayi dogaro da Allah,haƙiƙa Allah zai iya masa bisa dukkanin abin da yasa a gabansa. Abin da nake so da kai shi ne kasa a shirya mini runduna ta mayaƙa kimanin mutum dubu saba'in,ni kuwa nayi musu jagora izuwa cikin waɗannan manyan ƙasashen duniya,duk inda muka je za mu yi musu wa'azi bisa addinin Allah cikin masalaha da nasiha,idan sun karɓa hannu shikenan Alhamdulillah,idan kuwa suka bijire sai na yaƙe su da ƙarfin tsiya na kafa tutar Musulunci a ƙasar. Tabbas in dai ka lamince mini hakan Musulunci zai rinjayi kafirci kuma cutar da zata kamaku sai na zamo sanadiyar warkewarku." Lokacin da gimbiya Fauwaza tazo nan a zancenta sai hawaye ya zubowa sarki Usman. Koda ganin haka sai hankalinta ya tashi ta matsa gare shi ta riƙe hannayensa biyu tana mai cewa, "Yakai Abbana ina dalilin zubar wannan hawaye a idanunka? Ka yi mini gafara idan har maganganuna sun ɓata maka rai,don kada na shiga cikin fushin Allah." Cikin alamun tausayawa dana nuna tsantsar kauna,sarki Usman ya kama kafaɗun gimbiya Fauwaza yace, "Yake 'yata na rantse da sarki makaɗaici wanda bashi da abokin taraiya baki taɓa faɗin wata kalma ba guda ɗaya wadda ta ɓata mini rai,tun haihuwarki kawo iyanzu,ki yi sani cewa ba komai ba ne ya haddasa zubar hawaye a idanuna ba face sanin cewa lokaci ya zo wanda zamu rabu tsawon lokaci alhalin kin sani cewa a duk duniya babu abin da nake so sama da ke. Daidai da rana guda ban son rabuwa dake,saboda tsananin so da nake yi miki ne na hana kowa kusantarkı,na hanaki yin aure,kuma na ɓoye kyawun nan da Allah ya yi miki. Yau gashi za ki tafi ki barni,kyawunki zai bayyana a duniya kowa ya gani." Sa'adda sarki Usman ya zo nan a zancensa sai jikin gimbiya yayi sanyi. Tausayi da ƙaunar sarki Usman suka baibaye zuciyarta. Kawai sai ta rungumeshi,ta fashe da kuka tana mai cewa, "Da yardar Allah duk inda na je zan dawo gida lafiya. Albarkacin wanda aka yi duniya da lahira dominsa,ajali ba zai zamo sanadin rashin sake saduwar mu ba. Zan cigaba da roƙon Allah da yasa mu yi tsawon kwana har ka ga ranar aurena kuma kaga jikanka da idanu ka." Sarki Usman ya janye jikinsa daga na gimbiya Fauwaza suka fuskanci juna sosai,yana mai share hawayen idanunsa yace, "Yake 'ya ta,ki dube ni da kyau ki gani fa haƙiƙa tsufa ya riske ni domin a ƙallah shekaruna sun haura casa'in,anya kuwa zan iya kai wannan lokacin?" Cikin sauri ta tari numfashinsa tace, "Kada ka ƙara faɗin haka ya Abbana domin kuwa rai da mutuwa duk a hannun Allah suke,kuma babu wanda ya san gawar gobe." Cikin yanayin nadama sarki Usman yace, "Allah na tuba ka yafeni,kuma na roƙe ka daka sakawa wannan 'ya tawa da lada mai yawa,domin ta kasance mai sani akan tafarkin shiriya. Allah na roƙeka da kayi mata jagora bisa wannan gagarumin aiki da zata yi dominka. Ka kareta daga dukkan tsautsayi,asara,mugun ji da mugun gani,ka bata nasara bisa maƙiyanka. Ka ɗaukaka ta,ɗaukaka irin wacce ka yiwa bayinka na gari magabatanmu." Haka dai sarki Usman yayi ta yiwa gimbiya Fauwaza addu'o'in alheri. Bai gushe ba yana yi har sai da itama ta karɓa,tana mai yi masa fatan alheri.