← Book details Nihad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 20

Sashe 13

Nihad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

duk faɗin ƙasarnan ta Rum babu wani abu da nake so sama da kai,kai ne ɗana a duniya don haka bazan yarda ka tafi neman wannan abu mai haɗarin ba a sanadıyar hakan rayuwarka ta salwanta. Ina son ka rungumi ƙaddara daga yau har izuwa ranar da zamu kamu da wannan cuta izuwa lokacin da rai zai yi halinsa domin ka gajeni ka zama sarkin Rum." Yarima Yauhana ya dubi mahaifinsa cikin dakakkiyar zuciya yace, "Ni kam na gama zartar da wannan hukunci kuma babu abin da zai hanani zartar da shi face mnutuwa,ba zan cika ɗa a gareka ba har sai na sami nasara bisa wannan buƙata. Ya kai boka Karluz ina son ka sani akan turba yadda zan iya zuwa wannan wuri inda kogon Maddarul ikisina yake." Sa'adda yarima Yauhana yazo nan a zancesa sai boka Karluz yace, "Ni kam nayi iyakar bincikena ban gano yadda za'a iya zuwa wannan wuri ba,amma a cikin binciken nawa na gano wani boka guda ɗaya wanda shi kaɗai ne zai iya faɗar hanyar da za'a bi aje wannan wuri. Shi dai wannan boka sunansa Hulumul Makahur,yanzu haka yana nan zaune cikin wani jeji da ake kira Dulmas a yankin kasar Sin kuma yarima Sammaru ɗan sarki Alyasil Buhus mai mulkin ƙasar Sin ya tafi izuwa gareshi don ya sa shi akan turbar zuwa kogon Maddarul ikisina." Koda yarima Yauhana yaji wannan batu na boka Karluz cikin zaƙuwa yace "Na umarce ka da kasa ɗaya daga cikin aljanunka ya ɗaukeni da gaggawa ya kaini wajen wannan boka a cikin ƙanƙanin lokaci." Karluz yayi murmushi yace, "Zanyi duk yadda kace amma nima ina rokon alfarma guda ɗaya a wajenka. Ina son kayi wannan tafiya tare da ni domin idan na sadu da boka Hulumul Makahur zan sami ƙaruwa mai yawa a cikin ilimin tsafi bare kuma ace an sami nasarar shiga kogon Maddarul ikisina tare dani." Yarima Yauhana yayi murmushi yace, "Na amsa wannan buƙata taka." Ba tare da ɓata wani lokaci ba boka Karluz ya kimtsa nan take ya kira wani basamuden aljani waishi Labagaza ya baiyana gabansa. Bayyanar Labagaza keda wuya sarki da 'yan majalisarsa suka zube kasa sumamnmu saboda tsananin razana. Boka Karluz da yarima Yauhana kaɗai suka rage a tsaye ƙiƙam su kansu zuciyoyinsu na rawa. Aljani Labagaza ya kasance ƙatoton gaske kuma mummuna ne na kwatance. Faɗin tafin hannusa guda yakai zira'i ɗari,hancinsa kuwa wawakekene tamkar ƙofar gari,idanunsa manya- manya ne kuma ɓalo ɓalo kamar za su faɗo ƙasa. Idan ya wangame bakinsa sai kaga harshensa ya zazzago ƙasa har yana shafar ƙasa saboda tsawonsa,girman haƙorinsa guda ya ninka ɓauren giwa uku. Yana da fukafukai guda ɗari,hamsin a kuiɓin dama,hamsin a kuiɓinhagu,idan ya bushe da dariya sai kaga ƙasa ta kama girgiza tamkar za'a kifar da duniyar. Labagaza risina gaban boka Karluz yace, "Ya shubana gani gareka me kake buƙata daga gareni? Ina mai tunasar dakai cewa a halin yanzu saura aiki uku kacal tsakanina da kai,idan nayi na ukun shi kenan mun rabu har abada bazan sake yin bauta a garcka ba." Boka Karluz yayi murmushi yace, "Zancen ka dutsene,ya kai Labagaza kayi sani cewa ban kiraka nan ba sai don ka ɗaukemu ni da yarima Yauhana ka kaimu dajin dulmas inda boka Hulumul makahus yake a cikin abin da bai wuce sa'a huɗu ba wato kafin yarima Sammaru đan sarki Alyasil Bubus ya isa gareshi." Koda jin wannan batu sai aljani Labagaza ya ƙyalƙyale da dariyar mugunta al'amarin da ya janyo rugujewar turakar kenan ƙasa ta kama girgiza,gaba ɗaya birnin na Rum ya kama tambal tambal. Ba don aljani Labagaza yayi sauri ya ɗauke su boka Karluz dasu sarki Jamshul ba da tuni sun rufta cikin ƙasa ta binnesu. Koda ganin wanna ɓarna ta aljani Labagaza yayi. Boka Karluz ya daka masa tsawa yace, "Ashe bana haneka da yin dariya a nan ba?" Labagaza ya sunkui da kansa ƙasa yace, "Tuba nake ya shugabana,haƙiƙa na sha'afane saboda jin bautar da na yiwa Bil'adama a doron ƙasa zan iya kai ku gaban boka Hulumul lakahur a cikin abin da bai wice sa'a daya da rabi ba." Boka Karluz ya sake yin murmushi a karo na biyu sannan ya watsawa su sarki Jamshul ruwa suka farfaɗo daga dogon suman da sukayi,kafin ɗayansu ya buɗi baki yace wani abu tuni boka Karluz da yarima Yauhana sun kama hawa kan aljani Labagaza tamkar masu hawa gini mai matattakala dubu,cikin gudu suka isa tsakiyar gadon bayansa suka zauna. Zamansu ke da wuya aljani Labagaza ya buɗe fukafukansa gaba daya đarin ya tashi da su sama. Yarima Yauhana ya rinƙa ɗagawa sarki Jamshul hannu har suka ƙule a cikin gajimare. Kamar yadda al'amura suka kasance a birnin Rum haka suka kasance a birnin Ƙisra da Farisa tamkar haɗin baki,sarkin Ƙisra na da ɗa guda kuma Jarumin gaske sunansa Lubaika. Yanzu haka Lubaika ya nufi dajin Dalmus don riskar boka Hulumul Makahur bisa kan wani aljani wai shi Karakainu. Shi kuwa sarkin farisa yana da 'ɗa' mai suna Larbuz wanda ya kasance gwarzon shekara acikin birnin Farisa domin shi kaɗai ya fatattaki waɗansu dodanni da suka addabi ƙasar da kawo sumamen bazato suna đauki ɗai ɗai cikin dare. Ance yawan dodannin ya kai dubu ashirin da bakwai kuma suna da matuƙar girma da ƙarfi amma da yake yarima Larbuz ya kasance sadauki mai tsananin zafin nama koda ya tarbasu cikin daji inda suka yi sansani sai ya zame musu alaƙaƙai yayi ta ragargazarsu,sai da ya kashe guda ɗari tara da saba'in da bakwai daga cikinsu. Koda sukaga yayi musu wannan ɓarna kuma sun kasa cimma masa sau suka ranta a ana kare amma duk da haka bai ƙyalesu ba sai da ya bisu ya rinƙa kifar dasu,da ƙyar guda ɗari biyar suka tsira da rayuwarsu. Wannan jarumtaka da yarima Larbuz yayi ba ƙaramar ɗaukaka ta jawo masa ba a wajen mutanen ƙasar Farisa. Sai da ya zamana kowa na ƙaunarsa maza da mata yara da manya,kai duk wata budurwa da ta isa da kanta a fagen kyau bata da burin da ya fi ta auri yarima Larbuz. A ranar da aka shirya gagarumin taro a fadar birnin Farisa don zaɓar budurwar da yarima Larbuz zai aura sai bokan ƙasar ya bayyana wanda a kewa laƙabi da Sharudul Bahabul. Nan boka Sharudul Sababul ya sanar da sarkin Farisa labarin masifar da zata faɗo kansa da kuma 'yan majalisarsa. Haka kuma ya zaiyana musu yadda zasu kuɓuta ta hanyar samo wannan tsumin tsafin dake can taskar tsafin bokanya Tazibul Luhucul. Bugu da ƙari yayi bayanin cewa babu wani boka da zai iya faɗin hanyar da za'abi aje wannan wuri face boka Hulumul Makahur. Duk wannan bayani boka Sharudul Bahabul yayi shine acikin bainar jama'a. Koda ya ƙare jawabi sai gaba ɗaya wajen ya ruɗe da iface iface,masu kuka nayi masu surutai nayi. Sarkin Farisa kuwa da 'yan majalisarsa tuni sun fita haiyacinsu tamkar wađanda suka shekara suna cutar ajali. Koda ganin abin dake faruwa sai yarima Larbuz ya daka tsawa cikin kakkausar murya. Take wajen yayi tsit kai kace mutuwa ce ta gifta. Yarima Larbuz ya hau kan wani mumbari dake ajiye a tsakiyar fadar ya waiga gabas da yamma,kudu da arewa yaga ko'ina jama'ane rututu babu masakar tsinke amma kowa ka dubi fuskarsa sai kaji tamkar ka fashe masa da kuka domin alamun tsorone da fargaba ƙarara zaiyane a fuskarsa. Yarima Larbuz yayi gyaran murya yace, "Yaku mutanen bimin Farisa kuyi sani cewa ni yarima zan tafi Larbuz na rantse da martabarku zan tafi wannan wuri inda tsumin bokanya Tazibul Luhucul yake ba kuma zan dawo ba sai da shi. Lallai na yi alƙawarin kare lafiyar sarki data 'yan majalisarsa,kamar yadda na kare rayuwar jama'ar ƙasar nan daga harin muggan dodannin nan." Koda yarima Larbuz ya zo nan a zancensa sai wajen ya cika da shewa ana yi masa jinjina. Ba tare da ɓata lokaci ba boka Sharudul Bahadul ya ajiye sandar tsafinsa a ƙasa sai ta rikiɗe ta zama wani ƙaton shaho mại girman gaske,wanda idan ya kaɗa fukafukansa sai ka ga iska na neman kwantar da jama'a. Sharudul Bahabul ya dubị shahon yace, "Ya kai wannan tsuntsu na umarce ka da ka duƙa ƙasa domin yarima ya hau bayanka ka ɗauke shi ka kại shi dajin Dalmus inda boka Hulumul Makahur yake." Ai kuwa tamkar da mutum yayi magana,sai shahon nan ya durƙushe ƙafafunsa ƙasa. Cikin hanzari yarima ya haye bayansa ya zauna. Kafin tsuntusn ya tashi sama sai boka Sharudul Bahabul ya matsa gaban yarima Larbuz yayi masa raɗa a kunne yace, "Da zarar kun dira a can wannan tsuntsu zai rikiɗa ya zama sandata ta tsafi sai kaɗauka ka riƙe ta har ku je taskar tsafi ku dawo. Lallai ka dawo tare da wannan sanda tawa." Yarima Larbuz yace, "Tabbas zan kasance mai cika alƙawari zan dawo maka da sandarka." Boka Sharudul Bahabul ya bugi bayan shahon kawai sai ya buɗe fukafukansa ya yi sama. Shahon ya yi ta lulaƙawa cikin gajimare,tun jama'a na iya hangensa har ya ɓace ɓat. Su kuwa 'yan matan da suka zo wannan gagarumin taro don a zaɓi ɗaya daga cikinsu a matsayin wacce yarimna Larbuz zai aura sai suka fashe da kuka,suka kamu da tsananin baƙin cikin rabuwa da abin begensu dare da rana. Wannan shine abinda ya faru a birnin Farisa. A can birnin Misra kuwa sarki Usman ne ke mulkí. A wannan lokaci mutanen birnin Misra gaba ɗayansu ma'abota addinin Musulunci ne. Sarki Usman na da kyakkyawar 'ya' guda ɗaya wacce saboda tsananin kyawunta ba a bari ga fuskarta,koda yaushe fuskar ta ta a rufe take da baƙin kyalle mai shara-shara. Ita dai wannan 'yar' sarki sunanta Fauwaza. Fauwaza ta kasance budurwa 'yar shekara goma sha takwas mai cikakkiyar sura tamka ita ƙera kanta. Haka kuma ta taso da kaifin basira da kuma ilimin addini ma yawa. Wata baiwa wadda Allah yayi mata shi ne tana da ilimin fassarar mafarki. Duk irin mafarkin da mutum yayi in dai ya faɗa mata take zata fassara shi,kuma duk abin da ta faɗa sai an ga faruwarsa walau na farin ciki ne ko na baƙin ciki. Yayin da sarki Usman ya ga mutane na girmama Fauwaza bisa lamarinta na fassarar mafarki har na suna neman su maishe da ita abin dogaronsu sai ya hanata fassara
Chapter 13 · 0% Book details