← Book details Nihad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 20

Sashe 2

Nihad Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

(Kutttttt😳😳😳 lallai yaran nan a gaishe su,suna gaf da mutuwa amma ta kishi suke😂🤣🤣)

Mazalish ta dubesu ta bushe da dariya tace,
"Haƙiƙa kukan daɗi kuke yi kawai saboda ganin masoyinku a kusa daku yanzu ni da ban san a inda nawa yake ba kuma ban san a inda zan riske shi ba,ai sai dai naci gaba da kuka tunda gashi ma yau zan bar duniyar gaba ɗaya."
A dai-dai wannan lokacin ne suka ga an ɗebo wani garin magani kala biyar an zazzagesu duk a cikin ƙaton kaskon nan.
Daga nan kuma sai wani ƙaton maridi ya dubi sarkin maridan yana
mai tambayar wanda za'a fara kashewa daga cikin su.
Sarkin maridai yai nuni ga aljani
Gulzum.
Koda ganin hakan sai Gulzum ya fashe da kuka yana baiwa Yelisa wasiya cewar,
"Idan ta koma duniyarsu ta nemi iyayensa ta sanar dasu yadda ya kasance kuma ta nema masa gafararsu domin ba'a son ransu ya bar gida ba,ya shiga duniya."
Yelisa ta zubar da ƙwalla don tausayi da sabo tace,
"Ya kai Gulzum ai abin da ya same ka shine zai same ni sai dai muyi hakuri gaba daya."

(😂🤣🤣🤣🤣. Su Gulzum anga mutuwa🤣)

Kafin wani daga cikinsu Jafar yace wani abu tuni ƙaton maridin nan ya suro Gulzum,igiyar da ta ɗaure shi ta tsitstsinke,da hannu ɗaya
maridin ya aza Gulzum a saman ƙoƙon sannan ya ɗaga ɗaya hannunsa ya kaiwa maƙoshin Gulzum suka da tsinin farcen babban ɗan yatsansa.
Ba zato ba tsammani sai aka ga wata runÉ—umemiyar macijiya mai kawuna dubu arba'in ta zuro bakinta guda ta gutsure hannun wannan maridi ta haÉ—iye.
Damar da bai samu ba kenan ta sukar makoshin Gulzum.
Maridin ya kwarara ihu sa'adda jini ke bulbula ta jikin dungulmin hannun nasa.
Ihun maridin ya haÉ—e da gurnanin macijiyar a lokaci guda.
Nan fa maridan nan suka firgice kowannensu ya fara neman hanyar gudu amma tuni macijiyar mai kawuna dubu arba'in ta fara yi musu ɗauki ɗai ɗai,sai dai kaga kawunanta na saukowa ƙasa suna wangame bakuna suna yin loma ɗaya da maridan.
Shi kansa sarkin maridan bai san
sa'adda ya kama rarrafe ba a ƙasa, sai da ya isa ƙofar ɗakinsa dake kan dutsen har ya tura kansa cikin dakin, sai macijiyar ta finciko shi da ƙarfin tsiya,ta lanƙwame shi.
Cikin tsananin zafin nama macijiyar nan ta ci gaba da cinye maridan nan ɗaya da ɗaya,sai da ta cinye su gaba ɗaya,a cikin abin da bai wuce daƙiƙa ɗari uku da sittin ba.
Koda ta gama cinyesu sai ta zube ƙasa rikica!
Tana ta numfashi da ƙyar.
Kawai sai ta fara shiga cikin wani ƙaton rami dake ƙarƙashin wannan dutse,wanda maridan suka yi gidajensu akai.
Sai da aka shafe sa'a guda cur sannan doguwar jelar macijiyar ta gama ƙulewa a cikin ramin,ta ɓace bat,tamkar bata taɓa wanzuwa ba a wajen.
Nan fa wajen yayi tsit ya zamana ba kowa face Gulzum,Jafar,Yelisa,Mashrila da Mazalish.
Koda Gulzum ya ga ya tsira sai ya daka tsalle ya kama rawa don murna.
Cikin sauri ya sauko daga cikin ƙaton ƙoƙon nan yaje ya kwance su Jafar yace,
"Maza ku zo mu bar wajen nan da sauri don bamu san abin da zai biyo baya ba,babu mamaki macijiyar nan ta sake dawowa idan abin da ta haÉ—iya ya gama
narkewa a cikin ta."
Ba tare da gardamar komai ba su duka suka runtuma cikin jeji da gudu ba tare da sanin inda suka dosa ba,sai da suka yi nisa sosai suka gaji sannan suka tsaya a wani wuri mai tarin rairayi suka zauna suna haki,har suka sami 'yar nutsuwa.
Jafar ya dubi Gulzum yace,
"To kai in banda abinka me wannan macijiya za ta ji idan ta haÉ—iye mu nan duka?
Ka duba fa yadda ta rinƙa loma ɗaya da manyan maridan nan tamkar mutum ya jefa ƙwayar hatsi a bakinsa."
Gulzum ya murtuke fuska yace,
"To ban da abinka ai mai kwaÉ—ayi bashi da ramuwa.
Komai ƙanƙantar abin lasawa baya bari."
Mazalish ta yi ajiyar zuciya tace,
"Kai jama'a wanda bai yi yawo a duniya ba bai sha kallo ba.
Ni kam tun da uwata ta haifeni ko a labari ban taɓa jin labaran macijiya irin wannan ba mai
tsananin girma,kuma mai duban kawuna haka barkatai ba.
Tabbas in muka sami nutsuwa sai
na roƙi Mashrila ta zana mini taswirarta.
Kun ga ku tashi mu kama gabanmu don an ce zama waje daya tsautsayi ne,inji kifi."
Koda jin haka sai Jafar ya bushe da dariya yace,
"Wannan shi ne abun mamaki kare da tallar tsire,wai ya za'a yi a ce aljani yafi bil'adama tsoro.
Gaskiya Gulzum kana bani haushi saboda raguwar zuciyarka."
Cikin tsananin fushi Gulzum ya yunƙura don ya make Jafaru in yaso komai ta fanjama-fanjam,amma haka ba ta yiyu ba, sakamakon ganin wata irin ƙatuwar inuwa da ta lullube su gaba ɗaya daga sama.
Cikin firgici suka É—aga kawunansu sama don su ga abin da ya yi musu
inuwar,kwatsam suka yi arba da wannan ƙatuwar macijiyar nan wadda ta cinye maridan nan ta
zubo kawunanta kas reras, barkatai ba kyan gani suna fesar dafi.
Kafin daya daga cikin su Jafar ya yi wani yunƙuri tuni ta lankwame su
gaba É—aya.
Wannan shi ne abin da ya faru ga su Jafar yayin da suka fuskanci kaÉ—an daga cikin azabobin
muguwar guguwa da ke cikin shafi na goma sha shida a KUNDIN TSATSUBA.

***************

A can fadar sarki Dujalu kuwa bai ci gaba da baiwa su Ruziyal labarin Hikayar jarumi Nazmir da gimbiya Luzaiya ba,sai bayan an zo da kan
wannan bawa mai kula da damisar sarki wanda tsautsayi ya sashi ya manta bai kulle kofar kejin damisar ba a jiya da daddare har ya zamana
damisar ta yi fitar burgu ta shigo fada,kuma har ta nemi hallaka mai gidanta.
Nan take sarki Dujalu ya bada umarnin a yi waje da kan bawan a hada da mushen damisar aje a
binne a jeji.
Bayan tafiyar masu cika umarni ne
sai Dujalu ya yi gyaran murya yace,
"To sai ku shirya don zan ci gaba. Lallai ina son na kai ƙarshen wannan doguwar hikaya ko ma shiga ta gaba,don na sallame ku a cikin kwanaki goma daidai,ku kama gabanku."
Koda jin haka sai boka Hajarul Mukurus ya sunkuyar da kansa ƙasa sakamakon ƙwallar dake shirin zubowa daga idanunsa, sannan yace,
"Ya kai wannan sarki haƙiƙa duk a cikin hikayoyin da ka bamu babu mai tausayi kamar wannan,na roƙe ka da ka hanzarta sanar da mu
ƙarshenta don mu ji yadda za ta wakana."
Sarki Dujalu ya yi murmushi yace, "Ai da sauran abin tausayi ma a gaba.
Ku dai ku bani aran kunnanku idan na gama sai ku yi muhawara."
Nan take sarki Dujalu ya ci gaba da bayani kamar haka.............
Chapter 2 · 0% Book details