Sashe 10
Nihad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a rayuwarsa. Kuma kayi sauri ka dawo nan domin ina son ka kirawo min gaba ɗayan hadimaina domin muyi shirin zagaye duniyar nan a cikin kwana arba'in don yaɗa wannan cuta ga dukkanin manyan sarakunan duniya da 'yan majalisarsu." Kafin Tazibul Luhucul ta gama rufe bakinta tuni aljani Haddagul Gulbur ya kwashe su sarki Alyasil buhus su goma sha ɗaya ya kai su cikin gidajensu ɗaya bayan daya cikin abin da bai wuce daƙiƙa biyar ba. Yayin da iyalan sarki da iyalan 'yan majalisarsa suka ga abin da ya faru sai hankalinsu ya dungunzuma,gari ya ruɗe, ko'ina ka gifta babu zancen da ake yi sai na wannan annobar cuta data samu sarakan gari. Nan fa jama'a suka yi ta shawarwari iri-iri har ma aka haɗa kai aka ƙudiri niyyar zuwa kogon Tazibul Lubucul don a roƙeta gafara. Bayan jama'ar gari sun yi dandazo da niyyar tafiya sai kawai aka ga aljani Haddagul Gubur ya bayyana a sararin sama. Nan take tsoro ya baibaye kowa. Jama'a suka firgice suka kama iface-iface da guje-guje. Cikin kakkausar murya Haddagul Gubur ya daka tsawa yana mai cewa, "Yaku jama'ar birnin Sin na umarce ku daku tsaya waje guda ku saurari saƙo daga mai girma uwar bokaye ko kuma yanzun nan nayi fishi da fishinta." Koda jin wannan batu sai kowa ya tsaya cak a inda yake. Gaba ɗaya garin ya yi sit tamkar babu wani mai rai. In ka ɗauke kukan ƙwari dana tsuntsaye da kuma sautin iska dake kaɗawa ba ka jin komai. Haddagul Gubur yayi gyaran murya yace, "Mai girma uwar bokaye tace a gaya muku cewa ba ta da buƙatar ganin ɗayanku don neman gafarar ta bisa abin da ta yiwa sarki da 'yan majalisarsa. Kuma tace tana mai yi muku gargaɗi cewar duk wanda duk ya kuskura yaje gareta akan wannan batu abin da ya sami sarki da 'yan majalisarsa shine zai same shi." Koda Haddagul Gubur ya zo nan zancensa,sai ya bace ɓat. Nan fa gari ya ruɗe masu kuka na yi masu faɗin albarkacin bakin su na yi. A can cikin gidan sarki kuwa,gaba ɗayan iyalansa sun taru a cikin turakarsa sun kewaye shi,yana kwance bisa gado sai kuka suke gaba ɗaya. Babban ɗansa kuwa a tsaye yake gefe guda ya yi jugum fuskarsa a murtuke babu annuri,haka kuma zuciyarsa cike take da tsananin baƙin ciki. Idanunsa sun kaɗa sun yi jawur, amma ba sa zubar da hawaye. Shi kaɗai sai huci yake kamar macijin da ya fasa kai zai yi sara. Kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar da cewa jarumi ne na gaske,domin yana da ƙirar ƙarfi. Ya kasance saurayi ɗan kimanin shekaru ashirin da biyar,kuma ana kiransa da suna Sammaru. Sammaru kyakkyawan saurayi ne,kuma mai kyawun hali,domin yana da tausayi da taimako ga talakawa,to amma ta yana da matuƙar fushi,domin ba wuya ya zare takobi ya ƙaddamar da mutum musamman mazalunci. A rayuwar Sammaru babu abin da ya tsana sama da zalunci. Sarki Alyasil buhus ya ɗaga kai yana duban iyalansa ɗaya bayan ɗaya,sa'adda hawaye ke zuba a idanunsa,amma bai ga Sammaru ba sai yace, "Ina yarima yake?" Mahaifiyar yarima Alfisa tace, "Ai gashi can a gefe guda." Sarki ya kira Sammaru yace, "Yakai ɗana zo nan gareni mu gana." Sammaru ya tako ƙafafunsa cikin karayar zuciya,ya iso gaban gadon ya durƙusa,sannan ya kama hannun mahaifin nasa ya sumbata kawai sai hawaye ya zubo masa yace, "Yakai Abbana ina so ka sani cewa zuciyata na faman zogi da raɗaɗin baƙin ciki bisa wannan hali da ka shiga. Ina son ka yi mini izini yanzu na tafi kogon uwar matsafa na sare kanta." Koda jin wannan batu sai gaba ɗayan iyalan sarki suka firgice suka faɗi ƙasa suna masu dunƙule jukunansu cikin tsananin tsoro don gani suke tamkar hallakarsu ta zo. Shi kuwa Sammaru ko gizau bai yi ba. Kawai sai sai ya zare takobinsa yayi tsayuwar shirin ko ta kwana. Sarki Alyasil Buhus ya ɗaga hannunsa na dama wanda bai shanye ba,ya kamo hannun Sammaru yace, "Yakai ɗana ka yi haƙuri ka sanyawa zuciyarka ruwan sanyi, ka sani cewa ba za ka iya ba da uwar matsafa,domin tafi ƙarfin ka. In ba don ta ɗauki alƙawari cewar ba za ta taɓa iyalannmu ba,da tuni wannan farucin da kayi ya zamo ajalinka. Ina roƙonka a bisa ƙaunar da ke tsananina da kai da ka janye nufinka na son yaƙar uwar matsafa,abin da nake so da kai shine ka saurari bayanin da zai zo mana akan yadda za'a samo maganin da zamu sha mu warke daga wannan cuta. Yakai ɗana na sani kai jarumi ne mai dakakkiyar zuciya da tsagwaron ƙarfi da jarumta. Bana shakkarka bisa kowanne irin hali da za ka tsinci kanka a ciki. Na sani cewa komai nisan wuri da kuma masifun dake kan hanya za ka iya ke tasu ka kai ga biyan buƙata. Ina son ka jajirce a ranka cewa za ka iya zuwa inda wannan maganı yake ka samo shi." Yayin da yarima Sammaru ya ji wannan jawabi daga bakin mahaifinsa,sai ya ji wani sabon ƙarfi ya zo masa tamkar zai iya y yaƙar duniya shi kaɗai. Cikin zafin nama ya miƙe zumbur ya juyawa mahaifin nasa baya sannan lashi takobinsa yace, "Yakai Abbana ka yi sani cewa na rantse da darajarka da kuma kaifin wannan takobi tawa duk inda wannan magani yake sai na je na nemoshi. Haka kuma komai daren daɗewa sai na tsinke kan Tazibul Luhucul da wannan takobi,domin kuwa ta kasance azzaluma. Lallai ba ni da abokin gaba a doron ƙasa wanda yafi azzalumi." Koda Sammaru ya zo nan a zancensa,sai suka ji ɗakin ya cika da dariyar Tazibul Luhucul. Al'amarin da ya firgita sarki da sauran iyalansa kenan. Shi kuwa Sammaru sai ya gyara tsayuwa gami da ƙara riƙe takobin sa hannu biyu. Dariyar ta ci gaba kamar ba za ta daina ba. Daga can kuma sai wani irin haske ya fara bayyana dishi-dishi a cikin siffar bil'adama. A hankali surar ta haɗu gaba ɗaya sai ga Tazibul Luhucul tsaye a gaban Sammaru riƙe da sandarta ta tsafi,kuma fuskarta a murtuke. Koda Sammaru ya yi arba da ita sai ya kai mata wawan sara a tsakiyar kafaɗarta da niyar tsargeta gida biyu,kawai sai yaji takobin tasa ta sari iska. Sammaru ya ci gaba da saranta amma iska yake sara. Tazibul Luhucul ta ƙyalƙyale da dariya a karo na biyu al'amarin da ya sa Sammaru ya ja da baya kenan ya sauke takobinsa ƙas. Tazibul Luhucul ta nuna shà da ɗaya hannun nata mara sanda tace, "Kai yaro tsaya iya matsayinka domin na gaba ya yi gaba,na baya sai labari. Ina so ka sani cewa duk duniyar nan babu wani mahaluƙi da zai iya kashe ni. Ba don na yi rantsuwa ba akan cewa ba zan taɓa iyalan sarakan garin nan ba da tuni ka daɗe da zama gawa. Ban zo nan dan komai ba sai don na tabbatar maka da cewa ni walki ce daidai da gindin kowa. Matsayina ya wuce yadda kake tsammani. Shawara ɗaya zan baka ka cire batun yaƙi da ni a ranka ka sanya tunanin nemo maganin cutar mahaifinka,domin kuna da ƙanƙanin lokaci. Tabbas indai ba ka samo maganin ba kafin shekara uku daidai sai dai ka dawo ka iske gawarsa." Cikin fushi Sammaru ya dubi Tazibul Luhucul yace, "Ina ne inda wannan magani yake? Na rantse da darajar mahaifina komai nisan wajen,komai masifar dake wajen sai naje na deɓo wannan magani." Tazibul Luhucul ta sake ƙyalƙyalewa da dariya, tace, "Yaüwa haka 'näke sön naji furucin namiji mai zuciyar maza. Kada ka damu nayi alƙawari zan faɗa sai ka jira zuwa tsakiyar daren yau cikakken bayani zai zo ya riske ka har nan." Tana gama faɗin hakan ta rikiɗe ta zama wannan haske. A hankali hasken ya rinƙa disashewa har ya ɓace ɓat. Wannan shine abinda ya faru tsakanin yarima Sammaru da uwar matsafa Tazibul Luhucul a can birnin Sin. A sauran manyan ƙasashen duniya kuwa labari ya iske sarakuna cewa ga wata annobar nan na shirin afko musu,wato gaba ɗayansu zasu zama naƙasssu. Sun sami wannan labari ne daga bakin aljanun da suke bautawa. Nan da nan hankalin sarakunan duniya ya dugunzuma,suka shiga ganawa da aljanun nasu don neman tsari daga wannan masifa mai shirin afkowa. Kowa ya tuntuɓi aljaninsa nasa sai aljanin ya ce da shi ai wannan al'amari yafi ƙarfin sa domin kuwa ba kowane zai haddasar dashi ba face bokanya Tazibul Luhucul uwar matsafa,ita kuwa wannan boka a halin yanzu duk duniya babu wani matsafi ko matsafiya mai tarin sirrikan tsafi kamarta. An ce tana da sirrin tsafi guda miliyan dubu tara da casa'in da tara guda ɗaya ne kacal ya rage mata ta mallaka,kuma duk ran da ta mallake shi za ta iya mayar da duniya tamkar ƙwan kaza a gaban ta. Waɗannan sirrikan tsafi data mallaka guda miliyan dubu tara da casa'in data tara ta ɓoye su ne a cikin wata taska,ita kuwa an ajiye tana a cikin wani kogon dutse. Shi kuwa kogon yana tsakanin duniya ta bakwai da ta takwas daga cikin duniyoyin ƙarƙashin ƙasa. Babu wani abu mai rai da ya taɓa zuwa wannan wuri,kuma ba za'a samu wanda zai iya zuwa ba. Lokacin da sarakuna suka ji wannan jawabi sai duk suka ɗimauce suka firgice, wasu ma dalilin rikirkicewar al'amuransu kenan. Wasu suka kama kuka,wasu kuma suka kama ciwo don tsananin fargabar wannan baƙin labari. Su kuwa aljanun na su sai suka rinƙa kwantar musu da hankali suna cewa su yi haƙuri su saurari jawabin da uwar matsafa za ta yi dangane da inda maganin wannan cuta yake,lallai zasu samo musu shi. A wannan lokaci manya ƙasahen duniya mafi girma guda shida ne,ƙasa ta farko ita ce birnin Sin,sai kuma birnin Hindu sai Rum,Ƙisra,Misra da kuma Farisa. Ƙasar da ake ganin za ta iya biyo bayan waɗannan ƙasashe ita ce Askandariya. A can fadar bokanya Tazibul Luhucul kuwa wato cikin kogonta na tsafi gaba ɗaya hadimanta sun taru sun durƙusa a gabanta yayin da take zaune bisa karagarta ta mulki. Amma bisa mamaki sai suka ga tayi shiru ba ta ce da su uffan ba,kuma ta sunkuyar da kai ƙasa ta nutsu ainun kamar mai jiran umarni. Jim kaɗan sai suka ga wani haske mai launin ɗorawa ya bayyana a tsakiyar