Sashe 16
Nihad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gidan kenan,suka rugo inda yake a firgice. Koda suka zo suka ga halin da yake ciki sai duk suka kama kuka suna cewa, "Shi kenan ta faru ta ƙare,annobar da ake faɗi ta sauka." A can gidan sarkin Kisra kuwa lokacin da Tazibul Luhucul ta sauka a tsakiyar harabar gidan sai ta iske sarki a kishingiɗe yana gyangyaɗi,amma hannunsa guda na kan irin wannan gunki wanda wazirinsa ke bautawa. Koda ganin haka sai hankalin Tazibul Luhucul ya dugunzuma don ta san cewa ba zata iya yi masa komai ba,muddn hannunsa na kan gunkin. Nan fa ta tsaya tana ta saƙe-saƙe a zuciyarta da tunanin mafita. Sai daya zamana alfijir ya kusan ketowa anma bata sami mafita ba. Ta ɗauko mudubin tsafinta ta shafe shi da hannun hagu,take taga duk abin da ya faru tsakanin hadimanta da 'yan mnajalisar wannan birni wato taga cewar gaba ɗaya sun sami nasara akan 'yan majalisar birnin cikin sauƙi,waziri ne kawai ya basu wahala amma shima ɗin a ƙarshe sun gama dashi. Kuma taga cewa tuni hadiman nata sun koma can bayan gari sun tsaya ita kawai suke jira. Gashi kuma saura baifi daƙiƙa ɗari uku da sittin ba lokacin tafiya yayi. Nan fa Tazibul Luhucul ta ji zuciyarta ta cika da mugun baƙin ciki tace a ranta, "Haƙiƙa abin kunya ne ace hadimaina sun sami nasara amma ni na kasa. Ya zama dole nima nayi tunanin dabara kafin ƙarewar ƙanƙanin lokacin da nake da shi." Tana gama aiyana hakan ne,wata kyanwa ta zo giftawa ta gabanta. Cikin fushi Tazibul Luhucul ta kaiwa kyanwar duka da hannunta na dama,ai kuwa kyanwar nan sai ta tsorata tayi tsalle ta faɗa kan sarki. Ba shiri sarki ya farka a firgice,ya miƙe tsaye gami da zare takobinsa ya kama leƙe-leƙe da dube-dube. Ba zato,ba tsammani,sai ya ji komai na tsagin rabin jikinsa ya daina aiki. Take ya faɗi ƙasa,kawai sai jin dariyar Tazibul Luhucul yayi tana mai cewa na gama dashi,na gama da shi. Ƙiri ƙiri ta baiyana a gabansa tana ta yin wannan furuci. Shi kuwa sai ya kurma ihu yana mai kiran sunan ɗansa jarumi yarima Lubaika wanda tuntuni yayi nisa akan hanyarsa ta zuwa dajin dulmus don saduwa da boka Hulumul Makahur. Kafin mutanen gidan sarautar su kawo wani ɗauki tuni Tazibul Luhucul ta ɓace ɓat sai zuwa akayi aka iske sarki a kwance ya zama naƙasasshe. Kamar yadda Tazibul Luhucul tare da hadimanta suka sami nasara a birnin Ƙisra haka ma Saubatul Azwas da nata hadiman suka sami nasara a birnin Rum wato dai suma sun mai da sarkin garin da 'yan majalisarsa naƙasssu masu mutuwar jiki. Bayan wannan gagarumar nasarane suka sake haɗuwa a wata mahaɗa dake tsakanin biranen biyu,nan take suka ƙyalƙyale da dariyar farin ciki. Saubatul Azwas tace, "Yauwa yanzu mun gama da ƙasa biyu saura guda huɗu. Yake ƙawata yanzu sai ki tafi ƙasar Hindu da Farisa ni kuma ki barni da Misra domin itace ƙasa mafi haɗari tunda sun kasance ma'abota addinin musulunci,waɗannan mutane suna iya hallakar da aljanu ta hanyar ƙonesu da wuta irin sihirtacciyar wuta yayin da suke kiran sunayen Ubangijinsu wato abin bautarsu. Koda jin haka sai Tazibul Luhucul tace ai dama babban kaya sai amale,dole ne na barki dabirnin Misra,babu abinda zance dake sai fatan sa'a." Saubatul Azwas ta fashe da mahaukaciyar dariya tana mai buɗe fukafukanta ta tashi sama cikin sauri hadiman dake tare da ita suka bi bayanta,nan da nan suka cilla izuwa ƙololuwar sararin samaniya suka nufi birnin Misra. Tazibul Luhucul da nata hadiman ma suka tashi sama suka nufi ƙasar Hindu da Farisa. Wannan shine abinda ya faru gasu Tazibul Luhucul bayan sun fara samun nasara bisa gagarumar buƙatarsu ta duniya wacce itace mallakar mutane da aljanu dakuma haɗa sinadarin gano inda wani sirin tsafiwanda shine kacal ya rage musu su mallaka a taskarsu ta tsafi. Al'amarin yarima Sammaru kuwa lokacin daya kama hanya ya nufi dajin Dulmas saida yayi tafiyar sa'a bakwai cif ba tare da ya yada zango ba,kuma bai haɗu da wani tsautsayi ba ko mugun abu face namun daji iri-iri waɗanda ko guda ɗaya bata tare shi ba ko afka masa. Yayin da rana ta take sai zafi ya yawaita a jejin,duk da cewa akan doki yake tafiyar sai daya jiƙe sharƙaf da gumi. Da yake zuciyarsa a harzuƙe take ko kaɗan bashi da niyyar tsayawa a ko'ina har sai ya riski kogon da boka Hulumul Makahur yake,dama ya sani cewar tafiyar sa'a goma sha huɗu ce zata kaishi wannan wuri daga cikin birnin Sin. Wato a ƙa'ida in dai mutum ya taso da sassafe tabbas zai isa bayan magariba. Babu zancen yunwa,ƙishirwa ko gajiya a tare yarima Sammaru domin yayi watsi da su a ransa burinsa kawai ya ganshi a gaban kogon tsafin boka Hulumul Makahur. Bisa rashin sa'a sai yaga dokinsa ya fara nuna alamun sarewa domin baya iya sauri sosai kamar da farko,sannu a hankali kuma sai dokin ya fara tafiyar sassarfa,wannan al'amari ya fusata shi amma daya fuskanci cewar dokin ya gaji ne kuma yana buƙatar ruwa da abinci sai ya rungumi ƙaddara ya tsaya ya sauka. Sammaru ya duba gabas da yamma,kudu da arewa don ya hango inda za'a sami fadama. Ai kuwa sai ya hango wata ƙorama wadda ke kwaranya bisa wasu ƙananan duwatsu. A gefenta wasu ciyayine masu tsawo da duhuwa,koda ganin wannan wuri sai murna ta kama shi cikin sauri yaja dokin ya nufi inda wannan ƙorama take. Abin da bai sani ba shine wannan wuri wata mafakace ta waɗansu gungun muggan 'yan fashi. Adadin waɗannan 'yan fashi ya kai dubu biyar,duk suna nan a kwance cikin ciyawa mai duhuwa sunyi lamɓo. Tun sa'adda yarima Sammaru yazo wajen suna ganinsa amma shi bai gansu ba kuma bai ji motsin komai ba a wajen,kai ko kaɗan ma bai taɓa zaton wani mai rai zai iya zama a cikin wannan duhuwa ba in dai kasance ire-iren su kifi,kwaɗo da makamantansu ba. Sammaru ya kai dokin nasa cikin ƙoramar,dokin yasa bakinsa ya sha ruwa ya ƙoshi sannan ya nufi cikin duhuwar nan inda doguwar ciyawa take ya kama cin ciyawar,shi kuwa yarima Sammaru sai ya cire takobinsa da sauran kayan yaƙinsa ya ajiye a gefe guda sannan ya tuɓe kayan jikinsa gaba ɗaya ya ajiye,ya faɗa cikin ƙoramar ya kama wanka. Faruwar hakan keda wuya 'yan fashin nan suka yi fitar burtu gaba ɗayansu suka kewaye ƙoramar duka. Waɗannan 'yan fashi sun kasance gabza-gabza masu ƙirar samudawa kuma suna ɗauke da muggan makaman yaƙi,komai rashin tsoron mutum in yayi arba dasu sai zuciyarsa ta harba,cikin tsananin mamaki Sammaru ya ɗaga kai sama ya dubesu,to amma shi dai yasan duk bala'in da za'ayi sai dai ayi amma ba zai yarda su kämashi ba su wulaƙantashi bare su ɓata masa lokaci bisa saurin daya keyi na isa kogon tsafin boka Hulumul Makahur. Wani garjeje daga cikin 'yan fashin wanda shine mafi girma,kwarjini da ban tsoro ya matsa kusa da Sammaru yace ɗan nema samamme fito kayi gaisuwa gaban sarkin ɓarayin jejin Dulmas tun gabanin banyi fishi da kai ba,ka ware ido kana kallon mu kamar mutum đa mutum. Wannan kalma ta ƙarshe ba ƙaramin ciwo ta yiwa yarima Sammaru ba domin shi a ganinsa anyi matuƙar muzantashi,wai shin ma me wannan ɗan fashi yake nufi da kamar mutum da mutum,lallai akwai raini a cikin wannan batu,wato yana nufin su sune mutane shi kuwa ba mutum bane,cikin tsananin fushi Sammaru ya dubi sarkin ɓarayin ya daka masa harara gami da tsawa yace, "Kai ƙaton banza,la'anannen wofi,shin bakusan ko ni waye ba,kake bani umarnı,kuma har kake ƙasƙantani. To kasani cewa idan kana yi mini kallon jaki ne ni kuma ina yi maka na harawa ne. Babu wani đan da ya isa ya ɗaga hannu a gabana ba tare da na ladabtar da shi ba,nine yarima Sammaru ɗa ga sarki Alyasil Buhus na birnin Sin,duk wani abu daya kwana ya tashi acikin jejin nan ƙarƙashin mulkina da iko na yake." Koda jin wannan batu sai sarkin ɓarayin ya bushe da mahaukaciyar dariya mai kama da gogen tsumma. Nan fa sauran yaransa suka karɓa,ma'ana suka taya shi yin dariyar. Lokaci guda kuma ya tsuke bakinsa ya sake murtuke mummunar fuskarsa mai kama da tatsilallan man shanu yace, "Kai yaro sarauta acikin gari ake yinta banda cikin daji,babu sarki a jeji sai mai ƙarfi,mune sarakan dawa maganin 'yan' dawa da baƙindawa,babu mai shiga dajin nan ya fita lafiya face mun tatseshi ya zama talaka fitik,koda kuwa shine ya fi kowa dukiya,sai mun kwankwashe shi ya zama tamkar ƙwaryar molo kuma sai mun ragarjeje shi ya fatattake tamkar yayin iska." Sammaru yace, "Ai kuwa ƙaryarku tasha ƙarya daga yau kun dena wannan ƙazamar sana'a ta zalunci domin na kasance mala'ikan azzalumai mai mai dasu turɓaya a doron ƙasa." Kafin Sammaru ya gama rufe bakinsa sarkin ɓarayin ya bada izinin a ragargaza shi. A guje mutum hamsin sukayi caaa a kansa da nufin su daddatsashi suyi gunduwa gunduwa dashi a cikin ƙoramar. Kash,rashin sani yafi dare duhu inda waɗannan barade hamsim sun san abin da zai biyo baya da basu haiyakewa Sammaru ba farat ɗaya. Lokacin da baraden hamsin suka yi caa kansa kowa ya kai sara da mugun nufi sai Sammaru ya yi nutso izuwa ƙarƙashin ƙoramar ya lume a cikinta suka nemeshi suka rasa. Cikin ƙaraji sarkin ɓarayin yace dasu suma suyi nutso ƙasa,nan take suka bi umarni. Ai kuwa tunda suka nutse,đayansu bai ɗago ba sai bayan gajeren lokaci sannan aka ga gawarwakinsu na tasowa sama kuma ko kaɗan babu alamar yanka ko tsini ko kaifi a sassan jikinsu. Al'amarin da ya ƙara harzuƙa sarkin ɓarayi da yaransa kenan. Kafin ɗayansu yayi wani yunƙuri sai ga Sammaru ya taso sama daga cikin ƙarƙashin ƙoramar riƙe da takobin ɗaya daga cikin 'yan fashin yana mai ƙaraji. Nan fa 'yan fashin nan suka yi caa kansa gaba ɗaya wuri ya yamutse ya shiga saransu suma suna mai da martani. Sai gashi Sammaru yana kutsawa ta cikinsu,in yaso yayi gabas ko yamma,wani lokacin kuma yayi kudu da arewa. Amma yin hakan baisa ya sami nasaran kai guda ɗayansu ƙas ba suma kuma ɗayansu bai samu damar saransa ko sukarsa ba,nan fa aka ci gaba da artabu da ɗauki ba daɗi. Shi dai Sammaru ya kasance mai tsananin zafin nama da jarumta