← Book details Nihad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 20

Sashe 12

Nihad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

me nema yana tare da samu,amma abin da kamar wuya tsohuwa da tauna ƙwallon goruba." Ko da Sammaru ya zo nan a cikin karatun wasiƙar,sai yayi jifa da wasiƙar. Cikin matsanancin fushi ya zare takobinsa ya nufi ƙofar fita daga cikin turakar sarki Alyasil Buhus,cikin sauri yan'uwansa maza suka ruga suka sha gabansa suna masu bashi baki da lallaminsa,da ƙyar ya haƙura ya dawo ya zauna sannan ya dubi sarki Alyasil buhus yace, "Ya kai Abbana kayi sani cewa haƙiƙa wannan matsafiya ta raina mana hankali. Shin a ina aka taɓa jin cewar wani mahaluƙi ya taba zuwa cikin wata duniya dake ƙarƙashin ƙasa." Sarki Alyasil Buhus ya muskuto da fuskarsa da ƙyar ya dubi yarima Sammaru yace, "Ya kai ɗana haƙiƙa akwai wasu duniyoyin a cikin ƙarƙashin ƙasa kuma na sami wannan labarine daga bakin bokana Hulumul makahur. Na umarceka da kayi shiri gobe da safe ka tafi izuwa jejin Dulmas ka riski boka Hulumul Makahur ka bashi wannan wasiƙar wacce uwar matsafa ta kawo kuma ka buƙaci taimakonsa a bisa wannan al'amari. Tabbas zai taimaka muddin akwai halin taimakawar." Koda jin haka sai Sammaru ya miƙe tsaye ya dubi Alyasil Buhus yace, "Ya kai Abbana kayi sani cewa bazan iya bari sai gari ya waye ba,tabbas a yanzu zanje nayi shiri na tafi jejin Dulmas kuma na rantse da darajarka ko boka Hulumul Makahur ya taimakeni ko bai taimakeni ba,ba zan dawo ba sai da tsumin tsafim uwar matsafa. In kuwa ban samo shi ba kar kuyi sallama gaba ɗaya sai wata rana. Idan da rabon zamu sake saduwa zan dawo." Ko da jin haka sai mahaifiyar Sammaru ta rungumeshi kuma ta fashe da kuka,suma sauran 'yan'uwan na sa duk sai suka matso gareshi suka rungumeshi suna kukan gaba ɗaya. Sarki Alyasil bubus ya share hawaye a idanunsa yace, "Ya kai ɗana ka sani cewa kaine babba a gidan nan don haka kaine mai jiran karagata. Mai zaisa ka yanke wa kanka wannan ɗanyen hukunci yanzu idan baka nan waye zai gaje ni?" Sammaru ya saki yan'uwansa ya dawo ga mahaifin nasu ya durƙusa a gabansa ya kama hannusa na dama ya sumbata a lokacin da gaba ɗayansu suna zub da hawaye. Sammaru yace, "Ya kai Abbana kayi sani cewa ko bana nan akwai ƙanne na don haka sai a zaɓi wanda ya fi dacewa daga cikinsu a bashi sarauta." Alyasil Buhus yace, "Ai kaine kafisu dacewa domin ka gajeni a komai." Sammaru yayi shiru tsawon 'yan daƙiƙu sännan yace, "Na yarda haka ne amma ina so ka sani cewa nine kuma nafi dacewa da tsayawa tsayin daka don kare darajarka da ƙimarka. In dai ina numfashi a doron ƙasa bazan taɓa barin rayuwarka a cikin tozarta ba,lallai sai nazo da maganin wannan cuta taka kafin cikar shekara uku,sai na dawo." Sammaru na gama faɗin haka ya miƙe da sauri ya fice daga cikin turakar. Da yake dama Sarmmaru bai taɓa yin aure ba kai hasalima bai taɓa son wata 'ya mace ba kuma a gaba ɗayan birninsu bashi da aboki ko guda ɗaya don haka bai sake neman kowa ba don yin sallama nan da nan yasa aka shirya masa guzuri sannan yayi shigar yaƙi ya hau wani baƙin ingarmar doki ya kama hanya ya nufi dajin dulmas acikin wannan dare. Wannan shine abinda ya faru tsakanin sarki Alyasil Buhus na birnin Sin tare da ɗansa jarumi Sammaru bayan wasiƙar bokanya Tazibul Luhucul ta riskesu. A can birnin Hindu kuwa sarki Bahacal da 'yan majalisarsa sun kasance cikin tsananin tashin hankali tun sa'adda boka Kirish ya sanar dasu cewa nan da kwana bakwai annobar ciwon mutuwar rabin jiki zata same su kuma sai sun shekara uku suna wannan cuta sannan zasu mutu. Tun a lokacin ne suka tambaye shi,shin babu wata hanya da zasu iya bi su kare kansu daga afkuwar wannan masifa? Boka Kirish yace ai ba wani bane zai aiko da wannan masifa ba face uwar matsafan duniya bokanya Tazibul Luhucul wadda ke zaune a birnin Sin. Tabbas wannan bokanya tafi ƙarfin dukkanin matsafan duniya babu wanda ya isa ya ja da ita. Abin da za'a iya yi shine kawai a saurara aji hanyar da za'a bi a samo maganin wannan cuta domin Tazibul Luhucul tayi alƙawarin baiyana hakan. A ranar da wasiƙar Tazibul Luhucul ta riski sarki Alyasil buhus da 'yan majalisar boka Kirish yaje fadar sarki Bahacal inda ya iskeshi tare da 'yan majalisarsa gaba ɗaya da kuma sauran fadawa da matanen garı a zaune cikin matuƙar ga zulumi da fargaba. Da zuwa sai boka Kirish yayi gaisuwa ga sarki sannan ya zaiyana musu batun zuwa kogon maddarul ikisina don đebo tsumin tsafin bokanya Tazibul Luhucul kuma ya sanar dasu a inda wannan kogo yake. Koda jin wanan batu fiye da kowa ne lokaci,take wasunsu suka kama kuka wasu kuwa suka rinƙa nadamar kasancewarsu a cikin wannan masarauta. Ana cikin wannan hali ne gimbiya Ashwarya ta shigo cikin fadar bisa wani farin ingarman doki sanye da kayan yaƙi kuma ta ɗora gawar wani murgujejen zaki akan wuyan dokin. Dawowarta kenan daga farauta sai ta samu labarin cewa ga boka Kirish can a fada zai yi ƙarin bayani dangane da masifar da akace zata zo ta riski mahaifinta da 'yan majalisarsa. Tun sa'adda labarin al'amarin ya fara zuwa kunnenta ta ɗauki abin tamkar tatsuniya don ma har sai da ta yiwa boka Kirish rashin kunya tace taga alama ya fara zautuwa tunda ya fara zuwa da labaru masu kama da almara. A lokacin da ta faɗi hakan boka Kirish baiyi fishi ba sai yace da ita ta zuba ido izuwa lokacin da abin zai faru lallai zata gasgata shi ta tabbatar da gaskiyar al'amarin. Gimbiya Ashwarya kyakkyawar budurwa ce ta kwatance wadda shekarunta baza su fi sha tara ba. Tun tana ƙarama ta taso da jarumtaka,rashin tsoro da kuma iya yaƙi,tana da matuƙar iya jure wahala,yunwa da ƙishirwa kuma idan ta kece da gudu ko barewa albarka,tana da matuƙar zafin nama kuma ita kaɗai tana iya fasa taron mayaƙa. Haka kuma tana da yawan shige da fice wajen matsafa don haka ta sami sirrikan tsafi da ɗan dama waɗanda suke taimaka mata sosai wajen fuskantar abubuwan haɗari. Bisa wannan daliline take shiga daji ita kaɗai tayi farauta sannan ta dawo gida. Lokacin da gimbiya Ashwarya ta shigo cikin fada ta iske mabaifinta sarki Bahacal da 'yan majalisarsa a cikin halin firgita da damuwa sai ta dubi boka Kirish tace yau kuma da wane labarin ƙanzon kuregen kazo mana dashi. Boka Kirish ya dubeta cikin fishi ya maimaita abinda ya faɗi gasu sarki. Ashwarya ta ƙyalƙyale da dariya tace bazan yarda da wannan labarin ba har sai idan abin da ka faɗi ya tabbata wato sai na gani da idona cewar sarki da 'yan majalisa sun kamu da wannan cuta nan da kwana bakwai,idan kuwa al'amarin ya kasance na rantse da darajar karagar sarki sai na nemo maganin da zasu sha su warke kafin shekaru ukun su cika." Gimbiya Ashwarya na gama faɗin hakan ta kaɗa linzamin dokinta ta wuce izuwa cikin gidan sarautar tana mai tunƙaho da matsayinta. Gaba ɗayan mutanen fadar suka bita da kallo. Yana zaune acikin turakar tsafinsa ya runtse idanu,ƙafafunsa a tanƙwashe suke kamar lauje yana mai fuskantar wani ƙaton kaskon wuta wanda aka cika shi da ƙiraren tsafi kala-kala har guda ɗari ba daya. Gashi babu garwashin wuta a cikin kaskon amma sai wani shuɗin hayaƙine ke ɓulɓula yana tashi sama daga jikin ƙiraren kuma basa ƙonewa. A dai dai wannan lokacine sarki Jamshul tare da 'yan majalisarsa suka banko ƙofar shigowa wannan turaka suka faɗo ciki,a fusace boka Karluz ya waigo ya dubesu a tsanake ba tare da wata fargaba ba sannan ya kau da kai yaci gaba da yin abin da yake. Su kuwa sai suka tsaya suka yi cirko-cirko kamar masu jiran umarni su ƙaddamar. Boka karluz bai sake waigawa gare su ba sai bayan daƙiƙa ɗari biyu da arba'in,cikin girmamawa ya risina ya gaida sarki Jamshul yace, "Ya sarkin sarakai lafiya kazo har nan turakana tare da 'yan majalisarka yanzu alhalin mun rabu akan cewa yau da yamma zan zo fada na riske ku?" Koda jın wannan tambaya sai sarki Jamshul yace, "Tun sa'adda ka labarta mana batun bokanya Tazibul Luhucul da kuma masifar da zata jeho mana muka kasance cikin matuƙar tashin hankali,mun kasa zaune mun kasa tsaye haka kuma mun kasa ci mun kasa sha,barci ya ƙauracewa idanunmu don hakane muka kasa jurewa har yamma tayi kazo fada,wannan shine dalilin da yasa kaga mun kawo maka ziyarar bazata,lallai muna son musan hanyar da zamu bi mu kuɓuta daga wannan masifa." Yayin da boka karluz ya ji wannan jawabi daga bakin sarki Jamshul sai ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubesu ɗaya bayan daya cikin alamun karayar zuciya yace, "Ya shugabana kayi sani cewa bincikena ya tabbatar mini da cewar ba makawa wannan masifa sai ta sameku acikin waɗannan kwanaki bakwai,dama ɗaya ce a gare ku kuma ba komai bace face tafiya neman maganin wannan cuta bayan kun kamu da ita kafin shekara uku,ku sani cewa shi dai wannan magani wanda zaku sha ku warke ba komai bane face tsumin tsafin bokanya Tazibul Luhucul wanda ke ajiye acikin taskar tsafinta. Ita wannan taskar tana can cikin wani kogone da ake kira Maddarul Ikisina. Maddarul Ikisina kuwa na nan tsakanin duniya ta bakwai data takwas daga cikin duniyoyin ƙarƙashin ƙasa." Koda boka Karluz ya zo nan a zancen sa,sai sarki Jamshul da 'yan majalisarsa suka firgice suka rasa abin dake musu daɗi nan duniya,gaba ɗayansu suka yi tagumi suna masu juyayin al'amarin cikin zukatansu. Ba zato ba tsammani sai suka ga yarima Yauhana ya fito daga cikin wani saƙo na wannan turaka shi kansa boka Karluz bai san sa'adda Yauhana ya shigo ba har ya ɓuya a cikin wannan saƙo don haka sai da yayi matuƙar mamaki. Yauhana ya dubi mahaifinsa sarki Jamshul yace, "Ya kai mahaifina ina son ku kwantar da hankalinku bisa wannan al'amari domin in dai akwai wannan kogo na Maddarul ikisina nayi alƙawarin sai na riskeshi a duk inda yake na deɓo muku wannan tsumin tsafi kafin cikar shekara uku." Ko da jin haka sai sarki Jamshul ya fashe da kuka sannan yace, "Ya kai ɗana ka sani cewa
Chapter 12 · 0% Book details