Sashe 18
Nihad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ikisina na sato waɗannan sirikan tsafi kuma na fito lafiya har na dawo nan cikin kogona. Har yau kawo yanzu maganar nan da nake muku ban gano mafita ba,kuma na rantse da darajar rayukan iyayena da 'yan uwana ba zan fasa wannan aiki ba,har ajalina ya riskeni. Wannan shine dalilin da ya sa nace daku kun naɗa gammo don shirin ɗaukar abinda yafi duniya da abinda abin cikinta nauyi domin abu ne wanda ya gagari dukkanin matsafan duniya." Sa'adda boka Hulumul Bakahur yazo nan a zancensa,sai su yarima Sammaru suka yi ajiyar zuciya,cikin zulumi da juyayi yarima Yauhana yace, "Ya kai wannan boka yanzu mun gamsu cewar wannan aiki dake gabanmu gagarumine,to amma ka sani cewa har abada mai rai baya fitar da rai ga samun rabo. Tuni mun sallama rayuwarmu bisa wannan al'amari,don haka babu gudu,babu ja da baya,walau mu dace,walau ba mu dace ba. Yanzu muna so ka sanar damu hanyar da za mu bi mu je wannan kogo na Muddaril Ikisina,inda taskar tsafi take don ceto rayuwar iyayenmu." Boka Hulumul Makahur yayi murmushi yace, "Yaro man kaza,lallai inda ka san bala'in dake cikin wannan al'amari daka rungumi ƙaddara amma koda yake ance ba'a ƙwacewa yaro garma. Zan faɗa muku matakan da za ku bi ku je wannan wuri,amma sai abokan tafiyarku sun iso." Cikin yanayin namaki yarima Sammaru yace, "Su wanene kuma abokan tafiyarmu?" Boka Hulumul Makahur yace, "Abokan tafiyarku mutum uku ne. Akwai gimbiya Ashwarya 'yar sarki Bahacal na birmin Hindu,wadda ta kasance gagarumar jaruma mace,mai dakawa maza gumba a hannu. Akwai yarima Lubaika 'dan' sarki Marluzil Hauras na birnin Ƙisra,sai kuma yarima Larbuz ɗan sarki Katimul Barhul na birnin Farisa,wanda shima gwarzon mayaƙi ne,wanda yayi gagarumar bajinta a nahiyarsu." Gaba ɗayansu sun taho nan don na sanar dasu hanyar da zasu bi suje kogon Muddaril Ikisina. Lallai gobe iyanzu sun iso,sai ku yi haƙurin zuwan goben,domin nayi muku jawabi tare dasu a lokaci guda,kuma na sallameku ku tafi izuwa wannan gagarumar tafiya." Take wata kuyangar aljana ta bayyana gabansa ta duƙa cikin biyayya da gimamawa. Hulumul Makahur ya dubeta yace, "Yake Ikilis na umarce ki daki kai manyan baƙinmu izuwa ga masaukinsu a basu kyakkyawar kulawa domin su sami hutu da nutsuwa. Gobe iwar haka a dawo mini da su nan." Ikilis ta ɗago kai tace, "An gama ya shugabana." Kafin su yarima Sammaru suce wani abu tuni Ikilis ta shafe su da fukafukanta guda ɗaya wanda ya lulluɓe su tamkar an jefa su cikin rijiya. Kawai sai suka ɓace,gaba ɗaya tare da Ikilis ɗin. Cikin abinda bai wuce daƙiƙa uku ba suka tsinci kansu a cikin wani ƙasaitaccen gida mai kyawun gini da abubuwan ƙasaita irin na sarakunan duniya. Barori da kuyangi na bil'adama kyawawa,kuma tsala-tsala nata kai komo,suna ta hidima. Cikin matuƙar mamaki yarima Yauhana ya dubi Ikilis yace, "Nan kuma a ina muke?" Koda jin wannan tambaya sai Ikilis ta bushe da dariya tace, "Ai nan masaukin baƙi ne irin ku sarakai. Daga can fadar mai girma Hulumul Makahur inda na ɗauko ku zuwa nan tafiyar wata uku ce,amma na gajarce ta izuwa daƙiƙa talatin. Ga gadaje nan da kujeru,masu taushi,kuma ga abinci nan da abin sha iri-iri,haka kuma ga matanan kyawawa sai kun zaɓi waɗanda kuke so,ku zauna ku huta sai gobe zan dawo na kwasheku na mai da ku can fadar mai girma." Ikilis na gama faɗin hakan ta ɓace musu ɓat. Cikin farin ciki Sammaru,Yauhana da boka Karluz suka hau ciye-ciye da shaye-shaye har sai da suka sha giya suka bugu,kuyangi kuwa suka rinƙa yin kiɗa da rawa don ɗebe musu kewa. Kai a taƙaice dai anan suka shagala da more jin daɗin rayuwa tamkar sun manta da abin da yasa suka baro gida. Washe gari kuwa Ikilis ta dawo masaukin su yarima Sammaru a daidai lokacin da tayi alƙawarin dawowa. Koda zuwa sai ta riskesu a kwance su duka suna ta sharar barci. Cikin mamaki ta dubi shugabar kuyangin gidan tace, "Me ya faru naga baƙina suna ta yin barci tun jiya,kawo i yanzu?" Shugabar kuyangi ta risina tace, "Ranki ya daɗe ai tun da kika tafi kika bar su suka shagala da ciye-ciye da shaye-shaye,kuma suka far mana basu gushe ba suna more rayuwarsu har dare ya shuɗe kuma alfijir ya keto. Daga sannan ne suka kama aikin rago har yanzu kuma basu farka ba." Koda jin wannan batu sai Ikilis ta ƙyalƙyale da dariya,tana mai cewa, "Tabɗijam yanzu a haka ne waɗannan ragwagen zasu je kogon Muddaril Ikisina. Ai kuwa da ganan ma sun faɗi jarrabawa. A yi dai mu gani,kallo ne namu kawai." Tana gama faɗin hakan ta lulluɓe su da fukafukinta guda. Take ta ɓace tare dasu bata bayyana a ko'ina ba sai a tsakiyar fadar boka Hulumul Makahur. Da zuwa ta yarɓar dasu a ƙasa tamkar wadda ta deɓo gawarwaki. A wannan lokaci gimbiya Ashwarya,yarima Lubaika da yarima Larbuz na zaune a cikin fadar sun harɗe akan kujeru na alfarma suna masu sauraron bayani daga bakin boka Hulumul Makahur bayan ya gama yi musu barka da zuwa. Bayan Ikilis ta ajiye su yarima Sammaru,sai Hulumul Makahur ya dubi su gimbiya Ashwarya ya nuna su Sammaru yace, "Yauwa ga abokan tafiyar taku waɗanda naba ku labarin cewa suna can masaukin baƙi." Gimbiya Ashwarya ta dube su tace, "Me ya faru gare su suke barci,mai nauyi haka?" Hulumul Makahur ya bushe da dariya,sannan yace, "Ai sun sha giya ne mai yawa jiya,kuma sun hole sosai bari na tashe su daga barcin." Nan take boka Hulumul Makahur ya nuna su da đanyatsansa guda na hagu. Take wata irin iska mai ɗan karan sanyi ta fito daga cikin ɗanyatsan ta buge su suka miƙe zumbur a firgice,suka hau kalle-kalle tamkar ɗan ƙauye ya shigo birni. Koda yarima Sammaru da yarima Yauhana suka yi arba da gimbiya Ashwarya sai suka ruđe,suka kiɗime saboda ganin tsananin kyawunta da kwarjininta. Yarima Lubaika da yarima Larbuz suka dubi juna suka yi murmushi. Lubaika ya yiwa Larbuz raɗa a kunne yace, "Ya kai abokina dubi fa yadda suma suka ruđe,lallaı muma ba mu yi laifi ba,da har muka yi faɗa da juna akan gimbiya domin kyawunta ya kai matuƙa." Larbuz yayi dariya ya lce, "Ƙwarai kuwa zancenka dutse ne abokina." Boka Hulumul Makahur ya dubi su yarima Sammaru yace, "Ya ku waɗannan 'ya'yan sarakai ku nutsu ku dawo cikin hayyacinku ku sani cewa in dai kyawun gimbiya Ashwarya ne ke ɗibarku to ku sani zan nuna muku wadda ta fita kyau sau dubu nan ba da daɗewa ba." Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuƙe 'ya'yan sarakunan nan su duka huɗun. Ita kuwa gimbiya Ashwarya sai kishi ya kamata tace a ranta, "Yanzu a cikin duniyar nan har akwai wata mace wadda ta fini kyau? Lallai zan so na ganta a duk inda take." Hulumul Makahur yayi gyaran murya yace, "Kamar yadda nayi alƙawari cewar yau zanyi muku bayanin hanyar da za ku bi ku je kogon Muddaril Ikisina to yanzu zan cika wannan alƙawari,don haka sai ku nutsu da kyau,ku saurareni,kuma ku kiyaye dokokin da zan faɗa muku,domin idan kuka kuskure guda ɗaya ku duka ne za ku hallaka. Abu na farko shi ne daga nan zaku yi tafiyar shekara bakwai idan akan dawakai ne,zuwa inda tsakiyar wannan duniya tamu take idan kuwa akan hadiman aljanuna ne kwana bakwai kacal za ku yi. Zaku keta ta cikin manyan dazuzzuka guda uku masu mugun haɗari kafin ku je wannan wuri. Daji na farko ana kiransa da suna Baluzul Mahaful. Babu komai a cikin wannan jeji face tarin dodanni ƙabila-ƙabila har kala bakwai. Waɗannan dodanni basu da abinci face naman bil'adama. Lallai a cikin wannan daji sai kun yi tafiyar kwana uku cir in dai akan hadimaina ne,tsafi ba zai ƙwaci rayuwarku ba,a wannan daji face tsagwaron ƙarfinku da kuma iya yaƙinku,lallai anan ne zaku jarraba iyakar jarumtakarku. Daji na biyu kuwa shi ne wanda ake kira Zamutul Makatul. Babu komai a cikinsa face mugayen namun dawa,kuma sihirtattu. Dole ne ku yi amfani da tsafi da kuma ƙarfin damtse a wannan wuri. Ga wanda ya san sirrin daji daga cikinku zai samu sauƙin kuɓuta a jejin Zamutul Makatul. Shi ma sai kun shafe kwana uku cur a cikinsa. Daji na uku kuwa wanda shine na ƙarshe ana kiransa da suna Halalil Masur. Shi kuwa wannan jeji babu komai a cikinsa face wata gagarumar wuta mai ci a ko'ina sama da ƙasa. A tsakiyar sararin sama ne kaɗai babu wutar,kuma dole sai dai ku bi ta kan wata doguwar gada a ko yaushe harshen wuta na lasota. Wani karon sai tayi girgiza kamar zata faɗo ƙasa cikin wutar ko kuma ka ga iska na majajjawa da ita,kamar zata yi sama da ita,cikin wutar dake sama. Dole ne ku yi tafiyar kwana guda akanwannan gada. Yayin da kuka je ƙarshen gadar zaku fita daga jejin Halalil Masur ku tsinci kanku a tsakiyar wani tafkeken jeji wanda babu komai a cikinsa face wata doguwar bishiyar gwanda guda daya cal,wadda tsawonta ya kai zira'i ɗari uku. A ƙarshen wannan bishiya ne hanyar zuwa duniyar ƙasa take. Zan baku wani icen tsafi wanda shine zai huda muku ƙasa ku shige cikinta ku yi ta tafiya har sai kun iso tsakanin duniyar bakwai da duniyar takwas,inda kogon Maddarul Ikisina yake. To fa daga wannan wuri ban san yadda za ku yi ku iya shiga cikin kogon Maddarul Ikisina ba. Iyayena da 'yan uwana ma a wannan wuri suka hallaka. Bayanina na ƙarshe a gareku shi ne a cikin bincikena na gano cewa duk duniyar nan babu wani mahaluƙi da zai iya shiga cikin wannan kogon dutse na Maddarul ikisina a sauƙaƙe face gimbiya Fauwaza 'yar sarki Usman na birnin Misra,wadda ita ce macen da tafi gaba ɗayan matan duniya kyawu a wannan zamani. A halin yanzu ta baro ƙasar ta tare da waɗansu dakarun yaƙi,don yaɗa addininsu wanda akewa laƙabi da Addinin Musulunci. Duk ƙasar da ta je sai ta cisu da yaƙi,ta kuma hana su yin addinin da suka gada tun iyaye da kakanni ta ɗora su bisa tafarkin nata addinin. Haƙiƙa gimbiya Fauwaza na da tarin baiwa da sirrikan nasara,ba zamu iya ja da ita ba,gaba ɗayanmu nan face mun mallaki sirrikan tsafi adadin wanda Tazibul Luhucul ta mallaka." Boka Hulumul Makahur na gama wannan jawabi