← Book details Nihad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 20

Sashe 19

Nihad Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read

ya yi nuni da hannunsa izuwa ga allon tsafi sai ga gimbiya Fauwaza tare da dakarunta suna gwabza yaƙi da kafirai a cikin birnin Askandariya. Koda su yarima Sammaru suka ƙyallara ido suka ga gimbiya Fauwaza sai kyawunta ya ruɗe su suka shiga sumbatu da koke-koke tamkar waɗanda suka shekara cikin cutar begenta. Ita kanta gimbiya Ashwarya saida ta raina kanta ta tabbatar da cewa ita kam ba kyakkyawa bace,kyau na wajen gimbiya Fauwaza domin ita ce ƙurunƙus.
Chapter 19 · 0% Book details