← Book details Nihad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 20

Sashe 7

Nihad Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ta ganshi cikin mawuyacin hali,kuma cikin sarƙa a ɗaɗɗaure. Kawai sai ta fashe da kuka. Nan da nan sarki ya sa aka zaunar da ita,shima ya zauna akan karagarsa,sannan yasa aka fara shirye-shiryen ɗaura aurensu. Su kuwa su jarumi Nazmir sai aka jera su a gaban wani ƙaton basamuden bawa baƙin fata wanda ya riƙe wata zabgegiyar adda. Shirin da aka yi shine da zarar an gama ɗaura auren sarki da gimbiya Luzaiya sai wannan baƙin bawa ya sare kawunansu jarumi Nazmir ta yadda jininsu zai zuba cikin wata ƙatuwar tukunyar tsafin boka Shamradu. A kowanne ɓangare na fadar gabas da yamma,kudu da arewa dakaru ne birjik tsaitsaye cikin shirin yaƙi,shi kuwa boka Shamradu na tsaye a tsakanin karagar sarki da ta gimbiya Luzaiya yana murmushin farin ciki, don ya san cewa saura ƙiris buƙatarsa ta duniya ta cika. Tsakanin boka Shamradu da sarki akwai wata yarjejeniya ta cewar idan ya taimaka masa yaga bayan maƙiyansa,shi kuma zai bashi kyautar babban gari daga cikin ƙasarsa ya mulke su,kuma zai zama makusanci a fadar sarki. Lokacin da aka ci gaba da harkokin ɗaurin aure, sai gimbiya Luzaiya ta dulmiya a cikin kogon tunani, inda take cewa da kanta,tabbas idan ta kuskura ta auri wannan sarki rayuwarta ta gama gurbata gaba daya. Babu wani abu da zai sata farin ciki a duniya face ta auri Jarumi Nazmnir masoyin da shi kadai ne zai iya mayar da ita kasarsu ta sadu da mahaifiyarta, kuma ta hau kan karagar mulkin da ta gada. Ta ya ya za ta sami wannan nasara? Babu wata dama face ta tsaida wannan daurin aure, kuma ta ceci rayuwar su jarumi Nazmir. To wai shin me za ta yi ta tsaida ɗaurin auran, kuma me za ta yi ta iya ceton rayuwarsu Nazmir din? Wannan tanbaya ce wadda gimbiya Luzaiya ta yiwa kanta, kuma ta kasa gano amnsarta. Tana cikin haka ne ta tuno da abin da ya faru dazu a dakin bauta tsakaninta da boka Sharmradu. Koda ta tuno wannan al'amari sai ta mike zumbur cikin zafin nama ta shammaci boka Shamradu ta fisge isgar tsafinsa daga hannusa ta cauɗa masa ita a wuyansa. Kawai sai aka ga boka Shamradu ya kankance ya zama ƙanƙanin dutse. Nan fa sarki ya zabura ya faɗa bayan karagarsa ya ɓoye dakaru suka yi ca kan gimbiya ita kuwa ta nunu su da isgar tsafin nan suma sai suka kuma suka zama gumaka. Nan fa fada ta hargitse aka hau guje-guje da iface-iface. Gimbiya Luzaiya ta ruga inda su jarumi Nazmir suke ta nuna sarkar da ta ɗaure su da isgar tsafi, take sarkar ta narke ta zama ruwa. Koda ta ga sun kuɓuta sai ta miƙawa jarumi Nazmir isgar tsafin, ta ce rike wannan ta zama makaminka, kai ne namiji ni kuwa macece ban saba da gumurzu ba. Cikin hanzari Nazmir ya karbi isgar. A daidai wannan lokaci ne sarki ya fito daga maboyarsa koda ya hango iskar tsafi a hannun jarumi Nazrnir sai ya dakawa dakarunsa tsawa ya ce, "Maza ku raba shi da wannan isgar tsafin ku kawo mini ita nan." Gaba daya dakarun wajen suka yi caa kansa, shi kuwa ya rinka nuna su da ita sai dai ka ga tsawa na dira kansu, suna zubewa kasa matattu. Wani lokacin kuma wuta ce jikinsu su kone kurmus. Wani lokacin kuma dai kawai aji wuyansu na karyewa rakakas, ko kuma a ga kibiyoyin tsafi na jukunansu. Anan fa yaki ya yi yaki, Nazmir zubar da maza, amma sai ka waɗansu na daɗa shigowa cikin fadar kamar ba za su kare ba. A wannan yaki sadauki Halufa ya taimakawa jarumi Nazmir matuka, domin shi ma tsohuwar jarumtarsa ce ta motsa, ya dunga girbar maza kamar yana sassabe a gona. Haka ma su Bagwan sun taka muhimmiyar rawa a wannan yaki. Yayin da aka shafe sa'a uku ana wannan yaƙi amma ya ki karewa sai hankalin su jarumi Naznir ya tashi. Don haka sai sadauki Halufa ya bada shawarar a bude hanya da ƙarfin tsiya a fice daga cikin fadar don a fita daga garin gaba daya. Ai kuwa haka aka yi, ámma duk da haka sai da sarki ya ja tawagar miliyoyin mayaka aka bi bayansu Nazmir har aka riske su a daji,sannan aka ci gaba da yaƙi. Yayin da gumurzu ya yi gumurzu,bala'i ya yi bala'i sai isgar tsafin nan ta subuce daga hannun jarumi Nazmir ta fadi ƙasa. Ai kuwa tana faduwa sai kasa ta tsage ta fada ciki. Take kasar ta rufe kanta tamkar an binne gawa a kabari. Koda sarki da dakarunsa suka ga babu isgar tsafi a hannun jarumi Nazmir sai suka yi kukan kura suka afka musu. Nan fa aka buɗe sabon lale,aka ruguntsume da mummunan yaƙi. Wannan yaƙi dai ba'a gama shi ba,sai bayan wata shida. Ma'ana bisa dole aka rinką tsayawa ana ja da baya musamman idan dare yayi. Da safe kuwa sai a sake gamuwa a filin daga a ci gaba da rubdugu. Tsakanin mutanen sarki da mutanan su jarumni Nazmir. A wannan yaƙi ne sadauki Halufa da dukkanin iyayen abokan Nazmir suka rasu,Bagwan ma a wannan yaki ne ya rasa rayuwarsa ya zamana jarumi Nazmir,gimbiya Luzaiya, da Bardil ne kaɗai suka rayu, suma ba su tsira ba sai da taimako ya zo musu daga birnin gimbiya Luzaiya na dakaru miliyan dubu huɗu. Jarumi Nazmir ne ya kama azzalumin sarkin garinsu da ƙarfin tsiya ya đaga sama ya fyaɗa da ƙasa. Take sarki ya sume. Kafin ya farfaɗo Nazmir ya kama wuyansa ya karya ya yar da gawarsa anan ƙasa. Bayan an gama yaƙi ne aka koma birnin gimbiya Luzaiya inda aka ɗaura auren jarumi Nazmir da gimbiya Luzaiyà ya zauna tare da ita a ƙasarta. Mutanensa suka so ya koma gida ya zama sarki,amma ya ƙi yace ya bar gida har abada,tun da ba shi da iyaye a garin bashi da kowa sai Bardil. Don haka sai aka baiwa Bardil sarautar ƙasar."
Chapter 7 · 0% Book details