Sashe 5
Nihad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kuka sani cewar marigayi mahaifin gimbiya Luzaiya ya roƙeni da na fara nuna kansa ga mahaifina tare da yi masa bayanin cewar ya sallama rayuwarsa don ceto tawa. Don haka idan muka shiga cikin gari babu inda zamu fara zuwa face gidanmu don riskar mahaifina. In yaso da safe sai mu tafi gidan sarki mu miƙa masa gimbiya Luzaiya." Yayin da jarumi Nazmir ya zo nan a zancensa sai gimbiya Luzaiya ta dube shi idanunta cike da hawaye tace, "Yanzu da hannunka zaka danƙani a hannun azzalumin sarki wanda ya zamo sanadiyar mutuwar abokanku,waɗanda kuka shaƙu ainun tun yarinta? Ka tuna fa cewa a sanadin wannan azzalumin sarki ne mahaifina ya mutu,kuma a sanadinsa ne aka yi asarar dubannan rayuka, kuma a sanadinsa ne kuka rabu da iyayenku da danginku tsawon lokaci,kuka jefa kanku cikin muguwar rayuwa mai mugun haɗari. Nikam da dai na zama matar wannan sarki gwara na mutu tsuntsaye su cinye gawata,ya zamana an mance da tarihina a duniya har abada." Lokacin da gimbiya Luzaiya tazo nan a zancenta sai hankalin su jarumi Nazmir ya tashi,suka yi shiru cikin matuƙar damuwa da kokwanto. Bayan ɗan gajeran tunani,sai jarumi Nazmir ya dafa kafaɗunta a karo na farko tun haɗuwarsu,suka tsurawa juna ido yace, "Yake gimbiya,sarauniyar kyawawan duniya ki kwantar da hankalinki ki sani cewa ni jarumi Nazmir na yi miki alƙawari cewar har abada ba zan bar rayuwarki ba a cikin ƙunci da baƙin ciki,lallai zan kuɓutar dake,kuma na mayar da ke kasarku don ki sadu da mahaifiyarki ki ci gaba da rayuwarki ta sarauta,kamar da a cikin ƙasarki ta haihuwa." Koda jin haka sai gimbiya Luzaiya tayi murmushin yaƙe sannan tace, "Duk wannan ba zai burgeni ba face ka hana faruwar aure a tsakanina da azzalumin sarkinku." Nazmir ya yi shiru bai ce komai ba, domin ya san cewa shi kam bai isa ya hana wannan aure ba. Yayin da Luzaiya ta ga jarumi Nazmir ya yi shiru bai ce komai ba sai zuciyarta ta karaya ta cigaba da zubar da hawaye tace, "Shi kenan kuyi duk yadda kuka so, amma ku sani cewa na gama yanke shawara cewa lallai a ranar da aka ɗaura aurena da sarki zan kashe kaina." Daga wannan furuci Luzaiya ta tsuke bakinta bata ƙara cewa komai ba. Kawai sai ta koma gefe guda ta ci gaba da kuka abinta. Nan fa su jarumi Nazmir suka shiga cikin sabon tsahon hankali da matuƙar damuwa,sai da suka shafe rabin sa'a suna masu tunanin mafita,amma babu. Kawai sai jarumi Nazmir ya bada umarnin kowa ya sauya kamaninsa. Nan take aka bi umarnin. Ita kanta gimbiya Luzaiya sai da aka ɓatar da kamanninta duk da tsananin kyawun nan nata ya dishashe aka mai da ita mummunar gaske. Bayan an gama wannan shiri ne suka hawa dawakansu suka nufi ƙofar gari. Da zuwa suka ƙwanƙwasa ƙofar,maigadi ya leƙo ta cikin wata mitsitsiyar taga ya dube su yace, "Su waye ku?kuma daga ina kuka fito,har da kuke ƙoƙarin shigowar a tsakiyar dare haka?" Jarumi Nazmir ya make muryarsa yace, "Mu manzanni ne daga ƙasar Maskur mun zo da saƙo na musamman ga sarki daga hannun sarkinmu." Koda jin haka sai maigadin ya rufe wannan mitsitsiyar taga. Jim kaɗan sai suka ji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar gaba ɗaya. Ita dai wannan kofar shiga gari ta kasance ƙatuwar gaske,domin tsawonta ya kai kamu ɗari shida haka kuma faɗinta ya kai kamu ɗari bakwai. An yi ta ne da zunzurutun ƙarfe mai kauri da nauyin tsiya. Mutum arba'in ne ke buɗe ƙofar waɗanda suka kasance ƙarti majiya ƙarfi. Bayan an gama buɗe ƙofar sai su jarumi Nazmir suka ga dakaru sama da mutum dubu ɗari a tsaitsaye bisa dawakai sun yi sahu a gabansu,kuma gaba ɗayansu cikin shirin yaƙi suke. Ba a bar jarumi Nazmir sun wuce ba sai da aka kawo fitila aka haske fuskokinsu aka yi nazarinsu sosai. Bayan hakan ma sai aka haɗa su da wasu dakarun mutum hamsin don su wuce dasu kai tsaye izuwa gidan sarki. Yayin tafiya gidan sarki ne zuciyar jarumi Nazmir da ta abokan tafiyarsa ta cika da mamaki domin ba su san dalilin wannan tsatstsauran matakin tsaro ba da aka ɗauka a garin. Haka kuma sai suka kasance cikin fargaba,domin idan suka bari aka kai su gidan sarki kai tsaye an tarwatsa shirinsu gaba ɗaya. Nan fa suka fara tunani da saƙe-saƙen zuci. Dabara dai bata faɗo musu ba,har suka shigo wata siririyar hanya matsatstsiya. Sai da suka zo tsakiyar hanyar sannan jarumi Nazmir ya dubi Bardil da Bagwan ya yi musu wata irin inkiya,suma sai suka yiwa sauran baradensu. Cikin gaggawa Nazmir,Bardil, Bagwan da baradensu suka zare takubba suka afkawa waɗannan barade hamsin masu yi musu rakiya izuwa gidan sarki. Cikin abinda bai wuce daƙiƙa ɗari da ashirin ba,suka karkashe su gaba ɗayansu ba wanda ya tsira. Nan da nan suka kwashe gawarwakin suka jefa cikin wata tsohuwar rijiya wacce babu ruwa a cikinta suka rufe,sannan suka sauya hanya suka nufi gidan mahaifin jarumi Nazmir wato sadauki Halufa. Abin ka da 'yan gari duk inda suka bullo suka ga dakarun tsaro sai su sauya hanya. Haka dai suka ta kauce-kauce da raɓe-raɓe har suka iso gidan sadauki Halufa ba tare da wani ya gansu ba. Koda suka hango gidan a kulle kuma suka ga dakarun sarki a kofar gidan a tsaitsaye suna kai-komo sai suka laɓe suka tsaya suna mamaki. Jarumi Nazmir ya dubi su Bardil yace, "Yaku abokaina ku yi sani cewa ruwa baya tsami banza. Lallai akwai wani mugun abun da wannan azzalumin sarki namu ya shirya a kanmu. Yanzu mene ne abin yi?" Bardil yayi gajeran tunani,sannan yace, "Bai kamata mu yi komai ba face mun gano abin da aka shirya a kanmu,ina ganin zai fi kyau mu je gidana da kuma gidan Bagwan don muga halin da suke ciki tun da mun ga halin da gidanku ke ciki. Ba tare da wata gardama ba suka tafi gidajen biyu. Abin da suka gani a gidan su jarumi Nazmir shi suka gani a gidan su Bardil da Bagwan. Nan fa hankalinsu ya dugunzuma ainun suka rasa abin da zasu yi. Daga can sai dabara ta faɗo musu suka haura gidan wani maƙocin Bagwan wanda ya kasance tsoho ɗan shekara tamanin da huɗu ana kiransa Hamlabi. Lokacin da suka shiga,Hamlabi na ta sharar barci har da munshari kai ka ce wata dabbar ce ke gurnani. Sai da suka zo kansa suka tsaya bai sani ba. Nan take Bagwan ya bugi tulelen cikin Hamlabi mai kama da kwarya. Hamlabi ya farka a firgice. Koda yaga zarata a gaban sa riƙe da takubba tsirara,sai ya taƙarƙare zai ƙwalla ihu. Cikin sauri Bagwan ya toshe masa baki da hannu yace, "Kada kayi ihu ya kai Hamlabi kayi sani cewa nine Bagwan maƙocinka, waɗannan kuwa su jarumi Nazmir ne abokaina da kuma sauran dakarun nan waɗanda sarki ya haɗamu da su don zuwa dauko gimbiya Luzaiya a can ƙasarsu." Koda jin wannan batu sai jikin Hamlabi ya kama karkarwa alamun tsoro ya bayyana ƙarara a fuskarsa. Cikin sanyin jiki Hamlabi ya miƙe tsaye ya je ya dauko fitila,sannan ya zauna ya dubi Bagwan yace, "Yakai maƙocina ya ya akai kamanninka suka sauya haka gaba ɗaya? Na rantse da darajar tsufana ko kaɗan fuskarka ba ta yi kama da ta makocina Bagwan ba,haka kuma suma waɗannan abokan tafiyar taka basu yi kama da su jarumi Nazmir ba,amma kuma gaskiya na ji cewar muryarka na nan kamar yadda na santa." Koda jin wannan batu sai Bagwan ya yi murmushi,nan take ya ɗebi ruwa ya wanke fuskar tasa,sai ga kamanninsa sun bayyana ƙarara. Al'amarin da ya jefa tsoho Hamlabi cikin matuƙar mamaki kenan,ya buɗe baki galala yana kallonsa. Daga can kuma sai yayi ajiyar zuciya ya dubi Bagwan ya ce, "Haƙiƙa kun yi babbar hikima,in ba don kun ɓatar da kamaninku ba da tuni yanzu kun daɗe da zama gawarwaki." Koda jin haka sai mamaki ya kama su Bagwan. Nazmir yace, "Yakai wannan tsoho wai shin meke faruwa ne? Ka sani cewa mun je gidajenmu mun iske su a kulle,kuma dakarun sarki na gadinsu." Yayin da tsoho Hamlabi ya ji wannan tambaya sai ya gyara zama gami da gyaran murya,kuma ya saita muryarsa tasa ƙasa-ƙasa yace, "Bayan tafiyar ku izuwa birnin su gimbiya Luzaiya wani hatsabibin boka ya bayyana a ƙasar nan, kuma ya nunawa sarki duk abin da ya faru gareku a cikin wani madubin tsafi. Duk yaƙin da kuka yi har da yadda mahaifin gimbiya Luzaiya ya sallama kansa gareku,ku ka sare kansa,ku ka taho mun gani a wannan madubin tsafin. Kai na taƙaice muku labari dai har lokacin da gimbiya ta faɗa ƙasan tsaunin nan don kashe kanta jarumi Nazmir ya bita kawo izuwa haɗuwarku akan dutsen nan inda Nazmir ya harbe barewa duk kowa a garin nan ya gani a cikin madubin tsafin can a fadar sarki. Bayan an gama ganin hakan ne boka Sharmadu ya sanar da sarki cewa kada ya kuskura ya bar iyayenku daku a raye. Muddin yayi haka kuwa har abada ba zai auri gimbiya Luzaiya ba, kuma ku ne zaku zama sanadiyar ajalinsa. A dalilin haka ne sarki ya sa aka kamo iyayenku gaba ɗaya aka kai su cikin turakarsa aka ɗaɗɗauresu da sarƙoƙi,yanzu haka ana jira ne ku iso a kamaku a hada da su a kashe ku lokaci guda dan haka dokar boka Sharmadu ta kasance. Bisa wannan dalili ne na yi mamaki matuƙa da na ganku a cikin gidana don nasan cewa an saka matakan tsaro masu tsauri akanku,wai shin ma ya akai kuka shigo nan ba tare da an kama ku ba? Ina mai yi muku ta'aziya bisa rashin abokanan ku,kuma masoyanku waɗanda kuka taso tare tun yarinta." Sa'adda tsoho Hamlabi ya zo nan a zancensa sai idanunsa suka ciko da ƙwalla,domin tausayin su jarumi Nazmir ne ya turnuke shi. Jarumi Nazmir ya dafa kafaɗar tsoho Hamlabi yace, "Yakai wannan tsoho haƙiƙa ka taimakemu da ka sanar damu halin da ake ciki. Yanzu wacce irin shawara zaka bamu domin mu tsira da rayuwarmu da kuma rayuwar danginmu?" Tsoho Hamlabi yayi shiru bai ce komai ba yana tunani. Nan take Bagwan ya shiga tunanin matarsa Muslaiya,wacce ya tafi ya bari da tsohon ciki wadda a halin yanzu bai san halin da take ciki ba.