← Book details Nihad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 20

Sashe 8

Nihad Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Lokacin da sarki Dujalu ya zo nan labarinsa sai ya yi shiru ya dubi boka Hajurul Mukurus,tsoho Rafkanagu da Ruziyal yace,
"yanzu ya ya kuka ji wannan hikayar ina fatan dai kun ji daÉ—inta?"
Ruziyal yace, "Ƙwarai kuwa ai na ji daɗinta,musamman yadda na ji ƙarshen wannan azzalumin sarki sai dai kuma na ji tausayi
matuƙa da ya zamana iyayen jarumi Nazmir sun mutu har da sauran abokansa ya rage mutum ɗaya jal daga cikin su, wanda hakan ne ya sa ya ji garin nasu ya fita daga ransa."
Tsoho Rafkanagu yace, "Ƙwarai kuwa nima haka na ji a raina, amma fa gaskiya wannan hikayar ta cika tsawo ina fatan ta gaba ba ta kai wannan yawa ba?"
Sarki Dujalu ya bushe da dariya yace, "Ai hikayar da zan ba ku nan gaba ta ninka wannan
sau biyu a tsawo,kuma akwai abubuwan al'ajabi da yawa a cikinta,sai ku gyara zama ku kasa kunnuwanku don ku ji ta."
Caraf sai boka Hajarul Mukursu yace,
"Ranka ya daɗe zai fi kyau dai kasa a sake kawo mana sihirtaccen shayin nan naka mu sha, don mu ƙara kimtsawa tun da dai ka ce hikaya ce mai tsawo."
Sarki Dujalu ya sake bushewa da dariya yace, "Wannan babu laifi."
Nan take ya ce, aje a gayawa kuyanga mai shayi ta kawo. Cikin hanzari wani bafade ya miƙe ya shiga cikin gida. Wannan shi ne abin ya faru a fadar sarki Dujalu bayan ya gama basu labarin hikiyar jarumi Nazmir da gimbiya Luzaiya.

*********

Al'amarin su jarumi Hubairu kuwa,bayan sarki Lu'umanu ya sace gimbiya Sima ya ɓace da ita a cikin sararin samaniya,sun neme shi sun rasa, sai hankalin Hubairu ya ƙara dugunzuma,
ya rasa abin da ke masa dadi, a duniya. Koda ganin halin da ya shiga sai sai aljani Abtarul
Hudes ya shiga rarrashinsa yana mai kwantar masa da hankali cikin daÉ—aÉ—an kalami, da nuna
masa mubimmancin rungunar ƙaddara.
Hubairu ya yi shiru bai ce komai ba. Daga bisani sai ya dubi Abtarul Hudes yace, "ya kai
Abtarul Hudes ka yi sani cewa shi SO cuta ce,wadda in dai ta shigi mutum har abada ba zai
warke ba,face ya sadu da masoyinsa. Ka yi sani cewa sarki Lu'umanu va zama babban maƙiyi na a duniya, tun da yana son ya raba ni da masoyiyata, kuma yana son ya abin da nake so kuma yana son daƙile addinina.
Abinda nake so da kai kawai shine ka ƙara azama don mu isa birnin Teheren da wuri
kafin Mushrikin nan ya samu damar aurar
masoyiyata.
Idan hakan ta faru zan kasance cikin baƙin ciki. Da yardar Alah zamu sami nasara akansa,kuma tsafinsa ba zai sami tasiri akan mu ba."
Yayin da aljani Abtarul Hudes ya ƙara ƙarfin kaɗawar fukafukansa, ya zamana suna masu tsananin gudu sai keta gajimare suke tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya.
A can birnin Teheren kuwa tuni sarki Lu'umanu ya sauka da gimbiya Sima har ma ya tashe ta daga wannan barci da ta daɗe ta na yi,amma bai tashe tan ba, sai bayan ya tsafanceta ya juyar da tunanin ƙwaƙwalwarta ya zamana ta mance da duk abubuwan da suka faru gareta a
baya. Wato ƙwaƙwalwar ta zama sabuwa tamkar ta jaririyar da aka haifa yau babu komai a cikinta face abin da za'a sa mata.
A cikin turakar sarki Lu'umanu bisa wani ƙasaitaccen gado na alfarma. Gimbiya Sima ce a zaune fuskarta cike da murmushi da annuri,kuyangi na ta shige da fice a ɗakin ɗauke da kayan marmari iri-iri da kuma sauran nau'in abinci da abin sha. Duk suna kaiwa gimbiya
Sima ne don ta zaɓi abin da za ta ci amma har yanzu ba ta zaɓi komai ba. Daga ƙarshe dai naman ɗawisu ta ci,sannan ta sha ruwan inibi.
Bayan ta gama kimtsa cikin ta ne,kowa ya fita ya barta,sannan sarki Lu'umanu ya shiga ciki ya risketa,da shigarsa ya ƙare mata kallo sama da ƙasa ya ga irin tsananin kyawunta sai farin ciki ya turnuƙe shi ya ji kamar an bashi duniyar nan gaba ɗaya. Sarki Lu'umanu ya zauna a gefen gadon kusa da gimbiya Sima suka dubi juna suna masu murmushi,mai nuna tsantsar so da bege. Lư'umanu yace,
"Yake masoyiyata ki yi sani cewa gobe i yanzu kin zama matata,ina nufin an É—aura mana
aure,yanzu me kike so a cikin faɗin duniyar nan na baki shi,koda kuwa yana ajiye a can bangon ƙarshen duniya?"
Gimbiya Sima ta ƙyalƙyale da dariya tace,
"Bana son komai daga gareka ya masoyina face ka yawata dani ko'ina da ina acikin gidan sarauta don na marewa idanuna da kallo."
Koda jin wannan batu sai sarki Lu'umanu ya bushe da dariya sannan yace ai wannan bukata taki a komai sauƙi ce a wajena. Nan take Lu'umanu ya nuna tagar ɗakin da hannunsa kawai sai tagar ta buɗe daddumar tsafinsa ta shigo ta cikin tagar.
Daddumar ta sauko ƙasa ta dira a gabansa kawai sai ya kama hannun Gimbiya suka hau kan daddumar suka zauna.
Zaman su ke da
wuya daddumar ta tashi dasu sama ta ringa shiga dasu saƙo saƙo lungu lungu na gidan sarautar kai har cikin kurkukun nan na ƙarƙashin ƙasa inda aka taɓa tsare aljani Markahul sabus sai da suka shiga. Anan né suka riski waziri kuddaru a ɗaure cikin sarƙa an ajiye abinci a gabansa ya zubawa abincin idanu yana kuka,koda ya ɗago kai yaga
Gimbiya Sima tare da sarki Lu'umano bisa daddumar tsafi saiya miƙe zumbur ya dubeta yana mai cewa ranki ya daɗe ki ceceni kisa a fitar dani daga cikin wannan mugun wuri,ki
tuna cewa ni ne waziri Kuddaru babban wazirinki.
Koda jin haka sai Gimbiya Sima ta dubi Kuddaru tace,
"Waye kai,a ina kasanni?
Waishin ma a ina muka taɓa haɗuwa har da zakace ka sanni?"
Yayin da Kuddaru yaji wannan batu sai ya cika da mamaki baisan sa'adda ya fashe da kukaba yana mai cewa,
"Yanzu har daÉ—in daula yasa kin manta dani. Ranki ya daÉ—e kiji tsoran Ubangijin da kikayi imani da shi ki ceci rayuwata." Girnbiya Sima ta dubi sarki Lu'umanu tace,
"Wannan kuma wane wawan mutum ne haka kamar mahaukaci?"
Lu'umanu ya bushe da dariya
yace,
"Ai kuwa mahaukacine na ƙwarai,asalinsa bawana ne mai kula da bargar dawaki. Rana ɗaya ya sani taɓin hankali ya rínga kashe mini
đewakai. Ni kuma da naji haushin abin daya aikata sai nasa aka kamo shi nan aka ɗaure.
Bazan yi masa komaiba har sai na kama babban maƙiyina da'ake kira Hubairu sannan zan
haÉ—asu tare nayi musu kisan gilla."
Sima ta sake duban sarki Lu'umanu tace,
"Waye kuma Hubairu,kuma menene ya haddasa muguwar gaba a tsakaninku?"
Lu'umanu ya numfasa yace, "Hubairu wani hatsabibin yarone mai taurin kai da ƙarfin
sihiri bashi đa burin da yafi ya rabani dake kuma ya hallakani." Koda jin haka sai gimbiya Sima a dafe ƙirji cikin alamun razana tace,
"Ya kai masoyina duk wanda ya nemi shiga tsakanina da kai sai naga bayansa. Domin duk duniya babu abinda nake so sama da kai. Duk ranar da ka
kama Hubairu ka bani dama na tsireshi da mashi da hannuna don hankalina ya kwanta na tabbatar da cewa na kashe maƙiyinmu."
Koda jin haka sai sarki Lu'umanu ya bushe da dariya yana mai
cewa tabbas nayi miki alkawarin wannan dama kece zaki kashe maƙiyinmu da hannun ki.
Lu'umanu yaci gaba da rusa dariyar ƙeta har suka bar wannan wuri inda kuddaru ke zaune yana ta faman kuka da mamakin abin da ya faru tsakaninsa da Gimbiya Sima.
Kashe gari da sassafe fadar sarki
Lu'urnanu ta cika ta batse da jama'a. Baƙin sarakuna kuwa suka hallara daga manyan ƙasashe don amsa gaiyatar sarki Lu'umanu bisa ɗaurin aurensa da gimbiya Sima.
Nan take aka fara kaÉ—e kaÉ—e da bushe bushe,kayan ciye ciye
dana shaye shaye kuma suka yawaita a fadar fiye da buƙatar Jama'a.
Sarki Lu'umanu da Gimbiya Sima suka fito daga cikin gidan sarauta suka zo suka zauna akan karaga mai É—aura aure ya fara
aikinsa. Ana cikin wannan haline aka ga aljani Abtarul hudes ya baiyana a sararin sama É—auke
da jarumi Hubairu.
Koda sarki Lu'umanu ya É—aga
kai yayi arba dasu sai ya hura musu wata irin iska mai sanyi daga cikin bakinsa,take suka
faɗo ƙasa sumammu.
Sarki Lu'umnu ya bushe da dariya yasa aka ɗauki jarumi Hubairu aka banƙareshi a jikin dirka sannan aka ɗaukeshi da igiya nan take yasa aka dauko kuddaru daga cikin kurkuku aka daureshi kusa da Jarumi Hubairu.
Kuddaru ya dubi jarumi Hubairu yaji daÉ—i a ransa yace tunda mun sake saduwa babu mamaki wannan karon ka ceci rayuwata.
Maimakon yaji Hubairu yace wani abu sai yaji yayi shiru.
Koda ya dube shi da kyau sai ya fuskanci cewar ai ko motsi ba yayi bare ya taɓuka wani abu.
Nan fa Kuddaru ya rikice ya
kuma firgice ya ƙaddarawa kansa mutuwa. Adai dai wannan lokaci sarki Lu'umanu ya baiwa
Gimbiya Sima mashi yace,
"Ungo kije ki tsire wancan saurayin shine babban maƙiyinmu a duniya."
Take ta karɓi mashin ta nufi inda Hubairu ke ɗauke fuskarta a murtuke ba tausayi.
Wannan shine abin da ya faru a fadar sarki Lu'umanu na birnin teheren bayan ya sami nasarär tsafance zuciyar Gimbiya Sima ta soshi fiye da komai a duniya kuma yayi sa'ar kama jarumi Hubairu da aljani Abtarul Hudes.
Al'amarin su Boka Durfus kowa bayan sun gama tattaunawa dangane da yadda zasu sami nasara akan Boka Shamharu Shahararre sai sukayi shiri suka nufi garin da sarkin ɓarayin
Aljanu yake.
Suna cikin tafiya a sararin samaniya su biyar kawai sai suka gawani abu mai kama da bakan Gizo yasha gabansu kuma abin na fitar da tartsatsin wutane tamkar batoyi ita kuwa wutar ta kasance mai hucin zafi kana doso ta sai kaji kamar ana dafa naman jikinka, cikin tsananin tsoro su duka biyar din suka ja da baya a sararin samaniya. Markahul sabus,bokanya Samaratu,boka Jinshan,boka Sulbaini da boka Durfus su kayi tsuru tsuru kamar jiƙaƙƙen tsumma a rüwa suna masu duban juna
Kowannansu ka duba kasan a matuƙar tsorece suke dan jikinsu ma karkarwa yake yi cikin ƙarfin hali Markahul Sabus ya dubi aljani Durfus yace,
"Yakai sabon boka mai abin al'ajabi mene ne wannan abun da ya sha gabanmu?"
Durfus ya haɗiyi miyau da ƙyar yace,
"Ashsha,kallonmu yake gaba ɗaya. Haƙiƙa daga yanzu tamu ta ƙare,duk wani buri da muke da shi cewa wannan abin da kuke gani a gabamu ba komai ba ne face boka Shamharu shahararre."
Durfus na gama faɗin hakan suka ji an ƙyalƙyale da mahaukaciyar dariya. Nan take
bakan gizon nan ya rikiɗe ya zama aljani Shamharu yana mai ƙyalƙyala dariyarsa,har wani irin tururin masifa ne ke fita daga bakinsa.
Nan take tsoro ya ƙara baibaye su Markahul Sabus suka ruɗe, suka rasa abin yi.
Shamharu ya daka musu tsawa yace,
"Ku ƙananan ƙwari ku sani cewa kun yi sake na rigaku kwana don haka dole ne na rigaku tashi.
Ina sanar muku cewa a yau ne na fito daga halwar tsafina kuma na gano hanyar da zan bi na zama MATSATSUBI a cikin wasu 'yan shekaru. Duk wani shiri da kuke yi a kaina na san da shi.
To ku sani cewa na gaba yayi gaba na baya kuwa
sai labari. Ni Shamharu shahararre na gama da duniya, don na san gaba dayan sirrin cikinta.
Da sannu zan mallaki komai da da kowa.
Ku kuwa ba zan hallaka ku ba, yanzu zan tafi da ku ne izuwa kurkukun fadata da ke can tsibirin Baharzus na ajiye ku a matsayin fursonini.
Ba zan sake ku ba har sai na zama MATSATSUBI nan da shekara goma sha tara da wata shida masu zuwa."
Koda jin wannan batu sai su Markahul Sabus suka yunƙura suka juya da baya don su gudu, amma sai suka ji wata irin iska mai ƙarfin tsiya ta tsaida su a waje daya,sun kasa yin gaba
ko baya.
Shamharu ya dube su ya sake ƙyalƙyalewa da dariya,kawai sai ya buɗe tafin hannunsa guda.
Take su Markahul Sabus suka zama 'yan ƙanana,mini mini suka faɗa tafin hannun Shamharu,shi kuwa sai ya buɗe aljihun rigarsa ya watsa su ciki.
Suka ji kamar an jefa su cikin rijiya gaba dubu. Take Shamharu ya rikiɗe ya zama bakan gizo sannu a hankali bakan gizon ya ɓace ɓat a sararin samaniya.
Wannan shi ne abin da ya faru ga su boka Jinshan bayan sun yi mugun gamo da boka Shamharu a sararin samaniya yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa birnin sarkin ɓarayin
aljanu.
Aljanin dashi kaÉ—ai ne zai iya zuwa fadar boka Shamharu ta tsibirin Bahar Zus ya sato addar tsafi.
A can fadar sarki Dujalu kuwa, jim kaÉ—an da aika bafade cikin gida,sai ga kuyanga ta fito É—auke da butar sihirtaccen shayi.
Koda shigowarta cikin fadar sai sarki Dujalu ya dubeta yace, "Maza ki zuzzuba mana shayin nan mu sha har kowa ya gamsu."
Cikin sauri kuyanga ta cika aikinta. Tana gamawa ta shige cikin gida riƙe da butar shayin
wacce babu ko digo guda a ciki. Sarki Dujalu yayi murmushi gami da gyaran murya yace,
"Shin akwai mai buƙatar ƙarin shayin ne?"
Gaba É—ayansu suka ce, "A'a."
Sarki Dujalu ya sake yin murmushi a karo na biyu,yace,
"To sai ku nutsu da kyau domin
yanzu zan baku labarin Hikayar wata azzalumar boka da ake kira Tazibul Luhucul da manyan
sarakunan duniya guda shida. Wannan al'amari ya faru ne a birnin Sin. ldan kuka nutsu sosai zaku ji abubuwan al'ajabi da kuma tsabar tuggu da kisisina waɗanda za su amfani rayuwarku wajen kare kanku daga sharrin maƙiya da mahassada......
Chapter 8 · 0% Book details