← Book details Nihad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 20

Sashe 3

Nihad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lokacin da jarimi Nazmir ya saɓa gimbiya Luzaiya a kafaɗarsa yana laluben hanyar da zai bi ya koma wajen 'yan uwansa su Bagwan. Sai Luzaiya tayi ta zulle-zulle tana ihu gami da dukan bayansa da hannu biyu,don ya sauketa ƙasa,shi kuwa sai ya yi biris da ita tamkar wanda ya goya kaza. Haka dai ta yi ta wutsil-wutsil a bayansa shi kuwa ya ci gaba da tafiya ta cikin kwazazzabai,duwatsu da ruwa yana dube-dube da ƙwalawa abokansa kira,amma shiru bai ji komai ba,a jejin face amsa kuwwar muryarsa. Sai da ya jima a cikin wannan hali har ya zamana gimbiya Luzaiya ta gaji da ihu muryarta ta dashe kuma ko hannayen tama ba ta iya daga su. Bisa dole ta rungumi ƙaddara ta daina motsi. Saboda gajiya sai barci ya kwashe ta akan kafaɗar jarumi Nazmir. A wannan lokaci duhu ya soma, kuma jarumi Nazmir ya gaji sosai. Koda ya fuskanci cewa Luzaiya tayi bacci sai ya isa gaban wata bishiya ya sauketa a hankali. Har ya miƙe zai tafi neman itatuwan da zai kunna su ji ɗumi sakamakon hunturun sanyin dake kaɗawa a jejin,sai ya tsaya yayi gajeran tunani,don haka sai ya fiddo wata igiya daga cikin jakarsa ya ɗaure ƙafafun Luzaiya sannan ya kwantar da ita ta yi rub da ciki, ya ɗaure hannayenta ta baya don kar ta gudu. Sannan ya tafi neman itatuwan. Bayan kamar daƙiƙa dari da ashirin da tafiyar jarumi Nazmir sai sanyi ya bugi gimbiya Luzaiya ta farka daga barcin. Ai kuwa tana buɗe idanunta,sai tayi arba da wata mayunwaciyar kura nesa can daga inda take. Ita dai wannan kura wannan rana ta yini da yunwa domin ta gaji da neman abin da zata ci ta rasa. Koda suka yi ido-da-ido sai kuran nan ta taso a guje haikan don rashin haƙuri ma har tsalle take sama tana kara dirga gaba don gani take gudun bai isheta ba. Koda Luzaiya ta yunƙura don ga miƙe tsaye ta gudu sai ta ji ƙafafunta da hannayenta a ɗaure. Nan take hankalinta ya dugunzuma jikinta ya kama karkarwa don tsananin tsoro ba ta san sa'adda ta ƙwala uban ihu ba. A wannan lokaci jarumi Nazmir ya deɓo kayan itatuwa niƙi-niƙi. Koda ya jiyo ihun gimbiya Luzaiya sai ya yi watsi da itatuwan ya kece da tsananin gudu ya nufi inda ya baro ta. Gudu yake iya ƙarfinsa kuma irin wanda bai taɓa yi ba a rayuwarsa. Har yanzu bai daina jiyo ihun gimbiya Luzaiya ba,al'amarin daya ƙara fusata shi kenan ya ƙara ƙaimi. Kafin ya iso tuni kuran nan tayi tsalle sama ta dira gaban Luzaiya. Nan take kuwa ta kaiwa gadon bayanta cafka da hakoran bakinta. Cikin zafin nama Luzaiya ta mirgina baya amma duk da haka sai da haƙoran kurar suka yage rigar Luzaiya kuma suka karce fatarta jini ya tsatstsafo. Kurar ta sake kai mata cafka a karo na biyu bisa rashin sa'a sai ta faɗa hannun jarumi Nazmir ya shaƙe wuyanta,suka kama kokawa, su faɗi nan su tashi can. A lokacin ne gimbiya Luzaiya ta zuba musu idanu kawai zuciyarta cike da tunani kuma hawaye na zuba a idanunta tace a ranta, "Wai shin mene ne ma dalilin da ya sa na tsorata da wannan kura? Ashe bani ce wadda ke neman mutuwa ba? Ya akai na kasance mai ƙoƙarin neman tsira? Haba Luzaiya me kike so ki yi a duniya alhalin baki da kowa,ba ki da komai. Haƙiƙa kin yi kuskure da kika yi ihu har jarumi Nazmir ya kawo miki ɗauki da wuri. In da kin yi shiru da yanzu haka kin mutu kin huta da takaicin duniya.' Tun da jarumi Nazmir yake bai taba haɗuwa da ƙatuwar kura irin wannan ba,a duk lokutan da ya sha arangama a jeji a yayin farautarsa. Ita dai wannan kura ta kasance mai taurin kai,ƙarfi da jajircewa. Sai da suka shafe kusan rabin sa'a suna gumurzu ya zamana tayi masa rauni sosai da faratan hannunta amma da zarar ta kawo masa cizo sai ya goce ya naushi bakin nata. Saboda ƙarfin naushin nasa sai kaga ta zube ƙasa rikica amma kuma sai ta sake miƙewa cikin zafin nama,ta afka masa. Yayin da jarumi Nazmir ya ga kurar nan tana so ta galabaitar dashi sai ya harzuƙa zuciyarsa ta yi baƙinƙirin kawai sai ya suri ƙafafunta biyu na baya ya dagata sama ya rinka haji-jiya da ita tamkar wanda yake wasa da majajjawa. Bayan ya wulwulata kamar sau arba'in a sama sai ya rinka rotsa kanta akan wani dutse har saida ya ga kan ya dagwargwaje sannan ya yi jifa da gawar kurar,shima ya tsugunna ƙasa yana haki da numfashi. A sannan ne suka haɗa idanu shi da gimbiya Luzaiya. Koda ya ga raunin da kurar nan ta yi mata a gadon baya sai tausayinta ya kama shi. Cikin sauri ya miƙe ya je ya buɗe jakarsa ya ɗauko magani ya shashshafa mata a raunin,sannan ya kwance igiyar da ya ɗaure mata hannaye da ƙafafu,ya jinginar da ita a jikin bishiya. Kawai sai ya juya mata baya yace, "Idan kin so kina iya yin ƙoƙarin guduwa amma ki sani ba za ki iya tsere mini ba,a cikin jejin nan,duk inda kika shiga kika ɓuya sai na laluboki." Yana gama faɗin hakan ya tafi ya barta a wajen cikin tunani. "Me kike jira ne ga dama ta samu? Walau ki gudu ko kuma ki sami wani icen ki tsire cikinki ki mutu. Ko kya huta da baƙin cikin rayuwa." Zuciyar Luzaiya ce ta saƙa mata waɗannan maganganu. "Me yasa na rayu har na kawo i yanzu? Lallai akwai wani dalili a ƙarƙashin wannan sanadi. Zai fi kyau na tsahirta dan naga wannan dalili da idanuna tunda dai nayi iyakar ƙoƙarina akan na ga na halaka kaina,amma abu ya faskara. Duk da kasancewar ban yi imani da ɗaya daga cikin irin addinan zamani ba babu mamaki wani Ubangijin ne yake tsara rayuwata saboda wani ɓoyayyen dalilin." Luzaiya na cikin wannan tunani ne jarumi Nazmir ya dawo ɗauke da itatuwa. Shi kansa yayi mamaki da ya iske ta har yanzu a zaune a inda ya barta,kuma hawaye bai daina zuba a idanunta ba. Ban da karkarwar ɗari babu abinda take yi. Nan da nan ya zube icen a gabanta ya kunna musu wuta,sannan ya sake buɗe jakarsa ya fiddo wata riga wadda aka yi ta fatar damisa ya lulluɓawa gimbiya Luzaiya. Shi kuwa dogon wando ne kaɗai a jikinsa na fatar zaki. Nazmir ya zauna tsallaken wutar suna masu fuskantar juna. Tsawon daƙiƙa biyar wurin yayi tsit baka jin komai face kukan tsuntsaye da kuma kukan manyan namun dawa,da ke can nesa. Nazmir ya katse shirun da cewa, "Me yasa ba ki yi ƙoƙarin guduwa ba sa'adda na kwance ki na tafi nemo itatuwa?" Ba tare da ta ɗago kai ta dube shi ba,tace, "Guduwa ta ba ta da wani amfani ko tasiri,domin na rigaya nayi kusure tunda har na yi ihu ka kawo mini agaji sa'adda kura ta afka mini." Nazmir ya yi ɗan guntun murmushi sannan ya janyo maganin nan da ya shafa mata a rauni ya fara shafawa a nasa raunikan. "Bai kamata ki yi ƙoƙarin kashe kanki ba,saboda baƙin cikin rashin mahaifinki,mulkinki da danginki,ki tuna cewa mai rai baya fitar da rabo,za ki iya sake saduwa da mahaifiyarki nan gaba,shin ba kya tunanin irin ɓacin ran da mahaifiyarki zata shiga idan ta sami labarin mutuwarki,ki sani cewa idan na kai ki ga sarkina ya aureki zaki ci gaba da rayuwa ne cikin tsananin jin daɗi da walwala." Koda jin haka sai ta dubi jarumi Nazmir cikin ƙunar zuci tace, "Shin jin daɗi da walwala zasu iya maishe da gurbin abokanka waɗanda ka rasa a wannan yaki da ka yi?" Koda jin wannan tambaya sai idanun Nazmir suka ciko da ƙwalla,jikinsa yayi sanyi gaba ɗaya ya kasa cewa komai. Luzaiya ta ci gaba da cewa, "Babu wani farin ciki da zai iya gusar mini da đacin zuciyar da nake ji sakamakon kisan gillar da kuka yiwa mahaifina. Ka yi sani cewa a duk sa'adda na dubi abokinka na kan ji kamar ana sukan zuciyata da tsinin masu. Inda zan kashe shi na yi gunduwa-gunduwa da sassan jikinsa izuwa sala-sala,mini-mini yadda tsuntsun kanari zai iya tsinta da bakinsa ya ci ba zan huce takaicin zuciyata ba. Bani da wani masoyi a duniya wanda yafi ubana. Na rayu a cikin ƙaunarsa,da begensa dare da rana,kuma cikinta zan mutu." Sa'adda Luzaiya tazo nan a zancenta sai ta fashe da kuka. Tausayi ya kara turnuke Nazmir yace, "Na san har abada ba za ki iya yi mana afuwa ba,wato ni da abokaina amma ki sani bamu kashe mahaifinki don buƙatar kanmu ba sai don mu ceto rayuwarmu da kuma farin cikin iyayenmu. Kowanne 'ɗa' na gari ba shi da wani buri wanda yafi na nunawa iyayensa tsantsar ƙauna kamar yadda suka nuna masa tun yana ƙarami kawo izuwa girmansa. Tsantsar ƙaunar da nake yiwa mahaifina ce tasa na fito wannan yaƙi,amma ba wai don tsoro da bin umarnin sarkina ba. Hasalima a duniya babu mutumin dana tsana fiye da sarkin garinmu saboda zaluncinsa da rashin tausayinsa ga talakawa." Koda gimbiya Luzaiya ta ji wannan batu daga bakin jarumi Nazmir sai ta cika da mamaki tayi shiru ba ta ce komai ba. Daga can kuma sai ta dube shi tace, "Ya kai wannan jarumi ina son nayi maka wata tambaya idan har ba za ka sami damuwa ba?" Nazmir yace, "Faɗi tambayarki in dai ina da amsarta zan sanar da ke." "Shin za ka iya gaya mini dalilin da ya sa mahaifina yace idan ya bari aka kashe ku ya ci amana? Mene ne dalilin da ya sa ya kawo kansa gareku har ya umarce ka da ka sare kansa kuma ka kamani ka tafi da ni? Kayi sani cewa zuciyata ta daɗe tana damuwar akan wannan al'amari,kuma ta shiga cikin bakin duhu babu mai fito da ita izuwa cikin hasken fahimta face kai." Sa'adda gimbiya Luzaiya ta zo nan a zancenta sai jarumi Nazmir ya yi ajiyar zuciya yace, "Ba komai ne ya sa mahaifinki ya yi haka ba sai don ya sakawa mahaifina abin da alherin da ya taɓa yi masa a baya kimanin shekaru da suka gabata." Nan take jarumi Nazmir ya kwashe labarin abinda ya
Chapter 3 · 0% Book details