Sashe 4
Nihad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
faru tsakanin sadauki Halufa da sarki Fahalul Bahafus ya zaiyane mata. Koda ya ƙare labarin sai ta fashe da kuka tana mai cewa, "Haƙiƙa mahaifinka masoyi ne a gareni da mahaifina lallai kai ba abokin gabata bane,domin ba don darajar mahaifinka ba da na girma a cikin maraici. Haƙiƙa mahaifina ya riƙe amana kuma ya tabbatar da alƙawari. Ya kai Nazmir kayi sani cewa daga yau na rungumi ƙaddara,kuma zan kasance mai bin umarninka har mu isa ƙasarku ka danƙani a hannun sarkinku,domin yin hakan a gareni shi ne cikar riƙe amanar da ke tsakanin mahaifina da mahaifinka. Lallai kun yi halacci a garemu,lokaci yayi da zamu saka muku,ina mai roƙonka da ka yafe mini kura-kuran da na yi maka a baya." Nazmir yayi murmushi yace, "Ai duk abin da kika yi mini banga laifin ki ba,domin kin yi ne don sanin martabar mahaifinki." Haka dai Nazmir da gimbiya Luzaiya suka ci gaba da hira har dare ya raba sosai,ya umarce ta da yin barci,shi kuma yayi gadin lafiyarsu. Koda jin haka sai ta miƙe tsam ta dawo inda yake ta kwanta tana mai ɗora kanta akan cinyarsa tace, "Yanzu hankalina ya kwanta da kai na san cewa har abada ba zaka cutar da ni ba,domin kai masoyi ne ba maƙiyi ba." A iya rayuwar jarumi Nazmir mace ba ta taɓa kusantar sa ba,irin yau sai dai a larura ko a wajen yaƙi. Don haka lokacin da gimbiya Luzaiya ta ɗora kanta akan cinyarsa,sai gaba ɗayan tsigar jikinsa ta tashi,ya ji kamar ya ture ta,amma da ya tuna cewar 'yar sarki ce fa mai mulki,kuma wadda ke cikin baƙin cikin rayuwa mai matuƙar buƙatar nutsuwa da kwanciyar hankali sai ya ƙyaleta. Yayin da asuba ta fara gabatowa sai Luzaiya ta farka daga barci ta roƙi Nazmir da ya kwanta don shi ma ya dan rintsa. Nazmir yace, "Ai gari ya kusan wayewa don haka kaima sai ka kwanta ba." Nan fa gardama ta ƙarke a tsakaninsu da ƙyar ta shawo kansa ya amince ya kwanta,ita kuma ta ci gaba da tsaron lafiyarsu. Luzaiya bata tashi Nazmir daga bacci ba sai da ta gari ya waye sosai,rana ta ƙwale. Koda farkawarsa kuwa yaga ashe gari ya daɗe da wayewa sai ya dubi Luzaiya yace, "Ya gimbiya me ya sa kika barni ina ta barci har tsawon lokaci haka?" Yayin da Luzaiya ta ji wannan tambaya sai tayi murmushi tace, "Saboda kaima ka bani dama na samu isasshen barci,kuma nasan cewa akwai bashin barci mai yawa a tare da kai,idan ba ka yi ba zaka iya samun matsala a lafiyar ka." Wannan batu ba ƙaramin bashi mamaki ya yi ba,domin shi a tunaninsa bai ga dalilin da zai sa ta damu da lafiyarsa ba. Nazmir ya miƙe tsaye ya ɗauki kwari da bakansa da kuma takobinsa ya gyara musu zama a jikinsa. Koda ganin haka sai Luzaiya ta dube shi cikin damuwa tace, "Ina kuma zaka je?" Nazmir ya maida mata murmushi yace, "Zan je ne nayi farautar abin kalaci." "Ai kuwa sai dai mu tafi tare, don ba zan yarda ka barni ni kaɗai ba a wannan mugun dajin." Wannan batu ba ƙaramin mamaki ya baiwa jarumi Nazmir ba,domin a tunaninsa Luzaiya bata kasance matsoraciya ba,in da kuwa matsoraciya ce ai ba za ta hau doki ba,ta yiwa mayaƙa jagora a lokacin nan da ake gumurzun yaƙi tsakanin su Nazmir da baraden mahaifinta. Jarumi Nazmir ya dubi gimbiya Luzaiya ya ƙyalƙyale da dariya yace, "Haba ranki ya daɗe ai ni zatona ke jaruma ce daga cikin mata,ya kuma kike nuna gazawarki a fili haka?" Luzaiya tayi murmushi tace, "Ai ido ba mudu bane,amma ya san ƙima. Tabbas ko kaɗan ban yi kama da jaruma ba,haka kuma ba ni da sura irinta jarumai." Ba tare da ɓata wani lokaci ba jarumi Nazmir ya nausa cikin jeji yana mai sauri-sauri, gudu-gudu. Luzaiya ta bishi a baya duk in da ya ɗauke sawunsa sai tasa na ta,ko kaɗan bata yarda ya bata tazara ba. Suna cikin dube-dube ne a jejin Nazmir ya hango wata barewa. Ai kuwa yana ganinta ya ɗana baka akan kwari ya sai tata. Koda ya saki bakar sai barewar ta ruga cikin dawa,kibiyar ta wuce ta saman kanta. Koda ganin haka sai Nazmir ya bi barewar da gudu,itama Luzaiya sai ta bi shi a guje iya ƙarfinta,don kada ya ɓace mata. Sai da suka shafe kusan rabin sa'a suna wannan gudu basu cimma barewar ba,ita kuma barewar bata ɓace musu ba. Ya zamana Luzaiya ta jigata ainun sai haki take,kuma tana sassarfa kamar za ta fadi ƙasa,amma sai ta jure. Koda suka iso kan wani ƙaton dutse sai barewar nan ta fara ƙoƙarin isa karshen dutsen. Anan ne jarumi Nazmir ya tsaya ya zaro kibiya guda ɗaya daga cikin kuttun kibbau ya aza akan bakar, sannan ya ja ya taɓe yana mai saita barewar nan. Yayin da ya gama taɓewa da saitawa iya ƙarfinsa da iyawarsa sai ya saki kibiyar. Cikin tsananin gudu da ƙarfi kibiyar ta tafi ta caki gadon bayan barewar ta faso ta cikinta ta ɓulla waje. Take barewar nan ta fadi ƙasa matacciya. A sannan ne Nazmir ya waiga bayansa ya yi arba da gimbiya Luzaiya wacce ta zauna dirshan tana kallon abin da ke faruwa cikin nuna al'ajabi. Nazmir yayi murmushi a gareta, itama ta yi masa fuskarta na nuna yabawa bisa jarumtakarsa. Kawai sai Nazmir ya nufi inda wannan barewa ke kwance da nufin ya ɗaukota. Ba zato ba tsammani sai ya gansu suna saukowa ƙasa daga saman wannan dutse. Ba wasu ba ne face Bardil,Bagwan da kuma sauran baradan nan abokan tafiyarsa. Koda su Bardil suka yi arba da jarumi Nazmir,kuma suka ga gimbiya Luzaiya a bayansa sai suka cika da tsananin farin ciki. Nan take suka rugo gare shi shima ya ruga garesu take aka rungume juna,cikin murna mara misaltuwa. Ba tare da ɓata wani lokaci ba aka ɗauko barewar nan aka sauko daga kan dutsen. Nan dai aka gasa barewa kowa ya yi kalaci,sannan aka shiga hira inda jarumi Nazmir ya baiwa su Bardil labarin abubuwan da suka faru bayan rabuwarsu. Al'amarin da ya ƙara jefa su cikin matuƙar al'ajabi kenan. Bayan nan sai Bagwan ya yi gyaran murya yace, "Yakai abokina kayi sani cewa bayan rabuwarmu daku muma mun sha baƙar wahala sakamakon gamuwa da muggan namun jeji da kuma nau'i-nau'in 'yan fashi,amma duk sai da muka fatattake su muka tarwatsa su. A haƙiƙanin gaskiya bamu taɓa tsammanin zamu sake saduwa da ku ba,domin mun zata kai da ita duk kun hallaka a lokacin da kuka faɗo ƙarƙashin tsaunin nan mai kwazazzabo. Tuni mun yankewa kanmu hukunci cewar ba zamu koma can ƙasar mu ba,muddin bamu ganku ba sai dai mu ci gaba da rayuwa a cikin jejin nan har ajalin mu ya riskemu, domin mun san cewa idan muka koma ba tare da biyan buƙatar sarki ba gaba ɗayanmu mun zama gawa." Koda jarumi Nazmir ya ji wannan jawabi sai yayi ajiyar zuciya,sannan ya dubi Bardil da Bagwan yace, "Ya ku abokaina ku yi sani cewa tabbas na ji a jikina cewa ɗayanmu ba zai sake mutuwa ba,har sai mun isa gida lafiya,tare da biyan buƙatar sarki sai dai baƙin cikin rabuwa da abokanmu shi ne babban abin damuwarmu." Yayin da jarumi Nazmir ya fadi haka sai idanun Bardil da Bagwan suka ciko da ƙwalla suka kama kuka,shima sai ya taya su. Al'amarin da ya sa gimbiya Luzaiya ma ta tuno da mahaifinta,mahaifiyarta da kuma ƙasarsu kenan. Itama dai bata san sa'adda ta fara zubar da hawaye ba,don haka sai ta miƙe ta koma gefe guda ta zauna ta ci gaba da kukanta. Su kuwa sauran barada sai suka kamu da tausayi suka yi shiru da zugum cikin juyayi. Nazmir ya kama hannun Bardil da Bagwan ya jasu izuwa gefe guda suka keɓe,sannan ya dube su ɗaya bayan ɗaya sa'adda yake goge hawayen idanunsa, yace, "Yaku abokaina ku yi sani cewa jikina yayi sanyi,haka kuma zuciyata na bugawa ma'ana ina jin tsoro da faɗuwar gaba bisa abin da zai faru garemu bayan mun isa gida. Jikina yana bani cewar akwai wani mugun abu da zai faru a garemu dangane da sakaiyar azzalumin sarkinmu zai yi mana domin halinsa ne ya cutar da talakawansa waɗanda suka kyautata a gare shi." Yayin da Bardil da Bagwan suka ji wannan batu sai duk hankalinsu ya tashi suka shiga tunani. Nazmir ya katse tunanin nasu da cewa, ni kam a yanzu tausayin gimbiya Luzaiya ya shigeni har ina jin cewa kamar bazan iya danƙata ba a hannun azzalumin sarkinmu, to amma fa idan nayi tunani sai na ga cewa ba mu wata mafita don haka dole ne na miƙata in ba haka ba kuwa rayuwarmu da ta iyayenmu na cikin haɗari. Yanzu ku mece ce shawararku bisa abin da kuke ganin zai fishshe mu?" Lokacin da Bardil da Bagwan suka ji wannan tambaya sai hankalinsu ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe duk suka yi shiru suna juya al'amarin cikin zukatansu. Bayan dogon nazari sai Bardil ya ɗago kai ya dubi jarumi Nazmir yace, "Ya kai abokina haƙiƙa maganarka abin dubawa ce matuƙa,to amma ka yi sani cewa yanke hukunci a garemu yanzu yafi komai haɗari. Ni a tunanina zai fi kyau mu bari mu isa gida in ya so sai mu yanke shawara bayan mun miƙa gimbiya ga sarki." Koda jin haka sai Bagwan yace, "Ƙwarai kuwa wannan shine abin da yafi cancanta a garemu." Da wannan shawara aka yi amfani. Wato daga wannan rana su jarumi Nazmir suka ci gaba da tafiya ba dare ba rana,sai dai kawai idan sun gaji su yada zango. Bayan wata da watanni ne suka iso ƙasarsu. Yayin da suka iso bayan gari dare ya raba,don haka sai suka tsaya suna shawarwari akan shiga gari yanzu ko kuwa su bari sai gari ya waye? Koda mahawara tayi yawa a tsakaninsu sai jarumi Nazmir yace, "Wai shin wane ne shugaba a cikin tafiyar nan tamu?" Bardil da Bagwan suka ce, "Kai ne shugaba ya jarumin jarumai." Nazmir yayi murmushi yace, "Tunda haka ne ni yanzu nake son mu shiga cikin garin,kuma ba zamu shiga ba sai mun ɓatar da kamanninmu domin mu san sirrin abin da gari ke ciki,don kada mu faɗa cikin tarkon sarki. Kamar yadda