Sashe 20
Nihad Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
********
Lokacin da sarki Dujalu ya zo daidai nan a labarinsa sai wata baƙar kyanwa ta shigo cikin fadar a guje ta nufi inda karagar sarki take.
Koda
ganin kyanwar sai sarki Dujalu ya miƙe zumbur cikin firgita,saura ƙiris yayi abin kunya ya ruga da gudu.
Kawai sai tsoho Rafkanagu ya cafke magen ya jefa ta cikin bakinsa ya tauneta da ranta ya haÉ—iye.
Al'amarin da yayi matuƙar razana sarki da sauran 'yan majalisarsa kenan,domin basu taɓa ganin mutumin da ya cinye mage da ranta ba,sai yau.
Nan fa kowa ya sha jinin jikinsa aka fara tunanin anya kuwa wannan tsohon mutum ne.
Rafkanagu yayi gyatsa sannan ya dubi sarki Dujalu cikin murmusi yace,
"Ranka ya daɗe ai sai ka cigaba da bamu wannan labari don mu ji yadda ƙarshen wannan Hikaya ta bokanya Tazibul Luhucul zata kasance."
Cikin alamun rashin yadda sarki Dujalu ya dubi tsoho Rafkanagu yace,
"Kai ba za ta yiyu ba.
Kowa ya tashi ya bani wuri,ba zan cigaba da wannan labari ba
har sai na yi bincike akan wannan baƙuwar mage data shigo cikin fadata tana ƙoƙarin hallakani,kuma sai na yi bincike akan ka kai wannantsohon,tabbas kaima ban yarda da kaiba."
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin su Ruziyal da sarki Dujalu yayin da yake basu labarin Hikaya ta huɗu wacce itace ta ƙarshe sai
dai su tafi wani garin neman sauran labarai don hada rubutun sabon KUNDIN TSATSUBA.
Al'amarin su Jafar kuwa bayan ƙatuwar macijiyar nan ta haɗiye su sai kawai suka ga an jefo su cikin ainihin ta su duniyar ta cikin KUNDIN TSATSUBA aka watsar da su a gaban littafin kundi,har yanzu shafi na goma sha shida ne a buɗe.
Mazalish ta dubi Jafar,Gulzum, Yelisa da Mashrila tace,
"To fa mun gamu da bala'i mara sauƙi da ƙarshe zai fi kyau mu hanzarta ganin ƙarshen sa don mu huta da tararrabi."
Cikin fushi da tsawa Yelisa tace,
"Amma dai ke kin cika mahaukaciya.
Ai da mu kai kanmu cikin bala'i gwara shi bala'in yazo ya same mu da kansa."
Caraf Jafar ya ansa yace, "Haba Yelisa ai Mashrila ta fiki gaskiya me zamu tsaya jira kawai a cigaba da karɓar sakamako tunda dai mu da kanmu muka ɓaro wannan aiki."
Gulzum ya dakawa Jafar harara yace,
"Tabbas ka cika wawa,sususu.
To bamu yarda wani ya buÉ—e shafin gaba ba.
Kawai bari ya buÉ—e kansa."
Nan fa aka hargitse da kace-nace.
Ba su ankara ba har lokaci yayi kundi ya buÉ—e kansa,
izuwa shafi na sha bakwai,sai ga hoton ƙatuwar macijiyar nan,kuma babu rubutun komai a jikin shafin.
Nan take iskar kundi ta zuƙe su suka faɗa ciki.
Sai tsintar kansu suka yi gaban macijiyar a wata duniya dabam,kafin su yi wani yunƙuri tuni macijiyar ta wangame ƙaton bakinta ta haɗiye su gaba ɗaya.
Haka dai su Jafar suka dunga shiga cikin masifu iri-iri har guda dubu,kuma duk guguwar nan ce ta rinƙa kai su cikin masifun.
A cikin shafi na ashirin ne na KUNDIN TSATSUBA suka rabu da wannan guguwar bala'i bata sake É—aukar su ta kai su wani wuri ba.
Bayan an watso su cikin duniyar su ne suka sami hutun daƙiƙa ɗari da ashirin,sannan KUNDIN TSATSUBA ya buɗe kansa izuwa shafi na ashirin da ɗaya suka yi arba da hoton wata duniyar da ke sararin samaniya.
SHIN GIMBIYA SIMA ZATA TSIRE JARUMI HUBAIRU DA WANNAN MASHI WANDA SARKI LU'UMANU YA BATA?
SHIN SARKI DUJALU ZAI ƘARASA LABARIN HIKAYAR BOKANYA TAZIBUL LUHUCUL?
YAUSHE NE SHAMHARU ZAI ZAMA MATSATSUBI?
INA LABARIN SU MARKAHUL SABUS WAÆŠANDA SHAMHARU YA MAIDA SU 'YAN MINI-MINI YA JEFA A ALJIHUN RIGARSA?
ME SU JAFAR ZA SU GANI A CIKIN WANNAN DUNIYA DAKE SARARIN SAMANIYA?
Mu haÉ—u a MATSATSUBI 3.