← Book details Nihad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 20

Sashe 15

Nihad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin sarki Usman da 'yarsa gimbiya Fauwaza kyakkyawar budurwar da babu kamarta a duk faɗin duniya a wannan zamani a cikin birnin Misra. Al'amarin bokanya Tazibul Luhucul,aljana Saubatu Azwas da hadimai talatin da bakwai kuwa kafin su rabu kaso biyu don tafiya aiwatar da wannan mummunan aiki dake gabansu saida süka tsaya suka tattauna gami da yin shawara bisa inda ya kamata su fara zuwa. Tazibul Luhucul ce ta fara magana yayin data dubi Saubatul Azwas tace, "Yake ƙawata ina son ki sani cewa sarkin Misra da sarkin Hindu dana Farisa sune mafiya jajurcewa akan yawaita bauta da ibada,don gudun kada su ɓata mana lokaci zai fi kyau mu fara zuwa kasar Rum da Ƙisra don aiwatar da wannan aiki in yaso daga baya sai mu je Misra,Hindu da Farisan." Koda jin haka sai Saubatul Azwas ta ƙyalƙyale da dariya tace, "Yake ƙawata haƙiƙa maganarki gaskiya ce,don haka ni yanzu zan kwashi rabin hadimanki mu tafi kasar Rum ke kuma sai ki kwashi rabin ku tafi kasar Ƙisra." Tazibul Luhucul tace, "Ƙwarai kuwa wannan shawara tayi kyau,kuma koda na haɗu da wata matsala zan neme ki a cikin madubin tsafina na sanar dake don ki kawo mini đauki." Saubatul Azwas ta sake ƙyalƙyalewa da dariya a karo na biyu tace, "Wannan ba matsala ba ce." Ba tare da ɓata wani lokaci ba Saubatul Azwas da bokanya Tazibul Lubucul,suka kwashi hadiman nan suka kasu gida biyu. Saubatul Azwas ta nufî ƙasar Rum,ita kuwa Tazibul Luhucul ta nufi kasar Ƙisra. Lokacin da bokanya Tazibul Luhucul tare da rabin hadiman ta suka nufi ƙasar Ƙisra basu fi sa'a uku da rabi ba suna tafiyarsu suka iso bayan birnin. A daidai wannan lokaci ne rana ta faɗi,wato Magariba ta doso kai. Tazibul Luhucul ta ciji yatsanta,sannan ta dubi hadimanta cikin alamun takaici tace, "Kash babu damar mu shiga cikin wannan birni yanzu dole ne mu tsaya anan har dare ya raba." Koda jin haka sai wata hadima mai suna Lulaija tace, "Ya shugabata mene ne hikimar hakan?" Cikin fushi da harara Tazibul Luhucul ta dubi Lulaija tace, "Amma dai duk yadda aka yi ƙwaƙwalwar ki ta kifi ce,mara basira da mantuwar tsiya. Ashe har kin manta da bayanin da mai girma Saubatul Azwas ta yi mana kenan cewar lallai ba zamu ziyarci sarakunan nan ba sai da tsakar dare,kuma kada mu kusance su yayin da suke aikin bauta ko tsafi." Lulaija ta duƙar da kai tace, "Ki gafarce ni ya shugabata haƙiƙa zancenki dutse ne,lallai na sha'afa." Kafin Lulaija ta gama faɗin haka tuni Tazibul Luhucul ta nuna gaba ɗayan hadiman da sandar tsafinta har dama ita kanta. Ai kuwa nan take suka bace ɓat,a lokaci guda tamkar dama can babu su a wurin. Bayan kamar rabin sa'a sai Tazibul Luhucul ta murza sandar tsafin nata suka sake bayyana gaba ɗaya a wajen. Bayyanarsu ke da wuya Lulaija ta rusina a gaban Tazibul Luhucul cikin alamun girmamawa tace, "Ya shugabata mene ne ya faru kika ɓoyemu gaba daya?" Tazibul Luhucul tayi murmushi, tace, "Ba komai ba ne ya sa na ɓatar damu ba face na jiyo ƙamshin aikin bokayen garin nan suna son su san da zuwanmu. Abin da ba su fahimta ba shine wanda duk ya riga ka kwana,dole ne ya riga ka tashi." Cikin alamun mamaki Lulaija tace, "To saboda me suke son su san zuwanmu?" Tazibul Luhucul tace, "Saboda su san matakin da zasu ɗauka wajen hanamu aiwatar da abin da ya kawo mu. Na rantse da ƙarfin tsafina yanzu ba su isa su ganmu ba,ko su ji muryarmu,domin na tsafance mu mu da ƙarfin sihirin tsafina. Kowannen ku ya zauna cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,da zarar dare ya raba zan baku izini ku tafi izuwa gidajen 'yan majalisar garin nan ku barbaɗa musu hodar tsafin nan wacce zamo sanadiyar kamuwarsu da cutar ajali." Kamar yadda Tazibul Luhucul tayi wannan batu haka al'amarin ya kasance,wato basu shiga cikin birnin Ƙisra ba,sai da dare ya raba tsakiya. Hadiman na ta suka kasu gida goma,suka tafi izuwa gidajen 'yan majalisar. Cikin sa'a kuwa duk gidan da suka je sai su iske maigidan na kwance yana ta sharar barci. Nan take sai su watsa masa wannan hodar tsafi,su wuce gaba. Gida ɗaya ne suka sami matsala,wannan gida kuwa na wazirin garin ne,shi dai wannan waziri ya kasance yayan bokan birnin wanda ake kira Garfas. Boka Garfas ya sanar da waziri cewa idan har ya daina barci a cikin dareren wannan shekara to tabbas wannan sihiri na cutar ajali ba zai hau kansa ba. A bisa wannan dalili ne ya sauya lokacin barcinsa gaba ɗaya,ma'ana ya daina yin barci da daddare sai dai da rana. Lokacin da hadimai suka zo gidan waziri sai suka iske shi a zaune yana ta aikin bautar gunkin da suke bautawa mai suna Gulmakuru. Koda suka riskeshi a cikin wannan hali sai suka ja da baya da sauri suka koma bayan katangar gidan suka zauna,suna haki da dafe ƙirazansu,cikin yanayin tsoro da tashin hankali. Daga can sai Lulaija tace, "Kai amma fa wannan shegen waziri da nacin tsiya yake,lallai ku sani cewa mun tsallake rijiya da baya,ba don mun yi sauri mun koma da baya ba da tuni gaba dayanmu mun zama gumaka. In kuwa muka zama gumakan babu wanda ya isa ya dawo damu ainihin halittarmu,shi kenan tamu ta ƙare." Yayin da Lulaija ta zo nan a zancenta,sai wata hadimar mai suna Kamtura tace, "Tabɗijam ai kuwa in dai haka ne babu wawaye a duniyar nan kamarmu yanzu saboda tsananin kwaɗayin abin duniya muka jefa kanmu cikin irin wannan mugun aiki,mai mugun haɗari?" Lulaija tace, "Eh, to haka ne,amma ai kin san cewa faɗan da yafi ƙarfinka dole ne ka mayar da shi wasa. Duk mun sani cewa ko muna so,ko bama so dole ne mu zama bayin Tazibul Luhucul,in kuwa muka ƙi bin umarninta hallaka mu za ta yi." "Kunga yanzu dai ba hira ce mafitarmu bà yaya zamu ɓullowa wannan shegen wazirin mai naci. Kun sani cewa idan fa lokacin da aka ɗiba mana ya cika dole ne mu bar wajen nan,kuma idan muka tafi ba tare da samun biyan buƙata ba gawa ma sai ta fi mu jin daɗi da kwanciyar hankali." Wata hadima ce mai suna Faltu,tayi wannan furuci. Gaba ɗayansu suka yi shiru suna tunani aka rasa wanda zai ce wani abu tsawon daƙiƙa sittin. Gaba ɗayan waɗannan hadimai su goma sha bakwai ne,amma namiji ɗaya ne tak a cikinsu,ana kiransa da suna Murkubalu. Cikin alamun mamaki Murkubalu ya dubi waɗannan hadimai 'yan uwansa ɗaya bayan ɗaya yayi tsaki,sannan yace, "Amma dai kun bani mamaki a matsayinku na mata iyayen kaidi a ce kun kasa tunano hanyar da zamu hallakar da wannan mutum. To idan kun sallama mini ni zan faɗi abu ɗaya da za'a yi mu sami nasara." Koda jin haka sai Faltuz tace, "Ai dama ku maza kaidin ku yafi namu masifa,kawai dai ƙaurin suna muka fiku. Maza sanar damu dabarar da zamu yi don mu hallakar da wannan basarake cikin ƙanƙanin lokaci." Murkubalu ya yi murmushi, sannan kuma ya ƙyalƙyale da dariya har da doka ƙafarsa guda ƙasa,yana mai yiwa kansa kirari da cewar, "Nine Murkubulu tsuliyar dodo, kuna nine baƙin annamimi uban munafukai. Nine sharri kayan kwalba,kakan mugayen aljanu,masu baƙar zuciya da mugun nufi da baƙin tanadi." Murkubalu ya ci gaba da cewa, "Abin da za'a yi shi ne,wace ce tafi kowa rashin tsoro a cikinku?" Nan da nan su duka suka nuna Lulaija suka ce, "Gata nan kuma ita ce wawiya don an bata sandar girma akan hakan,kuma an tabbatar da cewa a cikin gaba ɗayan al'ummar aljanun garinsu babu mai iya sai da rai kamarta." Murkubalu yayi murmushi,a karo na uku yace, "Yauwa ke nake so ki juye kamanninki izuwa na matar wannan waziri,ki kasance cikin suturu mai shara-shara wato wadda ke nuna surar jikinki sai ki gifta ta gabansa,yayin da yake wannan aikin bauta na gunkinsa. Tabbas yana ganinki sha'awarsa zata motsa ya tashi ya bar bautar ya bi bayanki. Mu kuma sai mu yi amfani da wannan damar mu cim masa." Koda jin wannan batu sai Lulaija tace, "Tabɗijam amma kun zo mini da rainin hankali,to ku tsaya ku ji don fa an ce ni wawiya ce kuma bani da tsoro baya nufin cewa bana son na cigaba da rayuwa a duniya,shin ka mantane cewa an ce kada mu kusance su yayin da suke aikin bauta ko tsafi? Ko kuwa kana so ne na halaka a banza." Murkubalu yace, "Ai ba so nake ki halaka ba,kuma bana ce ki kusance shi ba,nesa da shi zaki gifta,buƙata dai kawai ya ga giftawar taki cikin wannan yanayi." Yayin da Lulaija ta ji haka sai tayi murmushi tace, "An gama." Kafin wani daga cikinsu ya ƙara cewa wani abu tuni ta ɓace ɓat,bata sake bayyana a ko'ina ba sai akan tagar turakar wannan waziri a matsayin tsuntsun kanari. A wannan lokaci waziri,ya tsugunna gaban gunkinsa bisa gwiwoyinsa yana bauta. Cikin hanzari tsuntsun kanarin ya sauko ƙasa ya tsaya ya zamana tsakaninsa da waziri ya kai taku arba'in. Kawai sai tsuntsun kanarin ya rikiɗa ya zama matar waziri wadda ta kasance ɗanyar budurwa mai tsananin kyawun fuska da kyawun surar jiki. Sanye take cikin wata irin doguwar riga mai launin shuɗi kuma shara-shara. Daga ƙasanta an yi mata beza da adon dutwatsen lu'ulu'u. Koda ta yi tafiya taku biyu sai ƙarar duwatsun lu'u lu'un suka janyo hankalin waziri ya ɗago da kansa da sauri don yaga komene ne. Ai kuwa sai ya yi arba da kyakkyawar matarsa tana mai bayyanar da surar jikinta kuma ta faɗa cikin ɗakin da sauri. Cikin kiɗemawa waziri ya miƙe zumbur har ma yana dungure gunkin nasa,wato abin bautar tasa. Gunkin ya tuntsure ya faɗi ƙasa,amma san bai lura ba. Kawai sai ya ɗaga ƙafarsa ya shallake gunkin ya nufi ƙofar ɗakin da matar tasa ta shiga. Har ya jefa ƙafarsa ta dama cikin ɗakin ya ɗago ta hagun kenan sai yaji wani irin abu ya shiga jikinsa gaba ɗaya,wanda ya haddasa sandarewar jijiyoyin jikinsa na tsagin ɓangaren hagu. Kawai sai ji yayi komai na rabin jikinsa ya daina aiki. Take ya yanke jiki ya faɗi ƙasa,yana mai kurma ihu. Al'amarin da ya janyo farkawar gaba ɗayan mutunen
Chapter 15 · 0% Book details