Sashe 32
Mutallab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
i da farincikin zuciyata, ku duka kuna da iyaye na tabbata ba za ku so rasa su a rayuwarku ba ka ji tausayina Please brother" "Ni ba brother naki bane ni an daba ne sunana Goje kin gane, idan kina bu atar wani abu kina iya bubbuga ofar" kafin Safiyyerh ta yi magana ya yi sauri rufo ofar ya fita. Ya je ya samu Moh a wajen gidan zaune ya sake tan washe afafuwansa ya kalle shi sosai kana ya ce "Scorpion" "Kana son fa ar sunan, zan manna maka hauka Goje zan ja maka ruwa". "Me ya sa baka son na dinga fa a ne? Ai dafinka ma ya fi na kunama ni ina son sunan" Moh ya yi shiru yana sake har e hannayensa duka biyun ya zubawa samaniyya idanu. "Idan zan nuna maka asalin kalata a Scorpion ba zaka auka ba, za ka daina ha a idanuwa dani sau in sunan na wajan fa a ne, ka kalle ni a Moh ko Mai dawa ok" "Yadda ka ce haka za a yi, ya zamu yi da yarinyar nan yanzu? Kwananta aya da wuni fa, kuma bata cin abinci" Cikin rashin fahimta Moh ke kallon Goje su yake ya tambaye shi wacce yarinyar bakinsa kuma ya yi masa nauyi ya dinga juya idanunsa akan fuskar Goje, fahimtar hakan ya saka shima Goje cewa "Manager wacce Ali wali ya saka mu akko yarinyar da muka je gidansu jiya" ha e fuska sosai Mai dawa ya yi idanunsa ya shige ciki haka kawai acin ransa ya sake ninkuwa ya yi shiru ya datse la ansa kamar zai raba su gida biyu ya yun ura zai tashi Goje ya ce "Wannan sauyin na yanzu na mene? Na fara jin da i a raina kwana biyu baka sha waya ba, lafiya dai?" "Mutallab" still ya yi shiru Goje ya sake kiran sunansa yana le a fuskarsa ganin babu alamar zai kula shi kawai ya mi e ya fice ya bar wajan. ***Gaba aya suna zaune a cikin parlon banda shi dake tsaye, zuwan nasan ake jira amma tunda ya shigo bai kalli kowa ba balle ya yi magana, fuskar nan a murtuke kamar kodayaushe. Yaya J, Awais Dr Hash, Anty Turai Waheeda sai Ummi dake zan gefe bata cewa komai sai goge hawayen da ya i tsaya mata take yi. Daddy baya uhm baya uhm'uhm kansa a asa zuciyarsa ta bugawa da arfi yama kasa yarda da abin da ake fa a har lokacin gani yake wasa ake yi masa da hankali da kuma wahalar da zuciyarsa da ake saboda anga yana aunar Safiyyerh auna mai tarin yawa an fahimci ita ce rauninsa. "Captain Aliyu Abdu Marafa shiru ba naka bane, ba muzo nan da a shiru ba a matsalar kidnapping ba a yi mana wasa" cewar Sp Ghali daya ara amsar case in Safiyyerh a karo na biyu ya aga kai ya kalli masu gadin asalin gidan da kuma na part in su Captain sai kuma ya ce "Heyy you man, mene sunanka da aikin da kake yi?" Cikin rawar murya ya ce "Sunana Isma'il ni mai gadi ne Yalla "Isma'il sanda abin ya faru arfe nawa ne? A daidai lokacin kana ina kuma?" "Ban san arfe nawa bane a lokacin don ban duba a gogo ba, sanda abin ya faru kuma ina bakin gate ne amma kafin nan na mi e na shiga ban aki kama ruwa wallahi gaskiya nake fa a maka Yalla "To na aryata ka ne? Kenan Isma'il bashi da sani akan wa anda suka shigo gidan ko? Da auke Safiyyerh?". "Duk abin da na ce maka na yi arya abu aya na sani fitowar su auke da ita, hannunsu ri e da makamai aya ya ce na bu e ko ya ola mini ciki na ji tsoro ha a sai na bu e ashe sun yi parking mota wata aka mai kyau daga can gefe" Murmushi kawai Sp Ghali ya yi yana duban aya ma'aikacin ya ce "Kai kuma fa? Mene information?" Shi wannan jikinsa har ari yake don tsoro ya ce "Yadda na gansu Allah Ya sa naga Annabin Rahama, misalin biyu da arba'in ne ina zaune na ji ana dirowa ta katanga kafin na yi magana aya ya make ni yana nuna yatsarsa a baki alamun na yi shiru, ni kuwa na yi shirun don wallahi a lokacin na auka mai gida shi sojan kenan daman shi ke kai wa dare a waje saboda yanayin aikin nasa, suka aure ni ina hango sanda suka nufi part in tunda can babu masu gadi daga nan ban san mene ya faru ciki ba sai gani mukai sun fito da ita a kafa a kamar ma a sume take yadda ta langwa ar da kai" Daddy da Captain suka runtse idanunsu lokaci aya, kowanne tunanin da yake daban a ransa, is he a loser? Captain ke tambayar kansa or he is falled as a husband maybe da yana kwana aki aya da Safii da hakan bai faru ba, idanunsa ya ara sauya kala. Daddy ma nasa tunanin dabanne, ko dai ya yi gaggawa ne ba yanzu ya dace ba? Ko mistake ya yi daya aurawa Aliyu Safiyyernsa ne? Is he a loser? Daya kasa tsare rayuwar yarinyarsa mace aya tilo a duniya ko dai da gaske he is falled as a father? Kafin kowa ya yi magana ta shigo cikin gidan a gigice duk da nutsuwar da take da ita, da sauri kuma Daddy ya mi e tsaye cike da tsoro da mamaki hatta Captain sai da ya ji wani abu mai kama da fa uwar gaba, who told her? Tun kafin ta yi magana daddy ya yi saurin matsawa kusa da ita ganin yadda take ta zare idanu fararen idanunta fuskar nan nata ya akko rana kamar ta yage don fari "Zahiyerh" Girgizawa daddy kai ta yi a daburce ta ce "Ina Maama?" Ya yi shiru yana arin ri e hannunta ta wace ta yi baya da arfi kuma ta ce "Ina Maama? Ka bani ita na tafi da ita where is Safiyyerh" "Safiyyerh has been kidnapped" "Kidnapped?" Ta maimaita tana juyawa ta kalli Sp Ghali anya ya san wacece ita da yake furta mata maganar anyi garkuwa da Safiyyerh kai tsaye bai tauna harshe ko ya lissafa maganar ba, Safiyyerh fa? Sp Ghali zai yi magana daddy ya girgiza masa kai yana sake kallon Zahiyerh wacce zuciyarsa ke bu ewa a duk sanda ya kalle ta. "Ummimi please ki kwantar da hankali ki samu nutsuwa tafiyar nesa kikai jirgi kika hau" "To na ji, ka fa a mini meke faruwa da Safiy yerh?" Daddy ya sauke numfashi a hankali kuma ya nuna Sp Ghali ya ce "As he said, he told you already Safiyyerh has been kidnapped" "Uhm" "Komai zai daidaita Ummimi" ita dai bata sake magana ba can ta aga kai ta kalli Aliyu da sauri ya zame idanunsa asa ta har e hannayenta a irji ta tsaya jikin hawa steps in bene. "Afuwa Sp muje ko?" "Next question in mu akan Captain ne" "Ok ka yi mana" in ji Anty Turai. "Aliyu kafa yi ha uri kalar aikin ku na sojoji daban, namu daban kowa da nasa iyawa da warewar a nasa angaren ok. Aliyu kai ne zaka fa a mana abin da ya faru a cikin gidan su waye suka sace maka mata har cikin gidanka a matsayinka na soja wanda kodayaushe zaka iya samun arin matsayi na aiki, ya akai haka ta faru? Su waye?" "Ban sani ba" Kai tsaye Captain ya bada amsa "Baka sani ba? Har kuma suka ji maka ciwo kada ka saka na fara zarginka na yi tunanin sace Safiyyerh set up ne kuma ne ka yi plans in hakan, ka sace matarka?" Aliyu ya dinga kallon Sp Ghali a hankali kuma ya ce "E". "kana nufin ka sace matarka Safiyyerh?" "E" ya sake cewa "Aliyu!!" Daddy ya kira Aliyu da arfi ya mi e ya ce "Da gaske ka sace Safiyyerh?" Kamar idanun Captain za su fa asa saboda yadda suka fito waje sai kawai ya lumshe ido ya bu e ya ce "E, na sace ta daddy" yana cewa ya fita daga parlon yana banko ofar da arfi kamar ya cire ta. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Muryar Ummi ta kara e parlon an mazan dai sukai shiru. "Karya yake yi" Ummimi ta ce har yanzu ta i zama lokaci zuwa lokaci kuma tana duba wayarta kawai sai tabi bayan Aliyu. Daddy har jiri yake gani baya so a fitar da maganar ya fiso a yi komai secretly har Safiyyerh ta dawo gare su amma sai yaushe ne?. Only God knows. ****Ammo na zaune ta yi shiru a akinta kamar kodayaushe ta yi nisa a tunaninta bata ma san Malam ya shigo ba sai muryar Inna Binta da ta ji a sama wajan ofar akin tana fa in "Yanzu don Allah Ammo da rana ma ba za ki daina kwantar miji kina satar kwana ba, wacce irin jaraba da masifa ce haka ni Bintalo jaraba kala-kala Malam in duk da basir ya cinye shi da rana ma ba za a bar mana miji mu dinga ganinsa duk da ba wata tsiyar yake yi mana ba" Ammo ta cira kai ta kalli Inna Binta ta juya ta kalli gefe har yanzu ba taga Malam ba cikin rashin fahimta ta ce "Kamarya?" "Ohho shafa ki ji mace an girma amma sai shegen munafurci da kissa wato kafin ki gama sallama an naki wa duniya kafin ya gama zama an ta'adda ya miki aikin mallake malam ko? Shi ya sa kaf gidan nan kin fi kowa yawan yara" Ammo ta kasa cewa komai da yar ta bu e baki ta ce "To ina Malam in yake yaushe ya shigo mini?" Ta banka mata harara ta nuna mata malam dake zaune ya yi shiru a hankali ta furta "Ikon Allah ki yi ha uri ban san ya shigo ba" Malam ya yi gyaran murya ko kallon Inna Binta bai yi ba cikin damuwa ya ce "Ammo ki nutsu ki ji me zan ce miki babu tabbacin abin dai har yanzu, ki yi ha uri idan har hakan ya kasance gaskiya" Jin haka ya saka Inna Binta neman waje ta zauna a