Sashe 24
Mutallab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abdullahi can ta matse masa" Modara ya bu e baki da nufin sake magana "Kana kira mini sunansa sai na yi maka sabuwar kaciya" ba shiri ya tsuke bakinsa suka ja Lauje tare da barin wajan cike da takaici. Safiyyerh na kwance tana bacci tun bayan sallar asuba da ta yi, Dr Hash ya sake aura mata ruwa a hankali kuma ya ji tana surutai asa- asa ya kasa kunne da kyau ko zai ji mene take cewa "Ashraf ka taimaka ka dawo ka fa a mini ma'anar FS, ka fa a mini suwaye mutane biyar in da kake magana akai, Ashraf the company is belong to your father,ko a mafarki ne ka fa a mini ko a fatalwa ne ka zo mini bazan ji tsoro ba, Ashraf i really really need your help, don ka dawo" Dr Hash ya juya ya kalli daddy da ya yi asa da kan shi "Daddy akwai damuwa fa, meke faruwa da Fiyya ne? Me take bu ata wajan matacce ne Ashraf zai fito daga kabarinsa kuma ya yi mata, daddy Ashraf ya rasu fa ranar da za a aura musu aure da Fiyya me ya sa ba za ta yi tawakakkali ba, me ya sa wai?" "She loves him so much, tana son Ashraf ne shi ne dalili" cewar daddy yana sake matsawa tare da zama a bakin gadon ya kama hannun Fiyya ya ri e cikin nasa da kyau "wannan zafin hannun fa? Her temperature is too high, bana son zazza i a jikin Maama ka yi wani abu Dr Hashim" Dr Hash ya ce "Ciwon kanta da bugawar ne ya saka mata zazza i, na yi mata allura zuwa anjima zai sauka ai" Maimakon Fiyya ta yi shiru sai ta cigaba da surutan sosai tana furta "Ni ba Tiger ba ce Tahhb, why are you decided to call me Tiger?" Kamar a gaske kamar kuma yanzu ne ta ji saukar muryarsa a tsakiyar kanta, sautin ya sauka a irjinta "Saboda ke matar Moh ce Tiger, zama matar Moh is not easy we most fight together halinki irin na tiger ne, matar Moh" tar da bu e idanunta a gigice a kuma sauti na ru ani ta ce "Motar Moh" Daddy da Dr Hash suka kalli juna jin abin da ta furta kafin su yi magana Safiyyerh ta juyo ta kalli daddy sai ta yi murmushi mai kyau wanda suka jima basu gani a saman fuskarta ba, ainahin murmushi da kyawun Safiyyerh daya shu e ya dawo fil ta ri e hannun daddy a nutse ta ce "His voice daddy, muryarsa ce" "Shi wa?" "Tahhb" daddy ya yi murmushi yana shafa sumar kanta ya ce "ai kuwa na ji nima, ki yi bacci Maama za ki samu sau i in sha Allah" ta jinjina masa kai tana ri e da hannunsa har lokacin ta ce "In sha Allah daddy, in sha Allah daddy" jikinta ya saki ta koma bacci daddy ya sauke numfashi ko samun sukunin karyawa bai yi ba, ya dubi Dr Hash ya sake duban Fiyya ya ce "Ka yi mata allura kafin ta farka" "Daddy ka duba Maama tana cikin damuwa ba, baka jin allurar zai saka ta dawo da abi'unta na baya daddy yin allurar ba mafita ba musamman ga lafiyarta, tsayin shekaru na daddy har yaushe ne ka duba Safiyyerh don Allah" mi ewa tsaye daddy ya yi ya ce "Ka yi hakan Dr Hashim Abdu Marafa, completely tsayin rayuwa haka nake son ganin Safiyyerh" jinjina kai Dr Hash ya yi sai ya ha a allurar har guda biyu ya juya bayanta ya caka mata cikin sauri ta ame jikinta wani irin azaba da ra i take ji a duk sanda aka yi mata allurar. Yana yi mata ya fice ba tare daya sake kallon daddy ba. Ya zubawa photonta idanu yana juya mata baya a hankali ya ce "Ki yafe mini Safiyyerh ki fahimce ni ki fahimci mahaifinki, i am sorry Safiyyerh" fita ya yi ya rufo ofar ya nufi parlonsa a zaune ya tarar da Ummi tana kallon shi ta ce "Ya jikin nata? Ta farka ne?" Ya zauna yana numfasawa "Ta sake yin bacci, ina Aliyu?" "Kasan sai ya yi niyya yake shigowa" daddy ya auki wayarsa ya kira number Aliyu yana agawa ya ce Aliyu zo mana ya ajjiye ya kalli Ummi cikin kulawa ya ce "Ina jin kamar ha a auren Aliyu da Safiyyerh na yi kuskure ina jin kuma hakan shine mafita, ina jin tsoron tambayar da dukkan su za su yi mini wacce bani da amsar su, da gaske bani da wannan amsar tasu Ummi, ba komai Safiyyerh take ganewa tana jin ta isa ta yankewa kanta hukunci ita ba kowa face yarinya mai wayon gaske da tunani Safiyyerh bata san komai ba ita kawai yarinya ce" "Ka san dole zaka jira amsar wannan tambayar da kake tsoro, amma sanar dasu auren shine zai fi maka a raina ina jin Maama ba zata yi maka gardama ba" kafin ya ce wani abu Aliyu ya bu ofar ya shigo da izinin daddy kamar kodayaushe wandon sojoji ne a jijinsa da farar riga tas ya ora hula p.cap a kan shi ya zauna kansa a asa yana furta "barkan ku da safiya" "Aliyu ya aiki, baka san Maama ba lafiya bane naga baka shigo ba?" "Na sani" ya ce kawai a ta aice yana danna wayarsa "Ka sani kuma? Shine ba ka yi mata sannu ba me ya sa kake haka ne Gadanga, me ya sa kai zuciyarka bata motsawa sai akan Maama meke damun tunaninka baka aukan responsibility inka as a brother" "Idan bai auki responsibility nasa matsayin yaya ba, yanzu zan auki responsibility Safiyyerh a matsayin mijinta" da wani irin yanayi Aliyu ya juya ya kalli daddy yana son sake tabbatar da abin da ya fa a masa a zuciyarsa wani irin fargaba ne ya wanzu ciki a fili kuma ko gezau ya dai zubawa daddy idanu can ya ce "kamarya?" "Da kai da Safiyyerh baku da wata kalma da za ku replying mutum ko responding maganarsa sai kamarya? To kamarya dai yadda ka ji ai aikin da ka yi na soja bai saka ka daina jin Hausa ba, har gwara Safiyyerh ma" daddy ya gyara zama Aliyu dai kallon mahaifin nasa kawai yake da wani irin yanayi mai auke da zallar mamaki. "Aliyu ni ban isa na saka dole ba, ban kuma isa na tilasta rayuwarka yin abin da ka yi niyya ko baka so ba, Aliyu ni dai mahaifinka ne ka saka hakan a zuciyarka. Bani da wanda zai mini wannan rufin asirin kaf family, ka manta da batun Junaid da Awais da kuma Dr, kar ka tambayi mai ya saka na za e ka na ji a raina zaka kula da Safiyyerh ko bayan bana numfashi ko bayan asa ta rufe mini idanu na za i aura maka ita saboda dalili mai arfi, na yarda da ingancinka" Ya yi shiru Ummi kuma Aliyun take kallo shi kuma yana kallon daddy da duk nutsuwarsa. "Ranar da Ashraf ya rasu a ranar aka aura maka aure da Safiyyerh, don Allah don girman Allah karka tambayan tsakaninka da Safiyyerh waye ba jinina ba, wannan tambayar shine abu mafi girman laifi a gare ni, ka taimaka ka yi mini alfarma ka ri e Maama ka amshe ta matsayin matarka" Captain ya kasa motsi balle magana bai ma san mene zai ce ba. Daddy ya matsa hannunsa "Don Allah Aliyu" "Ita ta sani?" "A'a, kai na fara sanarwa Safiyyerh bata da wata matsala ga umarni na" Aliyu ya sake yin shiru idanunsa a asa har ya juya baya ya sake juyawa ya kalli daddy a hankali ya ce "tell her first, ko bana son ta zan yi arin ganin na fara son Safii in sha Allah" "Ba zan tambaye ka ni ne ba anka ba ko ita, zan bar tambayar a raina har sanda ka shirya fa a mana gaskiya ni da ita, zan rayuwa da fargabar sanin amsa, da gaske daddy zan so Safii iya tsayin numfashi tunda kai ka za a mini ita" Daga Ummi har daddy kallon Aliyu suke musamman daddy bai yi tunanin jin wannan amsar ba ya dinga kallon Aliyu ba ko iftawa "da gaske zaka so Safiyyerh? Ka san Safiyyan da nake nufi Aliyu?" Aliyu ya bu e idanunsa wanda hula ta an rufe masa su "Safiyyerh Abdu Marafa ko ba ita ba?" "Ita, zaka so ta ka ce?" Daddy ya sake fa a da mamaki "Bata da Qualities in da za a sota ne?" "Haka ne tana da shi, na shirya tafiyar ku za ku bar asar nan nan da kwana biyu bana bu atar ku gaba aya a yanzu domin nutsuwar zuciya" Aliyu ya sake duban daddy ya ce "Kuma? Ka bar tafiyar nan daddy" sai kuma ya juya gaba aya ya kalli Ummi da daddy "Aliyu soja ne, so i will be with her always" Yana cewa haka ya fita da yar ya yi jarumtar kai kansa aki ya cire p.cap in kansa ya shiru ba auran ke damun shi ba, tunani ya fara wa daddy ya haifa tsakanin shi da Safii? Da yamma Safiyyerh ta akko asa bayan tafiyar Kinal daga ita sai duguwar rigar bacci kanta ba hula sosai uruciyar nan tata ya bayyana, ta zauna saman kujera ta lumshe idanunta ta zama wata ira tun bayan tashin ta daga bacci jikinta ba wari. I dake kallonta ya ce "Sannu Manager, ya jikin yanzu?" "Baya na ke mini ciwo Yaya J, ina jin Dr Hash ya mini allura, bana son allurar nan Yaya J bana jin da in ta watarana zata kashe ni don Allah ka cewa daddy ya daina sawa Dr ya yi mini" idanunta ya shiga kawo ruwa ta yi lamo da kanta saman hannun kujera. Daman yana bakin ofa jin abin da take cewa sai kawai ya juya shi kuma Yaya J ya ce "Ki yi ha uri Maama za a daina miki in sha Allah" ta yi shiru kawai. Dr Hash na zaune a lambun gidan yana waya kasancewar baya da wani aiki a asibiti hutawa yake kashe wayar ya yi ganin Captain tsaye a kan shi. "Babban yaya barka da fitowa" kamar ba zai zauna ba