Sashe 23
Mutallab Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
about your life, zan kira daddy a auki gawarki ok" kashe wayar ya yi. Safiyyerh wani irin zafi ta ji a zuciyarta da ra i bata san ma wanne gurbi zata saka Aliyu ciki ba idanunta ya kawo hawaye ba in cikin kiran da ta yi masa tana zargin kanta da laifinta ne. Ta cikin madubin motar take sake kallon motar dake bib bayanta da kuma sauran baburan ta runtse idanunta a fili ta ce "Ya Allahu Ya Rahmanu ka dubi Safiyyerh ka kawo mata auki..Daddy!" Ta kira sunan daddy a gigice tana sakin steering motar bata sake sanin abin da ya faru bayan nan ba. Yana tsaye fitowar shi daga motar kenan ya dubi yadda ta yi flat kwance a asa gefen kanta da jini ya kalli sauran jami'an tsaron da suke wajan "Is she ok? Tana numfashi?" "She is, buguwa ne kuma Allah Ya rufa asiri motar ta tsaya da kanta, ba'a yi nasarar kama ko mutum aya ba, yarinyar ce dai bamu san wace ita ba za mu duba id card nata sai a kira iyayenta a shaida musu ko asibiti ne a tafi da ita" ya yi maganar cikin girmama kan shi a asa, wanda ke tambayar ko Fiyya na raye ya yi baya rungume da hannunsa can ya duba a gogo sai bai ce komai ba "Sir meeting in naka? Ina tunanin ka je kawai za mu kula da komai tunda shugaban jam'iyya da secretary na jam'iyya na jiran zuwan naka" kafin ya yi magana cikin sauri wata mota ta arasu wajan kamar zata tashi sama ko gama daidaita tsaiwar motar bai yi ba ya fito idanunsa a kan Safiyyerh, mutumin ya dubi fuskarta shima a hankali kuma ya ce. "Easy Captain, ka kira ni sanda muke kan titin da take ta ku uta Allahamdulilah" jinjina kai Aliyu ya yi cikin girmamawa ya ce "thank you" "Anything for you Aliyu, amma ku kula tana da harshe zuciyar nan tata irin take ce, Allah Ya bata lafiya" Aliyu dai na tsaye idanunsa akan fuskarta ya kasa magana har mutumin ya shiga motarsa driver ya ja, jami'an tsaron suma suka shiga motar suka marasa masa baya cikin tafiyar sirri. Ya jima yana kallon ta hannunsa ri e da wayarsa tunanin yadda zai yi da ita, ar mitsitsiyar yarinya ta fito da shi, banda darajar daddy da babu abin da ya yi masa zafi sanin cewa idan Fiyya ta mutu hakan na nufin tsayawar numfashi daddy ya saka ya lallashi zuciyarsa. Cak ya auke ta ya saka ta a gaban mota yana yin baya da kujerar a ransa ya ji ba zai zama drivernta ba, ya auki wayarta ya rufe motar yana shiga ya tare da zama ya sake juyawa ya kalle ta da kyau sosai jinin ke fita a goshin nata ya ta e bakinsa kawai a hankali kuma yana ora mata tissue ya furta Fitinanniyya... Safiii Farar safiya ce gari ya yi shiru amma shi idanunsa biyu, yadda ya ga dare haka ya ga rana idanunsa tarwai a sararin subuhana yana kallon sama da abubuwan da Ubangiji ya wanzar a cikinta, a hankali ya juya ya kalli Darma da Goje sai kuma Mangal dake can gefe guda ya sha ta gaya masa babu da i sai lilo yake da afarsa a sama. Mangal ne ya bu e idanunsa da sauri ya mi e zaune yana murza idanunsa alamar bai gama wastsakewa ba. "Jeji naka dawa taka ka huta mai dawa, ba dai gaba da gaba ko ta baya aryar mutum dan uwatar ya aka yi ba ka yi kasa bane ka raya daren da gadin mu?" Moh ya yi shiru irjinsa sai agawa yake. "Ina tsoron shirun nan naka don ba zai haifar da a mai ido ba, ka tara dafi a cikinka jira kake ka samu inda zaka sauke arin dake damun jikinka ka sarara a kaiwa mai duka lillahi kukan kawai" sai a lokacin ya juyo da gajiyayyun idanunsa da suka shige ciki duk girman da suke da shi, sun yi wani bala'in ja ya zubawa Mangal ido "Talk da turanci kenan da hausa na goga maka yi magana sarkin jeji" "Mangal" "Yes inji masu jajayen kunnuwa bi ma'ana na'am" muryar Moh bata fita sosai a lokacin duk wanda ya nutsu zai hango wani irin sanyin murya da yake da shi da sauti maraya hayaniya. "Wacce cuta aka ta a yi maka a rayuwa wacce ba zaka iya yafewa ba?" "Kan uban nan, ni ai ka sani a kusurwa kaina ya kulle wanda sukai mini kuma tuni sun girbe abin da suka shuka bana yafiya bana cuta bana bari a cutan" cije baki kawai Moh ya yi yana lumshe idanunsa da sauri ya bu e su tar saboda yadda yake jin kakari da numfashin fitar ranta yana yi masa amo a kunne, ya mirgina ka an ya auki afarsa aya ya ora akan aya yana girgiza wa ya zubawa zara-zaran yatsun afarsa idanu tare da rungume hannayensa a irji. "Wai what happened Mai dawa?" "Ka dai na yi mini turanci don uwarka" an tsinanniya ba, ba uban da ya iya kuma ya san ai duk bama ji shima a Legas ya koya" cewar Goje yana farkawa tare da zama dukkan su babu wanda yake da niyyar mi ewa domin yin sallah. Goje ya kalli Mutallab ya ce "Yaushe za a kwalo berewar nan ne? Ka yi shiru karfa ka ji a masa aiki" Da sauri Mutallab ya kalli Goje jin sunan daya kira na barewa ya lumshe idanu ya bu e zuciyarsa na bugawa sosai sai bai ce komai ba can dai ya mi e zaune a hankali kuma ya tashi tsaye ya zaga bayan katanga ya da e kafin ya dawo wajan Darma ya kalli hannun Mai dawa ya bu e idanu ya ce "Bura... Wannan wayar ka shanye to kwarankwasa ka shirya zama mahaukaci, wayar doki ce fa? Wai kashe kanka za ka yi akan wasu an jakuna ka fito musu gaba da gaba mana, a yi komai duk abin da zai faru ya jima bai faru ba, arshe dai gidan an kande ne kuma mu ba wai ba in ta bane" Mutallab ya tsaya cak a tsakiyar wajan naman jikinsa na motsawa musamman kakkauran irjinsa mai fa i sai kawai ya shagi e bakinsa gefe kamar zai yi murmushi da sauri ya tsuke fuska zuciyarsa na tuna masa shekarun da suka shige a fusge ya furta "Sai godiya" gaba aya suka mi e tsaye suna maimaita "Sai godiya" Basu fargaba sai ganin tarin wasu an daba suka gani suna fitowa daga wasu lunguna a alla sun fi su ashirin auke da gorori wasu wu e. "Dara ta ci gida lallai an raina mu, mu wasu da ai zasu kawowa farmaki har lukanmu?" Cewar Darma Mangal ya kalle su ya ce "Kuma suwaye ku yara?" Wani daga cikin su ya fito ya tsaya a gaba ya ce "Sanin sunana ko waye ni bashi da wata fa'ida a gare ka, da zaka tambayi wanne kalar kisa zan maka zai fi maka, amma saboda gudun tilawa ko tafiya iyama da tunanin wanda ya kashe ka lallai zan goga maka sunan nawa". Ya zaro wu a daga cikin ugunsa idanunsa akan Moh da bai ma kalle su ba sama kawai yake kallo yana jin yanayin na yi masa da i ya ora da "Uban an daba nake maganin ananun yara masu oyewa a sa o, to cut you short sunana Lauje, ban du o dan na saka muku makami ba, na zo na tafi da uban gidan naku salin alin akasin hakan wajan bijire mini zai saka an samu kwacewar lissafi dar kenan" wanda ke kusa da Lauje mai suna Modara ya ce "Ka sa o shi a wuya mana sai ka tsaya ata yawun da Ubangiji ya halitta a bakinka Oga?" "Ban zo don rigima ba, bisa umarnin Hon na zo wannan shine" Darma ya matsa gefe yana nuna musu Mai dawa Moh kenan ya ce "Bisimillah gashi nan kuje da shi kuna da hannu na san" Moh ya sake juya musu baya maganganunsu da gaske ciwon kai da zafin zuciya suke ara masa hannunsa kawai yake dun ulewa yana hura iska sama ko yaushe ya zama sa'annin yara irin su Lauje? "Ji mana" Mutallab ya juyo yana gyara tsaiwa idanunsa a birkice Lauje ya dinga kallon Mai dawa, shi bai ya yi tunanin haka yake ba yaji ana Mai dawa da Mutallab sai ya ji sunan Mutallab kamar na ananun yaran ganin Mutallab cikakken namiji a tsaye mai kakkauran hannu da bu irji gaba aya jikinsa a mur e yake musamman damtsen hannun ya basar ya ce "Shige muje" Da hannu Mutallab ya yi masa alama da ya zo ya tafi dashi, Lauje ya nufi wajan Mutallab ba tare da sanin cewa akwai shafin hannu a jikinsa ba ganin ba wani makamani hannunsa ya saka ya nufe shi. Yana mi a hannu da sunan kama shi Mutallab ya yi masa wani naushi a gefen irji, nan take Lauje ya fara fari da idanu ashin gefen irjinsa ya yi ara ya sulale a wajan ba numfashi. Ganin hakan ya saka su Modara ja baya a tsora ce ya ce "Kut ya bazar dashi ba, wannan mahaukaci ne" "Bai mutu ba tafiyar zango alilan ya yi kawai ya samu karaya a irji, kar dai ku manta da Mai dawa kuke magana masu jeji da namomin jejin da kansu matsalar gajanci kenan kun tari mutumin dake da shafi a hannunsa duka aya ka sume gwara ya saka maka kaifi daya saka hannu, ya zame muku hadda. Yi batu waye ya aiko ku?" "Hon Ma atai" "Wani abu ne haka? Me za a yi masa?" Modara ya ce "Bamu sani ba, ya ce yana bu atar ganinsa shi ka ai kuma a sirrince" "To ba zan zo ba" Cewar Moh yana cije bakinsa hannunsa har yanzu rawa yake baya son yin kisa, idan ya ri e wu a bai san me zai iya yi ba kuma sam. Da mamaki Modara ya ce "Kasan waye hon Ma atai kowa? Wallahi taimako zai baka shine kawai yake jin tausayin an daba irin mu" an daba irin ka dai, shi Malam Abdullahi ne balle ya yi mini baki, ko Malam