← Book details Miskili Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 54

Sashe 7

Miskili Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

kud'in safaran kokin ne da kud'in dazan miki Asirin sakashi ya Auri y'ata zaki saka yaturo mun"murmushin gefen baki shariff yasaki yana rufe laptop d'in"yanzun burunsa kawai fareedah ta kamasa zobban nan"yaga Abinda yakeso yagani sannan zai dawo kan Alh yahaya yarabashi da mahaifiyarsa"ada haushin mus'ab yakeji Amma yanzun sai yaji bbu jin haushin sai jin k'aunarsa"dan yasan mus'ab Abokine nagari"gashi yabi shawaransa yaga Amfani Acikin ta"inda be Ajiye CTV camera d'in ba taya zai san me Alh yahaya ke k'ullah akansu??da wannan tunanin ya wuce katafaren bed room d'in sa Aljannar duniya"time yaduba har 10 pm ta wuce"wanda tsarin lokacinsa 9:30 pm yake shiga bath room yayi wanka"zuwa 10 pm yake kwanciya bacci "kasancewar sa kamar bature yake"be kwanta d'in ba saida yayi wankan"Abin mamaki yayi mafarkin gashi nan shida wata yarinya suna sanye da fararen kaya cikin wani lambu"suna zaune kan grass carpet,kansa saman cinyar ta"ba'a ganin fuskarta sosai ta kama hannunsa tasaka masa wata red d'in flower tana fad'in tukwicine gareka my *salfad* yanadai kallonta beyi mgn ba sai kok'arin kissing d'inta yakeyi ita kuma tak'i yarda"ya riketa sunata dariya.....adaidai nan ya farka"wanda shariff yayi mamakin mafarkin"sunan *salfad* kuma yak'i barin zuciyarsa"da hanzari ya sauka daga saman bed d'in yanufi bath room.... misalin k'arfe 7:43 am Amaan ce zaune a parlourn taci gayunta cikin sabuwar doguwar riga gownt dark blue me zanan white"dukda bata shafa koda hodaba Amma tayi kyau na musammun"tayi tagumi da alama tunani takeyi"veil d'in kayan na hannunta"yayinda baba ladi na kitchen tana had'a musu Abin kari"wanda Amaan taso tayata Aikin itace tace tabarshi sbd gudun kar Asamu matsala"har fahad shariff ya shigo yayi sallama Amaan bata saniba"kallo d'aya yamata ya d'auke kansa yana lura tunani takeyi"gefen kujera ya zauna fuskarsa kamar kullum Ad'aure"yasha wankan suit bak'ak'e sunyi masifar haska fatar jikinsa..... k'amshin turarensa me dad'i daya cika wajen shine yasaka Amaan saurin kallon cikin parlourn"tana hangosa tasaki murmushi zumbur ta mik'e tsaye tana fad'in hamma nah yaushe ka shigo?"yana zaune yana Aikin danna waya kallo bata isheshiba"k'asa ta duk'a tana fad'in Ina kwana?"be Amsaba sai cewa yayi dama kina tunanin gulma Ina zakisan na shigo?dukda ga yadda take bata hayyacinta saida taji yabata haushi "sai bata koma mgn ba ta mik'e tsaye takoma inda take zaune"Ahaka baba ladi ta fito suka gaisa dashi ya tambayeta koda Akwai wani abu da suke buk'ata?"tasanar masa babu"daga haka ya mik'e tsaye yasaci kallon mutuniyar tasa datak'i koda kallon inda yake ya tab'e baki yasakai yafita....da yamma yana zaune office nashi mus'ab yashigo"da k'yar ya Amsa sallamar tasa"shi kuma yana y'ar dariya yace"haba hamman Amaan Abin bana fushi bane"banaso laifin mansoor yashafeni"ni kaina na masa bayanin dududu shekaransa 4 dayun Aure, babu Abinda yarasa wajen matarsa meye naya k'ara tun yanzun?"ai yabari zuwa nan gaba saiya k'ara"kuma niban sanar masa komai kan Amaan ba"Amma duk yarikice kanta.... tab'e baki shariff yayi yana d'age kafad'a yace"damuwarsa ce! kune matan ke gabanku shiyasa"Abinda nasani kawai idan na sadata da iyayenta ko a ranar zai iya zuwa subashi ita banida damuwa da hakan"mus'ab na murmushi yace"kaima Akwai lokacin da macen zata zama itace a gabanka.....dam! k'irjin shariff yabuga daya tuna kalaman yarinyar mafarkinsa *tukwicine gareka my salfad*.....yanzun ya kuke ciki kaida fareedah?"ya d'auki kusan second 10 kafin yace"zuwa jibi insha Allah zamu gama da babinta"Aikinka na kyau Abokinah"Amma kasan dai Alh isah yasan Ankama Alh tanimu?"duk nasani"kuma yanzun haka tuhumarsa akeyi shida waye keda hannu Aciki Amma yasaka taurin kai"nace su tuhumesa da shoking"gaskiya hakan shine zaifi"Amma dan Allah kamanta da komai ku cigaba da hud'd'a da mansoor"shiru shariff yayi be koma mgn ba"mus'ab daya gaji da zaman kuramen saiya mik'e tsaye yafita"sai wajen k'arfe 6:30 pm shariff ya shigo gidan"baba ladi ce kawai a parlourn "Amaan na d'aki ta shiga toilet"yana rik'e da ledar turarukan datace masa tana so da ledar ice cream d'in da duk yasiyo mata"saidai kuma daya fahimci bata cikin parlourn saiya zauna suka gaisa da baba ladi"Ahaka Amaan ta fito daga cikin d'akin ta canza kaya bana safe bane jikinta"tana ganinsa saita koma d'aki da sauri tana b'ata rai"duk yana lura da ita"baba ladi na murmushi ta tashi tabi bayanta"bbu jumawa ta fito tanata turo baki idanuwanta cike da k'wallah"da Alama baba ladi ce ta turota"tazo ta zauna kan kujerah batayi masa mgn ba"sosai tabashi haushi"yasha Alwashin saidai su kwana Ahaka bazai mata mgn ba.....✍️
Chapter 7 · 0% Book details