← Book details Miskili Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 54

Sashe 22

Miskili Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

one duk wanda yasake yamaka wata banzar tambaya game da Amaan kace kaima baka saniba"da sauri Abdallah yace"to shikenan yaya yanzun na biyoku ko?tsaki shariff yasaki yana bud'e k'ofar ya shiga..... Amaan dai ta bishi da kallo Aranta tana gulmarsa wai hamman nan yacika masifa"kasancewar tana cikin motar tana lura da yadda suke mgn shida Dr mansoor"shiru na wasu y'an mintinah yaratsa"shi yana driving d'in ,ita kuma tana y'an kalle kalle da wasa da yatsun hannunta"hamma ! shiru yamata yak'i mgn"ganin Hakan datayi sai bata koma gigin masa mgn ba har suka iso wani had'ad'd'en wajen siyar da ice creams da kayan ciye ciye"saida yagama parking ya juyo ya kalleta"d'an sakin fuska yayi sbd ganin damuwa Atare da ita..... Amaan! yakirata cikin k'asaitacciyar muryarsa yana kafeta da manyan idanuwansa"kasa Amsawa tayi kanta dai na'a k'asa"yaci gaba da cewa"kinfi kowa sanin halinah bana son yawan surutu ko?"so you have to be care full"yana fad'in hakan yabud'e k'ofar yafito"itama fitowa tayi batare data fahimci me kalamansa na k'arshe ke nufi ba"saidai tayi k'ok'arin daidaita nutsuwarta"gefenta ya matso ya tsaya yana lock d'in motar"idan ka kallesu wuf d'aya zaka d'auka sud'in masoyane dan ba k'aramin marching da juna sukayiba"wuce muje"shine Abinda yafad'a yana juyawa cike da aji had'e da shan k'amshi yafara hawa stars d'in shiga cikin wajen"Amaan batayi mgn ba tabisa"kusan atare suka shiga ciki"maza da mata y'an gayu masu aji kowane na zaune shida friends d'in shi ko budurwasa"directly table d'in da bbu kowa Anan shariff yanufa yaja kujerah ya zauna Anutse"Amaan ma tazo ta zauna tanata b'ata fuska"ya kalleta , fad'amun dame dame kikeso aka miki?"bakace wajen wasanni zamuje ba?"Babu time ,kinga Ammi tace karki jima"zuwa next week zamuje can "is okay?"nok'e kafad'arta tayi ta turo baki"yatab'e baki yana d'age kafad'a had'e da cewa ke kika sani to"hakan yayi daidai da isowar wani ma'aikaci"cikin harshen turanci sukayi mgn da shariff yasanar masa Abinda suke buk'ata"kamar Ance yad'an kalli wajen"yatsina fuska yayi sbd ganin wasu daga cikin matan nata kallonsu"daga can gefe kuma Ibtihal ce zaune tsakkiyar wasu maza suna bata ice cream"tayi wata irin shiga irin ta marassa tarbiya"su kansu mazan daka gansu kasan bana gari bane"tunda shariff da Amaan suka shigo Ibtihal ta lura dasu take binsu da wani irin mugun kallo tana girgiza jikinta"har aka kamusu komai gabansu duk kan idonta"kasancewar Amaan tasan ice cream tunda yana siya mata shi"saidai sauran snacks da shawarma da aka Ajiye musu bata fahimci ko meye suba"roba guda shariff yatura mata gabanta yatsareta da Ido beyi mgn ba"yayinda shima tashi tana gabansa"da k'yar yad'an sha ice cream d'in kusan rabin roba ya Ajiye yana had'e rai "sbd yaji gaba d'aya wajen ya ishesa sbd yadda aketa kallonsu"d'aya daga cikin ma'aikatan wajen yakira"bayan ya iso yasanar masa Amusu take a ways d'in sauran"bayan tafiyar mutumin ya kalli Amaan yana fad'in 5 minit nabaki ki idar mu wuce"batayi mgn ba tana dai tsakuran ice cream d'in"can idanuwanta suka hasko mata Ibtihal dake rik'e da waya tana danne danne"hamma! oh my God"pls Amaan tashi muje "yafad'a yana tashi tsaye"ya Amshi ledojin da ATM card daya basu su zare kud'insu"Amaan kuwa tana rik'e da robar ice cream nata ta biyosa"sai bayan sun shiga mota tace"hamma naga wannan da mukayi fad'a da ita"sarai ya fahimci Ibtihal take nufi saiya shareta yak'i mgn"kai tsaye gidan mlm suka nufa"bayan sun iso nanma saida yamata warning sannan suka shiga ciki"yanayin yadda mlm da babah ladi sukaga Amaan sun tabbatar tana samun kulawa over"wasu magungunan da y'an shawarwari mlm yabashi"yasanar masa sunata Addua da k'ok'arin ganin An karya wannan sihiri insha Allah"itadai Amaan tana zaune bata wani fahimtar meye suke cewa"da zasu tafi Shariff yamusu Alkhairi me yawa sannan suka nufi gida, bayan shariff yakira Abdallah yatambayesa su Abdul sun tafi?yace masa Eh....sai wajen k'arfe d'aya saura suka iso gida....✍️
Chapter 22 · 0% Book details