← Book details Miskili Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 54

Sashe 52

Miskili Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

hasara kuma yana tare da dana sani.....kinga dallah ki dena mana wani zancen banza munata kanmu"ki tashi kibamu waje ko jikinki yaga miki"tunda dama duniyar ta juya miki baya ai dole kiyi nadama marar amfani"cewar sharrif atsawace yana binta da kallon banza"ta mik'e tsaye tana share hawayenta ammi ta tsaidata ta zaro dubu goma a jaka ta bata"hannu na kirma ta amsa tana godiya ta wuce"daga yanzun bance ka koma irin hakaba sharrif "dama kwanaki sadeeq ya gayamun ta kamu da ciwon k'anjamau"tana bin asibitoci yawon neman taimako sbd dangin uwarta dana ubanta babu wanda zai taimaketa"tunda daga uwar har uban kowa ya mutu...ita irin wannan rayuwar idan mace ta fara yinta"jinta takeyi babu ya ita"kuma babu abinda zatayi da manyan kud'ad'e zasu shigo mata sai hakan"saidai duk ranar da duniya ta dena yayinsu tayi juyin waina dasu saidai addua"fatanmu allah ya shiryi masu irin halinta "yana k'ok'arin mgn aka bud'e k'ofar labour room d'in..... atare ammi da sharrif suka nufi bakin k'ofar suna kallon doctor d'in"tayi murmushi tana fad'in ta sauka lafiya"ansami baby boy"ina dr sadeeq?"alhamdulillah nayi me gida"yau allah yanuna mun ranar danaga sharrif ya haifi d'an kansa"kai masha allah! cewar ammi cikin jin dad'i da tsantsar farin ciki"uban gayyar kuwa hannu sama ya d'aga yana godiya ga allah "doctor d'in na k'ok'arin komawa ciki sadeeq ya iso yana fad'in da alama ta sauka ko?"eh ta sami d'a namiji "cewar ammi"ok doctor kije ki shiryata itada babyn akaisu d'akin hutu"yak'are maganar yana rungume sharrif yace"congratulations yaya"kaga abdallah yaci million guda kenan?"gaskiya bazan iya bashi ba"kama isa ? yadda ka cika baki kayi alk'awari dole ka cika"barama na kirashi nasanar masa"cewar ammi tana zaro waya"sharrif kuwa cikin tsantsar farin ciki yacika sadeeq yakira mus'ab da hamma yusuf "cikin k'ank'anin lokaci kowa yaji labarin haihuwar amaan....me jego kuwa taji yau yadda akeji"bata tab'a zaton haka haihuwa takeba"bayan angama shiryasu itada babyn aka wuce d'akin hutu dasu"tana kwance babyn na gefenta kyakykyawan gaske dashi"ya kwaso kamannin mahaifinsa ,ya kwaso hasken fatarta"sai murmushi takeyi aranta tana tunanin wai yanzun wannan d'anta ne??...tana cikin wannan tunanin sharrif da ammi suka shigo cikin d'akin"ya jefeta da tattausan murmushi yana matsowa jekin bed d'in "tayi k'asa da kanta"sannu my salfad ya jikin?"alhamdulillah hamma nasami sauk'i"da sauri haka mom khalil?"kallon tambaya ta masa ya gyad'a mata kansa yana k'ok'arin d'aukar yaron"ammi ta matso tanata yimata hannu"itadai kanta na ak'asa tama kasa mgn"tun tana jin surutun sharrif yana yiwa yaron wasa yana tambayar ammi dawa yaron ke kama har tadena ji"daga nan bacci yayi awon gaba da ita....cikin farin ciki abdallah ya shigo cikin d'akin yana ihun murna ya ajiye basket d'in da ammi takirashi yakawo"saida yataka rawa kafin yace"kyauta biyu nasamu data d'a data million guda"ammi dai tayi murmushi batace komai ba "sharrif na kallonsa yamik'a masa babyn yana fad'in congratulation kayi weaning"bari kawai yaya shariff yazo yabani kud'ina party zamuyi da friends d'ina ranar suna"to shikenan zan k'ara maka million guda sai kuyi hidimar dashi"wai meyasa kuke bannata dukiya hakane sharrif?"ga mabuk'ata kuba mawa sai sharholiya kukeyi?"amma ammi ai kinsan yaya meyin kyauta ne da sadaka koda ba lokacin yin zakka ba ko?"hakane allah ya kyauta.....lokacin da amaan ta farka har ammi tayiwa babyn wanka sharrif shima yakoma gida ya d'akko zazzafan wanka"babu yadda ammi batayi dashiba kan yatafi ba yanzun zata tashiba yak'iya"saima tambayarta yakeyi idan ta farka waye zai mata wanka"baba ladi datazo itada matar mus'ab tace"itace zata mata"ana cikin hakan amaan ta farka...salfad kin tashi?"uhmm hamma dama baka tafi ba?"sai kuma tayi shiru sbd ganin duk mutane nata kallonsu"shi kuwa yatasata agaba yanata kallonta" anty billy da baba ladi ina wuninku?"lafiya qlau me jego"barka kuma"barka kad'ai"cewar sharrif yana murmushi sbd yafahimci tana jin nauyin amsawa ne "sharrif kaga zoka fita taci abinci tayi wanka"dama sadeeq yace bayan sallar la'asar za'a bamu sallama"bece komai ba ya juya yanufi k'ofa"hamma! juyowa yayi ya kalleta"zaka dawo anjiman ko?"kansa kawai ya gyad'a mata yafita"ammi ta girgiza kanta tana tunanin anya amaan zata yadda takoma wajenta tayi zaman wanka?sbd ta lura tana matuk'ar kishin sharrif....saida amaan taci ta k'oshi sannan baba ladi ta mata wanka ta gasheta"bayan ta fito ta shirya ta zauna tana shayar da yaron.....bayan sallar la'asar.....✍️
Chapter 52 · 0% Book details