← Book details Miskili Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 54

Sashe 34

Miskili Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

suka b'acewa ganinsa.....basufi mintina 20 da fara tafiya ba"text message na first bank yashigo cikin wayarta"da mamaki ta duba saiga sabon acc number ta gani"Atake ranta yabata shariff ne yasaka Aka bud'e mata sabon Acc"bata gama wannan tunanin ba Alert d'in 2million ya shigo cikin wayarta"shiru kawai tayi tana kallon wayar.....daga nan bacci ya kwasheta sai wajen la'asar suka tsaya wani restorant sukaci Abinci sukayi sallar Azahar data la'asar"Amma banda Amaan dake fashin sallah....sai Anata kiraye kirayen sallar magrib suka iso garin Adamawa"basu iso gidaba saida isha'i "driver d'in shariff da body quards nasa suka musu sallama sbd zasu tafi masauki daga nan washe gari da Asuba su koma gida"daddy yaso su sauka Anan Amma sukace bbu damuwa sunada masauki.....sune da kansu suka bud'e get d'in gidan sbd babu kowa cikin gidan"zabba'u da family nata suna can Asibiti An bata gado"ciwo yayi k'amari dole Aka kwantar da ita"Nasir be shiga cikin gidan ba daga waje ya musu sallama yayi tafiyarsa"Amaan da madeenah suka kwashe kayan Amaan suka wuce cikin gidan"bayan sun shigar da komi itama madeenah bata zaunah ba Abbansu tabi suka wuce gida"daddy kuwa part nasa yanufa....mommy tabi kayan dake Ajiye tsakkiyar parlourn da kallo tace" wa'annan ledojin fa na meye salma?wlh mommy hamma shariff ne yamun shopping"dayake hankali ya miki yawa shine kika Amsa ko?"kina ganin irin hidimar da mutanan sukeyi damu ko?"ah ah wlh Ammi nima sai yanzun driver d'insa yabani yace injishi"yanzun haka yabud'e mun sabon acc yasaka mun million 2 ciki"million biyufa kikace? Amaan na kok'arin mgn wayarta tayi ringing"da sauri ta duba k'irjinta na bugawa"saita mik'e tsaye ta wuce bed room sbd ganin sharif ne ke kiranta"itadai mommy da kallo tabita tana mamakin wasu Abubuwan "saita d'auki baby Nokia d'inta ta lalubo number d'in Ammi tayi dealing sbd ta sanar mata sun sauka lfy.....cikin sanyin murya Amaan ta masa sallama"ya gyara zamansa yana shafa kansa yace"yanaji muryarki wani iri ko iskan mota kika shak'a ne?"uhmm uhmm"Ina wuni?"lafiya qlau da fatan kun sauka lafiya?"Alhmdllh "d'an shiru na second 5 yaratsa"can yace"menene kikayi shiru bayan nasan idan kina tare dani kinamun surutu?"yanzun dan Allah hamma Abinda kayi ka kyauta?"so kakeyi ka k'arar da dukiyarka akaina ko?"dama wannan shine k'orafin?"Eh mana"mommy sai fad'a takemun....kinga ya Isa haka "yanzun kinyi wanka?"ah ah"sai yaushe?"yanzun zanyi nad'an kwanta"okay kina Ina yanzun?"Ina d'akin mommy a bed room "idan kin gama shirin kwanciya ki kirani"dato ta Amsa shi kuma ya yanke wayar "tashi tsaye Amaan tayi ta bud'e ward rope ta haska kayanta da flash light d'in wayarta tana kallo ta sauke Ajiyar zuciya ta zaro farin towel ta d'aura ta shiga wanka"duk da sanyi Akeyi hakan be hanata yiba sbd Akwai heater a toilet d'in "tana wankan tana tunanin Shariff harta idar ta fito"shiryawa tayi cikin riga da wondo na bacci"kafin ta fito parlourn sbd jin muryar yayun nata"sadeeq, yusuf,khalifa"sallama ta musu ta zauna suka gaisa suna murnan ganinta"yayi da sadeeq keta tsokanarta "mommy dake zaune ta kalleta tace"kije ki kwashe indomie na nan dana sauke na d'iba"dato ta Amsa ta fita daga cikin parlourn "bata jimaba ta dawo ta zauna tana cin Abincin tana tuna gidan Ammi"Ahaka daddy ya shigo da jallabiya Ajikinsa da farin glass ya zauna"duk mazan suka masa sannu"yayinda mommy be isheta kalloba sbd har yanzun fushi takeyi dashi"gyaran murya yayi yace"yanzun na gama waya da shamsiya"tace mun Aiki za'a yiwa zabba'u a k'wak'walwa sbd buguwar datayi Akai ya shafi cikin k'wak'walwarta"Ana buk'ata kud'i nera dubu d'ari shidda da hamsin"ta kumayi mun complaine d'in zabba'u ta koma kamar k'aramar yarinya"sannan likita yace"idan ba'ayi gaggawar yin Aikin ba zata iya samun tab'in hankali....yusuf yace "subahanallahi !kai meye kace musu daddy??.....✍️
Chapter 34 · 0% Book details