← Book details Miskili Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 54

Sashe 10

Miskili Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

hankalin duk Wanda ya aza idonsa Ajikinsa"kasancewar yau satday bbu office"dukda dai a week end yana ziyartar yaransa yaduba komai"sanye yake da wani had'ad'd'en yadi me tsananin tsadar gaske ash colour"yanada taushi da santsi"yabi ya haska choco skin nashi"kansa bbu hula"sumar nan Tasha gyara tana d'aukar Ido"sai fitinannan k'amshi ke tashi Ajikinsa "kamar ko yaushe hakama yanzun kyakykyawar fuskarsa Ad'aure take"baba ladi ta Amsa sallamar tasa ya zauna gefen kujera yana k'arema parlourn kallo suka gaisa"yana lura da Amaan na kuka"saidai miskilin kallo bata isheshiba "ganin yabasar da ita yasaka tace"hamma kaga baba ladi tak'i kunnah mun kallo ko?"ikon Allah! yau kuma k'arata zaki kawo Amaan??"ka ganta nan wlh bbu yadda banyi da itaba tayi kari tak'iyi wai tana jiranka kuje ka siya mata kayan wasa "tunda suke maganar ko gezau miskilin beyiba,kansa aduk'e yana dannah waya" saida sukayi shiru sannan yad'ago kansa anutse yazuba mata Ido"ta turo baki tana sunkuyyar dakai k'asa "tashi kije kiyi break fast"to hamma zaka jirani na gama saimu tafi ko?"ki tashi kije kiyi break fast"yakoma maimaita mata"kukan shagwab'a tasaka ta kwasa aguje ta nufi dining area"baba ladi ta girgiza kanta ta tashi ta wuce kitchen"shariff yaja tsaki yana tunanin Ina zashi da Amaan?"bayan ga yanayin yadda take ciki"kuma shima bayaso aganshi da mace yana yawo mak'iyansa suyi masa wata fassarar"dukda baya tsoro baya shakkar uban kowa"Amma yafiso ya kammala Abubuwan dake gabansa"musammun plane nasa da fareedah"wacce yana tunanin sai monday zaije gidansu ya Amso zobban nan.... Hamma na gama saimu tafi ko?"yaji muryar ta Agabansa"ya d'ago kansa yamata kallon second 3 ya d'auke kansa yana yatsina fuska yace"sai kin koyo yadda Ake gaisuwa da ladabi sannan saimu tafi"sannan kije ki canza kaya zan saka aka miki hijabai da gyaluluwa"Amma hamma nidai bazaka tafi ka barni ba ko?"ta fad'a cikin shagwab'a"shareta yayi yak'i mgn"ganin Hakan yasa ta wuce kitchen tasami baba ladi na wanke wanke "wai baba ladi ya Akeyin ladabi? murmushi tayi tace"ladabi shine idan zaka Amshi abu hannun wani musammun wanda ya girmeka zaka duk'a kasaka hannu biyu ka Amsa"haka idan zaka bashi ruwa ko Abinci saika duk'a cikin ladabi kabashi"kuma idan zaka gaidashi saika duk'a har k'asa,ta nuna mata "daga k'arshe tace"itama mgn Anaso kayi cikin ladabi da iya karya harshe"bawai tsiwa ko d'aga murya ba"shiru kawai Amaan tayi tana tunani can kuma ta fita daga cikin kitchen d'in "d'aki ta koma ta canza kaya zuwa bakar jallabiya"masha Allah! saita fito kamar balarabiya"saidai mayafin saman kanta ta azashi"ta saka takalminta plate shoes ta fesa turare"fuskar ta tayi fiyau sbd bbu make up,ko hoda da kwalli bata shafawa"fitowa tayi tasamesa zaune yana danna laptop d'insa "Ahanakali ta masa sallama ta duk'a gabansa tace"hamma sannu da hutawa"dama na gama shiryawa"da mamaki yabita da kallo ta sunkuyyar dakai "bece komai ya rufe laptop d'insa ya mik'e tsaye yana fad'in Amshi rik'emun na fito"batayi mgn ba ta russinah ta Amshi wayoyinsa guda biyu cikin ladabi"nanma yakoma mamaki "sai kuma ransa yafara bashi kodai yarinyar na hayyacinta?"saiya kawar da tunanin Aransa ya haye upstairs"Ajiye laptop d'insa yyi a parlourn yarufe yasakko k'asan "tana tsaye da Alama tunani takeyi"hamma sannu da fitowa"beyi mgn ba yamik'a mata hannunsa Alamar ta bashi wayoyinsa"saita nok'e kafad'arta "yatab'e baki yafita"ita kuma ta wuce kitchen ta sanarwa baba ladi sun fita"sannan tabiyo bayansa"hangosa tayi yafita get hakan yasa itama ta fito"tanata y'an kalle kalle sbd tunda tazo gidan sai yau ta fito waje"juyowa yayi suka had'a Ido "harara ya balla mata"ta turo d'an bakinta"bani wayata zanyi kira"batayi mgn ba ta bashi k'aramar "ya Amsa ya bud'e driver sit ya shiga"itama sai tabud'e front sit ta shiga"bayan yasaka kira sannan yatashi motar"Assalamu Alaikum yallab'ai"wslm ka Amso sakon?Eh yallab'ai "okay zanzo yanzun na Amsa"daga haka ya yanke wayar "ita dai tana zaune tayi tagumi"harya tashi motar batayi mgn ba hankalinta na wajen wayarsa tanata kallon wayar"Anutse yake driving d'in ya kunnah karatun Alkur'ani me girma"sunyi shiru suna saurare"basufi mintina 10 suna tafiya ba wayarsa babba tayi ringing "da sauri Amaan ta mik'a masa"ki danna green d'in ki karamun"yafad'a sbd yaji ringing d'in daya sakama Ammi ne idan ta kirashi zaiji"Amaan dai d'aukar masa wayar tayi ta kara masa a kunne shi yana driving d'in "garin hakan yatsun hannunta suka tab'o sajensa da gefen kunnansa....dan kallonta yayi sai kuma ya kawar da kansa"tun kafin yayi mgn Abdallah yace"yaya bbu lafiya kana Ina?"meya faru?"ciwon Ammi ne yatashi"gata nan kwance bata numfashi"inata neman inhela d'inta banganiba"yafad'a yana yanke wayar da sauri"shariff ya sauke Ajiyar zuciya yana saka hannunsa guda ya janye hannun Amaan batare dayayi mgn ba"yajuya akalar motar zuwa gidan Ammi "sai bayan sun iso yayi parking sannan yatuna kuskuransa na zuwa da Amaan dayayi Agidan"kallonta yyi murya bbu wasa yace"ki zauna zan shiga na Amso sako"karki sake ki fito"kina jina?"to hamma bazan fita ba"beyi mgn ba ya Aza mata gudar wayar sa saman cinyar ta yafita da sauri.....befi mintina 5 da fitaba k'aramar wayarsa tahau ruri sai Amaan ta fito daga cikin motar ta maida ta rufe"sai kalle kalle takeyi sbd ganin securities tsatstsaye da bindugu abakin get"ga wasu maka makan motoci a haraban gidan fake"gaba d'aya tama rasa Ina zata dosa"sai raba Ido takeyi"can ta hango wata yarinya (Ibtihal) ta fito daga wani corrido"hakan yasa ta wuce wajen"sbd Azatonta bazai mata fad'a ba tunda wayarsa zata kai masa"kallon kallo sukayi itada Ibtihal kafin Amaan tanufi interest d'in shiga cikin gidan"dukda ga yanayin yadda take Amma saida taga kyawun gidan da tsaruwarsa"kamar marar gaskiya haka ta tura k'ofar babban parlourn, adaidai lokacin da wayar shariff keta faman ringing"tun kafin Amaan ta shigo k'irjin shariff yabuga! sbd jin ringing d'in wayarsa"kafin yayi wani abu Akai Amaan ta shigo da sallama cikin parlourn....✍️
Chapter 10 · 0% Book details