← Book details Miskili Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 54

Sashe 50

Miskili Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

*************
mommy ce zaune Acikin had'ad'd'en parlourn ta da sharrif yagyara mata yazuba komai sabo"ga kuma yacika musu store da kayan Abinci"game Aiki ya d'aukar mata"kai ita Abin saidai godiya"ta k'ara haske da y'ar k'iba"yanzun lafiya qlau zamansu da daddy gwanin burgewa"ga jin dad'in y'arta na zaune lafiya d'akin mijinta.....sai sallama Aketa dokawa Amma k'arar TV mommy bata jiba"can aka yaye labulen parlourn"saida gaban mommy ya fad'i sbd ganin Anty zabba'u da Hjy hauwa (mahaifiyar Nasir) "dakewa tayi fuska bbu yabo babu fallasa ta Amsa musu"saidai kallo d'aya ta musu ta fahimci sunyi nadama"dama kwana 2 da suka wuce tasami labarin warkewar zabba'un"k'asa suka zauna kan carpet sunata kalle kalle Acikin parlourn"Ina wuninku?"cewar mommy sbd taga basuda niyar yin mgn sai kalle kalle da sukeyi"Ina wuni Hjy bilkisu?"Alhamdulillah" sai zabba'u ta fashe da kuka tana fad'in dan girman Allah kiyiwa Allah ki yafemun keda salma"wlh nayi nadama na girbi Abinda na shuka"tunda nadawo hayyacinah Aka sanarmun Abinda yafaru nayi nadama"dan Allah Hjy kiyi hak'uri kisaka Alh ya maidoni cikin zuri'ata"Hjy hauwa ta karb'e zancen da cewa Eh Hjy bilkisu nima nida Nasir muna neman gafaranku dan Allah Ayi hak'uri Ayafe mana sharrin shed'an ne.... murmushin takaici mommy tayi tace"Ayanzun kika gane kin girbe Abinda kika shuka zabba'u?"kinso ki wulak'anta rayuwar salma sai Allah yakareta ke taki rayuwar ta wulak'anta"sbd k'arshen wulak'anci har fyad'e maza biyu sun miki"salma kuwa Allah yatsareta ya had'a ta da mutum na gari da kowa a zuri'ar gidan nan kecin Arzik'in sa"kinga kuwa mu jarabawar Alkhairi ta zamar mana"inaso kisani! duk wanda yace" zaiyi takara da hukuncin Allah saiya fad'i k'asa warwas"batun Alh ya maidaki kinada baki kimasa mgn mana"banida damuwa da dawowarki kok'in dawowarki"yafiya kuma tun kafin kizo mun yafe kodan sbd baiwar ni'imar da Allah ya mana"kuma Allah nason masu yafiya"ke kuma yaya hauwa? Ai dama yau da gobe saurin zuwa gareta"nasir idan yana da kunya ya rok'i yafiya"yagama zargin dason kunyatamu?"yazo yayi Auren huce haushi Ashe yarinyar daya Aura har cikin shege tayi?"kin d'auka bamu sani bane?"ita rayuwa tun Anan duniya wasu Abubuwan Akeyin hisabi A kansu me hankali kawai ke ganewa"na d'auka salma ko lalacewa tayi Nasir me rufa mata Asiri ne matsayinta na y'ar uwarsa saidai kash ! Abin ba haka bane"saidai babu komai rayuwa ce"na yafe muku ubangiji ya yafe mana baki d'aya.... zabba'u da Hjy hauwa na kok'arin mgn sadeeq da wasu yara su ukku suka shigo da kaya nik'i nik'i suna jibgewa "baki washe yace"mommy su yaya shariff ne da salma suka zo yi muku sallama" wai America da saudiyya zasuje"bara naje mu kwaso sauran kayan.....✍️

wannan book d'in na kudine ! idan kina buk'atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

❤‍🔥 *MISKILI NE*❤‍🔥

*75&76*
Chapter 50 · 0% Book details