Sashe 51
Miskili Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
.......duk yadda amaan taso mutumin nata yatashi yabita suje suci abinci k'iyawa yayi"saima yakoma mata sak sharrif d'insa nada"sudai sadeeq da abdallah kallonsu kawai sukeyi suna dariya"sosai amaan ta k'ule saidai bata tanka kowaba ta koma kan kujerah ta zauna tana danna waya, sharrif kuma yana satar kallonta sbd dama so yakeyi ya ganta cikin irin wannan yanayin tafi masa kyau"wai yaya baraka tashiba sbd anty amaan?"cewar sadeeq"kaga mlm ba'a shiga tsakaninmu inama ruwanka?"murmushi yasub'uce mata ta kalli sadeeq ta masa gwalo tana tashi tsaye sharrif yabiyota suka wuce dining area"salfad! uhmm ba gida zamu koma ba?"toni me zaka mun idan mun koma?"kinfi kowa sani yarinya" ya k'are maganar yana ja mata kujerah ta zauna shima ya zauna gefenta"abinciccika masu rai da lafiya na gargajiya dana zamani gasu nan"amaan ta zuba musu sunataci suna santi "sai tsokanarta yakeyi, sadeeq da abdallah da ammi nata kallonsu daga nesa"bayan sun gama yatafi masjeed shida abdallah sbd ankira sallar azahar"ita kuma amaan tabi ammi d'aki sukayi tasu"bayan sun gama ammi nata kallonta sbd ba k'aramin kyau da canzawa taga tayiba"hak'orin makkan data sa yamata kyau sosai"ita kuwa kunya dukta kamata sai taga kamar cikin ammin ke kallo"na d'auka kota can adamawa zaku wuce kafin daga can kuyo tanan....itada zuwa adamawa sai bayan ta haihu insha allah "cewar shariff ko ajikinsa daya shigo ya tsintsi maganar"to allah ya sauketa lafiya"cewar ammi daga haka tayi shiru"yayinda amaan batace komai ba saima mik'ewa tsaye tayi tace"ammi bara nakoma parlourn "wanda tayi hakanne sbd ta basu waje su gana"kuma hakan yak'ara mata mutunci wajen ammin "bayan ta fita shariff ya zauna kan sofa yana shafa kansa"dama inason muyi wata mgn dakai"to ammi ina jinki" kaga yanzun dai idan madeenah ta k'are karatunta za'a sa musu rana da sadeeq "inaso kafin ayi auren nasu nima nayi nawa auren.... atake fara'ar dake saman fuskar shariff ta b'ace b'at"yayi kicin kicin da fuska yana fad'in haba ammi! wane irin mgn ne haka?"bayan bani nan wani ke zuwa ko?"kin manta abinda alh yahaya yaso yamana ne?"dama nasan zakayi wannan tunanin "ba wani bane alh kabiru ne abokin mahaifinku....wannan ai cin amanane ammi"yana abokin mahaifinmu zaice zai aure ki? ya katseta fuska bbu walwala"raya sunar manzon allah s a w d'in shine cin amana sharrif?"wuce nayi auren nayi ne kome?"to bari kaji! na riga na gama mgn sbd na shawarci y'an uwana "ban sanarwa sadeeq da abdallah ba na bari saina fara yimaka mgn"sbd nasan zab'inka shine nasu"idan sbd gidan mahaifinku d'aya zama naku ayanzun"har nike zaune ciki kuke tak'ama saina bar muku gidanku naje gidansa wata tsiyar ce"sbd ina lallab'aku shiyasa kukeyin abinda kukaga dama bama kamar kai....sosai gaban sharrif yafad'i yana tunanin kodai alh kabiru bebar ammi hakaba"sbd k'aramar mgn sai fad'a take masa haka...idan baza kayi mgn ba tashi kabani waje" kaje kaja matarka kubar min gida....yanzun ammi sbd y'ar wannan maganar har ranki zai b'aci?"babu komai aure daine ko?"allah yasa alkhairi bana fatan abinda zai saka kibar gidan nan har abada"idan na miki laifi sbd maganar auren kiyi hak'uri "yana fad'in hakan yamik'e tsaye yabar d'akin kamar zai tashi sama"gaba d'aya kuma ammin sai taga kamar bata kyautaba"sharrif na fitowa amaan ta kallesa"atake ta fahimci ransa ab'ace yake"ko mgn be mataba saidai hannunta yakama ya d'auki hand bag nata da wayarta dake gefe yayi hanyar k'ofa da ita"sadeeq da abdallah suka bisu da kallon mamaki"sanin halinsa na zafin zuciya yasaka tabishi da yadda yakeso batare data tankaba "koda suka iso parking lot da hannu yayima driver mgn"kafin ya bud'e motar yasaka amaan sannan ya zauna kusa da ita"ta kwanto ajikinsa batare data ce komai ba ...har suka iso gida babu wanda yace uffan"ko wane da irin kalar tunanin dayakeyi"sharrif yayi dana sanin dawowa k'asar inda yasan b'acin ran dazai samu kenan daba yanzun zasu dawo ba"duk ma'aikatan gidan sunata k'ok'arin gaishesu amaan ta sanar musu suyi hak'uri agajiye suke"shidai uban gayyar be tankaba yana dai rik'e da hannunta suka wuce babban parlourn gidan mutum ukku na biye dasu d'auke da tsarabar da sukayi"ko ina share goge k'al dashi"bayan sun ajiye suka fita"amaan dake zaune gefensa ta kama hannunsa guda ta fashe masa da kuka"yabita da kallo da idanuwansa da sukayi jajir"ya zare hannunsa guda datake rik'e dashi yakai saman bakin ta data b'are ya rufe mata bakin yana girgiza kansa had'e da yimata nunal d'in menene?"bakai bane kaketa fushi daga dawowarmu"pls nidai hamma kayi mgn mana konaji sanyi cikin zuciyata"yaka mata kasanar mun meke damun ka ?"amaan fad'in bashida amfani"tunda aikin gama yagama"nasan kinsan alh yahaya da y'ar sa iftihal wanda ammi ta aura?"eh nasan komai"to yanzun wani abokin abban mune yakeso ya aureta na nuna bana so shine ranta ya b'aci"banaso na zama sanadin b'acin ran mahaifiyata amaan "yah salam! to hamma cewa kayi baka amince ba har tayi fushi?"uhmm"kayi hak'uri ka koma yanzun kasami sadeeq da abdallah kununa mata kun amince"sannan nasan kasan beda matsala wanda zata aura d'in ko?"k'in mgn yayi"amaan ta girgiza kanta ahankali tace "hamma ammi fa bata wuce aure ba"ka barta tayi abinta ta sami ladar"kuma zai k'ara mata mutunci wajen idanuwan jama'a "pls salfad kaje ku bata hak'uri kaji ko? ta fad'a cikin rarrashi had'e da kwantar da murya"ya d'auki kusan second 5 kafin yace" to idan nadawo meye zaki bani?"kaina gaba d'aya zan baka nawan"kyan alk'awari?"tana murmushi tace cikawa"ta k'are maganar tana jan hannunsa saiya fisgota ta fad'o saman jikinsa ya rungumeta itada cikin"murya can k'asa yace"pls inaso na gaisa da baby nah salfad"tunda ajiyarsa ta fara bayyanah ajikin ki kike wahalar masa da daddynsa ko?"nidai kaje kadawo pls"shikenan tunda korata akeyi" dama mun had'u da wata y'ar budurwa a face book kinga sai naje wajenta.....be rufe bakiba ta juyo ta ballo masa harara tana turashi"yasaki guntun murmushi yana fad'in wasa nake salfad"amarya kuma uwar gida agidan fahad shariff keda kishiyasa har abada insha allah"kin isarmun da komai habibaty"k'ank'amesa amaan tayi cikin jin dad'in kalamanta "daga k'arshe suka fara kissing d'in juna"da k'yar ta samu ta lallab'a shi yatafi"ita kuma ta wuce saman su inda bataba masu aiki damar zuwa ba"da kanta ta gyara sashensa dana ta"sannan ta shiga wanka "tana fitowa ta sami shariff kwance kan bed dagashi sai d'an guntun boxer"suna had'a ido ya d'age mata gira "harka dawo?"eh salfad"kinsan meya bani mamaki?"uhmm uhmm"bayan mun gama rarrashinta sai cewa tayi nasan sharrif amaan ce ta turoka ko? nace eh cikin mamaki"sai cewa tayi allah yayi mata albarka hak'ik'a kayi dace"kaima sadeeq allah yasa madeenah ta kasance irin haka"kai kuma abdallah allah yabaka ta gari"amaan na murmushi tace"ameen ameen"to y'an mata sai azo a sauke alk'awari ko?"sallah fa zanyi hamma"kumafa nidai saida dare ko?"ta k'are maganar cikin shagwab'a "kinsan allah kije kiyi sallarki tun kafin nazo na karya miki alwallah"sanin halinsa k'aramin aikinsa ne yayi fin hakan yasaka tayi shiru ta nufi gaban ward rope ta d'auki doguwar riga da hijab"bayan tasaka ta kabbara sallar"tana sallamewa ta zauna zaman yin azkhar "tana cikin yin azkhar d'in saidai taji sharrif yayi sama da ita"daga ita har cikin yanufi saman bed"tanata kukan shagwab'a daga haka komai yaci gaba da wakana...... kwanci tashi asaran me rai! yau da gobe batabar komai ba"rayuwa ta lula"amaan suna rayuwa me dad'i ta hanyar zuba ingantacciyar soyayya da kulawa da juna dukda dai wata ran akan sab'a"tuni ammi tayi aurenta"alh kabiru tsakanin sa ga allah ya aureta "yanada mata guda da yara 5"gefe guda kuma ansaka ranar auren madeenah da sadeeq wata biyar masu zuwa"yayinda daddy ya yafema anty zabba'u saidai yace"babu batun maida ita d'akinta"yanzun babu laifi mommy na kulawa da yaran"zancen da akeyi ma ansaka ranar auren shamsiya itada nasir sbd yasaki waccan matar tashi"shima hamma yusuf ansaka masa rana"kuma abin farin ciki duk wata gudane za'ayi harda nasu madeenah.... amaan me juna biyu ta tabbatar abinda ke cikin cikinta d'an gata ne gaba da baya"sbd kowa zancen cikin yakeyi"ammi ta tanaji komai na haihuwa"ada sharrif yace banan zata haihu ba"ammi ta hana tace"idan ta tashi yin haihuwa ta biyu ko inama zasuje suje batada matsala"amma haihuwar fari anan gida nigeria zata yita.....ayau yakama week end babu office"tun wayewar garin safiyar yau amaan takejin jikin nata sai ahankali daurewa kawai takeyi"sbd ko yaya tace batajin dad'i zakiga sharrif yadamu ya lailayeta sun tafi asibiti"sadeeq kuwa kullum sai yazo gidan yadubata ko bata magani ko tambayarta yatakeji?abdallah kuwa idan bashida lactures zaizo yayi zaune yana bata labarin yadda zasu dinga wasa da yaron da zata haifa musu"sbd shi namiji yakeso ahaifa"sadeeq da amaan da shariff duk y'a mace suke so"kuma sharrif ya hana aduba musu meye zasu haifa"yanzun haka dai sadeeq yace"idan namiji ne zai bama abdallah million guda"shi kuma yace "idan macece zai masa wanki da guga na shekara guda"shidai shariff da amaan dariyace tasu.... abubuwan basu ida dagulewaba saida sharrif yabuk'aceta"sbd wannan cikin baya hanashi yayi budurinsa son ransa ajikinta"wajen k'arfe 12:30pm ciwofa yafara cin k'arfin amaan "sharrif dake zaune gefenta yana danna mata k'afafuwan ta yace" yaya dai salfad?pls hamma marata ke ciwofa,kuma abinda ke cikin sai motsi yaketa yawan yi... ai muje asibiti kawai salfad"kinga dama saura 3days edd naki yacika"yafad'a yana tashi tsaye yatai maka mata ta tashi suka wuce wani d'aki "duk abinda zasu buk'ata sharrif ya had'a cikin wani babban troley kafin su fito yakira masu aikinta yace suje zasu fita.....lokacin da suka shigo cikin mota abin yak'ara k'arfi addua kawai amaan keyi"arud'e sharrif yakira sadeeq yasanar masa yaje asibintinsa yanzun gasu nan isowa amaan ke labour" kuma yasami doctors mata babu wani namiji ko yarinya nurse da zata duba masa mata"yana gama wayar dashi yakira ammi"tasanar masa su had'u can"suna isowa sharrif beyi wata wataba ya d'auki amaan yashige labour room d'in da ita"kasancewar sadeeq be isoba amma yayi waya"sai masifa sharrif keyi cikin labour room d'in yak'i fita wai agabansa zasu dubata"saida ammi da sadeeq suka iso suka masa mgn sannan yafita"itama ammin fitowa tayi itada sadeeq tana bashi baki sbd sai safa da marwa yakeyi yayi uban gumi"bayan sadeeq yatafi office"suna tsaye sukaji sallama"ammi ta juyo ta amsa sallamar wata mace tana tsareta da ido sbd taga kamar ta santa"matsowa tayi ta duk'a gaban ammin ta fashe da kuka tana fad'in nice ibtihal ammi"nasan bazaki ganeniba sbd rama da duhun danayi"hak'ik'a duk wanda duniya tayi galaba kansa ya aureta har yayi sharholiya acikin ta"tofa yayi