← Book details Miskili Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 54

Sashe 17

Miskili Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

........ sheriff yabi bayan ta da kallo yana tab'e baki "k'asan zuciyarsa yana jin dad'in zaman Alh yahaya da mahaifiyarsa da yazo k'arshe....hamma! siririyar muryarta ta katse masa tunani"ya zuba mata mayatattun idanuwansa beyi mgn ba "d'an daburcewa tayi tana kauda kanta cikin b'ata fuska tace"ka bani pls"meyasa dole sai ta jikina kikeso?"yafad'a kamar bashine yayi maganar ba"to Ai banida ita kuma sanyi nakeji"shiru yayi ya k'yaleta"ganin bema da niyar mgn"kawai saita mik'e tsaye da nufin ta koma d'akin Ammi tayi zamanta....Ina zakije?"batare data juyoba tace"wajen Ammi mana"bakyason na baki suwaitar ne?"toba kak'i bani ba hamma"saida yad'an numfasa cike da basarwa yace"zoki Amsa"juyowa tayi tadawo gefensa ta zauna tana kallon yatsun k'afarta daya take d'azun"sai turo pink lips nata takeyi tana b'ata fuska"duk shariff na lura da ita ta wutsiyar Ido"saidai taji ya azo mata suwaitar me masifar k'amshin turarensa Asaman jikinta batare daya furta komai ba "saidai kafin ta juyo ta kallesa ya mik'e yabar wajen"saida ta hamgosa yana hawa stars"ta kauda kanta tana lumshe Ido sbd jin dad'in k'amshin da suwaitar keyi..... Amaan! da sauri ta ware lumsassun idanuwanta taga Abdallah tsaye yana kallonta"hararar sa tayi"murmushi yasaki yace"kije inji Ammi"in kinyi hak'uri fitama wajen ball zanyi"yafad'a yana kallon suwaitar dake a hannunta"bata kulashiba ta mik'e tsaye ta Aza suwaitar saman kayan jikinta....wow! Anty Amaan kinada kyau sosai wlh"harma kinfi yaya shariff kyau nake gani"kai kuma waye kafi kyau?"wannan mugun yaya sadeeq d'in mana"wanene haka?"nan gidan yake yana can london karatu, yakusan dawowa kin gansa can"yafad'a yana nuna mata k'aton pics nasu su 5"wanda b'ata tab'a lura dashiba sai yanzun daya nuna mata"Abbansu ne da Ammi,sai shariff da sadeeq da Abdallah"pic d'in zaiyi kusan 5yrs da d'aukar sa...kunyi kyau "shine Abinda ta fad'a tana d'aukar d'an kwalin shaddarta da shariff ya Ajiye mata kayanta yanzun yabar wajen"Abdallah dai yanata kallonta yakuma yima Ammi tambayar duniya kan ta sanar masa wai Amaan Acikin danginsu take ko kuwa ya Alak'ar su take da ita??.... Amma tak'i sanar masa"ransa na bashi kodai soyayya sukeyi itada yaya shariff.... Anty Amaan! yadakatar da ita tana k'ok'arin shiga bed room d'in Ammi "wai kinada k'anwa ne?"juyowa tayi suka had'a Ido...you are very stupid! yaji kakkausar muryar shariff tana dukan dodon kunnansa"Aguje yabar parlourn batare da yayi gigin kallon gefen da shariff d'in yakeba"Amaan ta juyo ta saci kallon sa"ya canzo suwaitar wacce tafi wadda yabata kyau"kuma irinta dole sai maza ke sanyata"shi kuwa kallon second 5 yamata ya d'auke kansa yana yin kicin kicin da fuska "kai hamma meye kuma nayi kaketa hararata?"tamkar bazai tanka mata ba can yatab'e baki yana fad'in kinfi kowa sani"idan kin gadama ki sameni A parking lot nanda mintina 5 ,idan kika wuce hakan karma kiyi wahalar zuwa"sbd kokin je bazaki sameniba"daga haka yayi hanyar k'ofa yana takawa cike da aji had'e da kasaita"ya zura hannunsa guda cikin Aljihun wondonsa gudan hannunsa na rik'e da waya"Amaan tabisa da kallo kafin ta wuce d'akin Ammi"tana zaune gefen bed tana waya da yaya sadeeq"tana ganin Amaan ta fad'ad'a fuskarta da fara'a tana fad'in zan kiraka daga baya sadeeq"inye y'ata kinyi kyau"murmushi tayi irin na yara"to yanzun ya Amince zai kaiki ko?"Eh Ammi yace" na samesa parking lot kar in wuce mintina5"okay to maza d'aura d'an kwalin "batayi mgn ba ta matsa gaban mirror tayi d'aurin ture kaga tsiya"ta yafa mayafin kan kafad'arta,kafin ta d'auki sabuwar hand bag nata da takalmin ta saka"Ammi daketa kallonta ta mata Allah yatsare ta fita"sauke Ajiyar zuciya tayi tana tunani indai Amaan ta wuce wata guda bata warkeba,to dole zasu saka cigiyarta A kowane state ko Allah yasa Andace da iyayenta"sbd ta fahimci shak'uwa me k'arfi na k'ok'arin shiga tsaninta da kowa na gidan"sannan kuma gefen zuciyarta tana mamaki da al'ajabin irin yadda shariff yafara canzawa kan Amaan"tana tsoron karya yafara sonta idan tadawo hayyacinta tace bata sonsa"dukda tasan d'anta ya wuce wata y'a mace ta ganshi tak'isa"idan kuma har Amaan batace bata sonsaba"zata iya yuyuwa ko iyayenta sun mata miji matsalar nan tazo ta gifta"wata zuciyar tace" kibisu dai da addua....tunda ya iso parking lot d'in driver ya iso Asukwane gabansa"da hannu yasanar masa baya buk'atarsa"kafin yanufi gaban motar dake goge k'al ya shiga.....yana k'ok'arin rufe k'ofar kiran mus'ab ya shigo cikin wayarsa"yaja tsaki yana d'auka beyi mgn ba"Abokinah kana jina?"da k'yar shariff yace"uhmm! zamu iya had'uwa yanzun?"ah ah"meyasa ?"zamu fita da Amaan ne"mamaki sosai mus'ab yayi"saidai yasan halin shariff baya k'arya iya gaskiya yake fad'a koda kuwa meye zai faru"shariff na kok'arin kashe wayar mus'ab yace"pls ka hak'ura da fitar mu had'u mana"wai menene?"kan cases d'in nan ne"pls mus'ab kasan ba any time nake kasancewa Ina Aiki ba ko?so pls idan kadamu dakoma miye bayan sallar isha'i kasameni Agida"daga haka ya yanke wayar "Adaidai lokacin kuma ya hango Amaan tana nufo wajen cikin nutsuwa"ita kanta tafiyar tata Abin kallo ce"saidai da Alama kamar tunani takeyi"d'auke kansa yayi ya danno mata uban horn"da sauri ta kalli sashen da motocin suke"Anan ta lura da motarsa"tunawa datayi d'azun yace"waye driver d'inki? yasaka kai tsaye ta nufi front sit ta bud'e ta shigo da sallama"saidai batayi masa mgn ba "Anutse yaja motar yana kunnah karatun Alkur'ani me girma"Amaan ta lumshe Ido tana saurere"shidai yana driving d'in sa Anutse"saidai miskilin ko a bece mataba tunda ta shigo cikin motar"bayan sun iso *mmn khadija beauty saloon* yayi parking gaban shagon"ya kalleta ganin idanuwanta arufe yasaka yakashe karatun"da sauri ta bud'e idanuwanta suka sark'e da nashi "itace ta d'auke kanta da sauri"shi kuwa be dena kallontaba murya Akausashe yace"zamuje ciki bance bayan kin gaishetaba ki koma mgn"dato ta Amsa suna fitowa suka nufi bakin k'ofar shagon"shariff ya matsa yayi knocking,matar tazo ta bud'e suka gaisa"kasancewar ta sanshi yana kawo Ammi "gata nan Amata gyaran gashin daya dace"daga haka ya juya zai tafi, Amaan ta toge tak'i bin matar"yallab'ai tak'i zuwa fa"juyowa yayi ya kalleta"ta shagwab'e fuska tana fad'in nidai hamma bazaka tafi ka barniba bayan ban sansuba"rasa meye zaice mata yayi"yana dai ta kallonta kawai"kinga Amota zai tsaya yajiraki"muje Amiki kar yamma tayi"daga haka taja hannun Amaan suka wuce ciki "shi kuma yakoma mota yaja yabar wajen.....sosai matar tayi mamakin yawa da tsayin gashin Amaan"steaming tayi mata"bayan Angama Aka d'aure matashi"sannan Aka mata wankin k'afa "wanda bece Ayiba kawai dai matar tayi mata sbd tana zaton budurwarsace ita"sai gab da magrib Aka gama "Ahaka kuma shariff ya musu knocking"kinga gama ya nan yadawo ko?"nok'e kafad'arta Amaan tayi tak'i mgn balle ta tashi"matar na dariya taje suka gaisa yabata kud'in da shima bai san ko nawa bane yana fad'in tana Ina?"k'ilan saika shigo ta taso yallab'ai dan tayi fushi"had'e rai yayi yana tura k'ofar yad'an zuro kansa ciki ya kalleta"ta kauda kanta ta sunkuyyar"ya tab'e baki murya bbu wasa yace"idan kika bari na shigo ciki saina b'ata miki rai"yana fad'in hakan yajanye kansa yayi gaba"tanata turo baki ta taso ta fito"matar na mata dariya"koda ta shigo cikin motar batayi masa mgn ba"yana k'ok'arin tashin motar Ammi ta kirashi"badan yasoba ya d'auka yana fad'in Ammi gamu nanfa Ahanya zan maidota"sai kuma yace to yana yanke wayar"hamma ! kasan ko?"harda wankin k'afa tamun"na tambayeki ne?"sosai taji haushin maganar tasa saita sharesa"har suka iso gidan bata koma tankashiba.....bayan sallar isha'i shariff yashigo cikin parlourn "yana sanye da jallabiya da hula pasincap da suwaita Ajikinsa"hannuwansa duka na zube cikin Aljihun suwaita d'in"fuskar nan tasa A d'aure tamau" cikin shan k'amshi yayi sallama" Amaan na ganinsa ta tashi tabar parlourn"d'an cije baki yayi ya zauna gefen kujera zuciyarsa na tambayarsa fushi yarinyar nan keyi dashi kome?"be gama wannan tunanin ba yaji muryar Ammi tace"Akawo maka coffee d'in?"Eh Ammi "batace komai ba ta tashi ta wuce kitchen"bayan ta had'a masa ta fito dashi tadawo parlourn ta mik'a masa"cikin rashin sa'a daya Amsa cup d'in yasub'uce masa yafad'i yadaki center table ya fashe...kwalbar ta soki d'an gefen d'an yatsan k'afarsa babba,saiga jini na fita.... innalillahi wa inna ilaihir raju'un! wannan shi ake kira tsotsai"cewar Ammi tana nufar d'aki da sauri sbd ta d'akko masa cotton da hydrogen"tana zaton idan yayi Amfani dasu k'ilan jinin ya tsaya"Amaan na kwance saman bed d'in rub da ciki"kayan baccine Ajikinta riga da wondo masu sulb'i,sai suwaitar shariff data Aza saman kayan"yadda taji Anturo k'ofar ba'ayi sallama ba yasaka tayi saurin tashi zaune tana kallon Ammi data shigo ta nufi gaban mirror"Ammi! na'am Amaan"wlh kinga yayan kune yaji ciwo jini nata fita....bata rufe bakiba Amaan ta duro daga saman bed d'in ta fita da sauri kanta bbu ko d'an kwali"saidai kawai shariff daya lumshe idanuwansa yana jin rad'ad'in ciwon ya ganta gabansa tana hawaye tana fad'in" hamma nah! meye yaji maka ciwo ?"sannu! bara na dafe maka wajen kar jininka yak'are"ta fad'a tana kuka had'e da kok'arin dafe masa gefen yatsan"shariff dake kallonta da tsantsar mamaki ya janye k'afar tasa gefe da sauri, yana girgiza mata kansa beyi mgn ba "hakan yayi daidai da isowar Ammi"bayan ta mik'a masa ta kalli Amaan tana fad'in kukan meye kikeyi?"ba hamma bane yaji ciwo"Ammi na murmushi tace"bansan zaki damuba daban sanar miki ba Amaan"ta fad'a tana tsintse glass cup d'in daya mutu tabar parlourn "shariff kuwa Anutse yazuba hydrogen d'in jikin cotton yashafa Asaman ciwon"sai gashi ya tsane jinin kuma yatsaya"Amaan dai na duk'e gabansa tana kallon yatsar"Ahaka yaji sallamar Abdallah"yabi gashin Amaan da yaji gyara da kallo"kafin ya zare pasincap d'in dake saman kansa ya aza mata saman kanta da sauri yana fad'in taso kidawo nan ki zauna"to hamma kadena jin zafin ?"kansa kawai ya gyad'a mata "yah Allah kabama hamma nah lafiya! ta fad'a tana d'aga hannu sama"shi mamakinta kawai yakeyi"be tab'a zaton zata iya kuka sbd shiba"saiya kalleta murya can k'asa yace"keda kike fushi dani shine harda yin wani kuka sbd naji ciwo?"toba na hak'ura bako?"kumafa lafiyarka ta fimun komai mahinmanci hamma"sosai yaji kalamanta na dukan zuciyarsa yana kallon ta babu ko k'iftawa"dan wannan kalmar tata ta wuce ace yarone yayita....yaya shariff kanada bak'i suna a parlourn bak'i "okay yafad'a yana kallon Amaan"kamar bazaiyi mgn ba can yace"tashi kije ki kwanta"ki kuma saka hula ko d'an kwali"to hamma ka bani wannan hular?",kansa yagyada mata"sai kuma tace"to yajikin naka?"nifa Amaan lafiyata qlau"yafad'a yana kallon gefen da Abdallah yake"yaga su yake kallo"harara ya watso masa yana mik'ewa tsaye "itama Amaan saita tashi tsaye ta nufi d'aki"shariff kuma yafita waje"sai wajen k'arfe 10:11 pm yadawo ciki"bbu kowa a
Chapter 17 · 0% Book details