← Book details Miskili Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 54

Sashe 4

Miskili Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

saura page 1 free Page yak'are maza ki biya naki kar Ayi Babu ke👇🏼

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

❤‍🔥👨🏻‍💻 MISKILI NE🧑🏻‍💻❤‍🔥

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written
by mommyn fareesa

last free page 9&10🙌

.........Cak ! Amaan ta tsaya ita bata juyoba ita bata tafi ba"shariff yatab'e baki yana zare takalmin k'afarsa sawu ciki"ak'ule yakoma fad'in saina maimaita miki kizo ne? yafad'a batare daya kalletaba"Ahankali ta juyo idanuwanta cike da kwallah tana fad'in hamma bazaka doke niba?zancen kikeso"kika sake kikamun kuka ko ihu wlh sai ranki yab'aci"yak'are maganar agundure yana yimata kallo d'aya ya d'auke kansa"ita kuma Atsorace ta iso nesa dashi ta zauna kan carpet"jin yayi shiru beyi mgn ba yasaka ta d'ago kanta ta zuba masa fararen kyawawan idanuwanta saman had'ad'd'iyar fuskarsa"cikin shagwab'abbiyar murya tace"hamma gani! banza yamata saida ya gama shan k'amshinsa batare daya kalletaba yace "daga yau kika koma ganina kina wani ihu ko rawar jiki rankine zaita b'aci"meyasa bakya jin mgn ne?"and last one ki dinga zama kanki da d'an kwali "karki yadda nasamu gashi koda guda d'aya ne a cikin parlourn nan"ya furta da k'yar yana jan tsaki sbd ganin ta rufe Ido tana hawaye....Atsawace yace"tashi ki bani waje"ni ciki nah ke ciwo Ai"d'an jim yayi k'irjinsa na bugawa yana fatan Allah yasa ba period zata yiba"saidai miskilin bece mata komai ba"tafi mintina 5 zaune daga ita saishi Acikin parlourn babu kuma wanda ke mgn cikin su"shi yatashi tsaye yanufi upstairs"tana ganin yabar parlourn ta turo baki irin na yara tana hararar bayansa ta tashi ta wuce d'aki ta kwanta"har baba ladi ta gama Abinda takeyi a kitchen ta dawo d'akin Amaan na saman bed kwance tanata juye juye taci kuka ta godema Allah"Amaan ki tashi muyi sallah ko?"ni bazan iyaba cikinah kemun ciwo"Ashsha! sannu kinji?"Amma kidena kuka kinjiko?"kasa mgn Amaan tayi ta rufe Ido tana koma dafe cikin"da k'yar baba ladi tayi sallah ta fito main parlour jiran shigowar shariff sbd tasan yana masallaci"be kuma shigo gidan ba saida aka gama sallar isha'i"ya shigo da nufin yayi musu sallama yatafi gidan Ammi"yasha brown d'in jallabiya sai shek'i kyakykyawar fuskarsa keyi"Amsa sallamarsa kawai baba ladi tayi ko gaisuwarsa bata Amsaba tace"Amaan fa batada lafiya"ciwon ciki ne ke damun ta"Ina zaton kamar Al'adanta ne zaizo....saida yad'an yatsina fuska yana daga tsayen cikin nutsuwa yace"ta fad'amun d'azun Amma na d'auka shirmenta ne "ah ah gaskiya da gaske ne, tanama can sai kuka takeyi nayi rarrashin nagaji Amma tak'i yin shiru"bece komai ba yanufi d'akin....tana kwance saman bed sai shure shuren k'afafuwa takeyi ,idanuwanta jage jage da hawaye"ta dafe k'asan mararta"gashin kanta yabaje saman pillow"kallo d'aya shariff yamata ya d'auke kansa yana mamakin wannan wane irin gashi ne da ita?"sai kuma yaja k'aramin tsaki yana jingina jikinsa Ajikin bango"cikin k'asaitacciyar muryarsa yace"tashi kimun bayanin meke damunki?...da sauri ta tsaya da shure shuren k'afafuwn data keyi"takuma dena kukan"saidai bata tashi zaune d'in ba"ta bishi da kallo da jajayen idanuwanta.....wai hamma nah kai baka yin dariya ne?"ta fad'a cikin sub'utar baki "da mamaki yazuba mata manyan Idanuwansa yana tab'e baki had'e da cewa"gulma zaki tsaya yi ko fad'amun Abinda ke damunki zakiyi ne?"saita kauda kanta tak'iyin mgn"sosai tabashi haushi yaja tsaki yadoka k'ofar da k'arfi bayan yafita"itadai baba ladi na kallonsa bata yi mgn ba"zuciyarta nada tarin tambayoyi sosai game da fahad sharif....Aharaban gidan ya tsaya yakira Abokinsa Dr Mansoor "kasancewar yasan beda matsala yamasa bayani Atak'aice k'anwarsace da suke zaune da mahaifiyarta Agidan sa bbu lafiya"Dr Mansoor yasanar masa nanda mintina 15 zai iso"bayan yagama wayar yayi shiru yana tunani yana jan tsaki"yana nan zaune Dr Mansoor yakirashi yana daga waje"okay ka shigo ciki get d'in bud'e yake"daga haka ya yanke wayar yanufi main parlour"babu kowa,hakan yasa yanufi k'ofar d'akin "tun kafin yashigo yaji muryar baba ladi na rarrashinta tanata kuka"yaja gajeran tsaki yana jin haushin Amaan "adak'ile yayi sallama sau biyu ya shigo"Amaan na ganinsa ta nutsu"wata uwar harara ya watso mata fuskarsa Ad'aure yace"ga likitah nan zaizo yadubaki kisanar masa dame dame ke damunki?"zai rubuta miki magungunan da suka dace"tunda kinfi k'arfin niki gayan meke damun naki"to shikenan bara na fita saiya shigo"cewar baba ladi tana rab'awa gefensa ta fita"shi kuma yanata cin magani kamar yana jiran ta fita"murya aka
usashe yace"bayan kin bashi Amsar Abinda ya tambayeki naji kinyi wata mgn sai ranki yab'aci "daga haka shima yafita"Amaan ta kwab'e baki tana sauka daga saman bed d'in,ta tsaya gaban ward rope da nufin ta d'akko d'an kwali....hakan yayi daidai da shigowar fahad shariff da dr Mansoor!uban gayyar ne Agaba yanata faman shan k'amshi yashigo da sallama"bata Amsaba ta juyo suka had'a Ido da Dr Mansoor wanda tunda yashigo ya kalli bayanta cikin second 10"saida yayi sumar tsaye"tambayar kansa yakeyi balarabiya ce ko kuwa wani yarece itah??....hamma ! d'an kwali nah zan d'auka"banza yamata kamarma badashi takeba"yayi tsaye gefen mirror"yana lura da yadda Dr Mansoor keta kallonta"ita kuma bayan ta d'akko d'an kwalin ta yafa saman kanta ta zauna gefen bed d'in batare data koma mgn ba"tayi k'asa da kanta tana kallon carpet"gaba d'aya jitakeyi sharif yacika wajen.....sannu ya jikin naki?"pls mlm ba wannan ba kayi Abinda yakawo ka mana"cewar shariff fuska bbu walwala"Dr Mansoor yayi d'an murmushi ya zauna kan bed side drower yana fad'in dame dame ke damunki?"yafad'a yana tsurama baby face nata Ido"ransa na bashi kodai jinsin larabawa ce ita, ko kuma cikakkiyar bafulatana ce"ciwon ciki,da ciwon kai nakeyi sai kuma.....sai tayi shiru"sheriff duk na saurare azahiri"Amma a bad'ini zaka d'auka kamar besan meke faruwa ba ku kuwa babushi acikin d'akin....sai Ina?"turo baki tayi tak'i mgn"haka nan kuma ta tsintsi kanta dak'in son ta kalli Dr Mansoor da shi kuma gaba d'aya idanuwansa na kanta"karki damu nasan ciwon mara ke damunki ko?"shiru tayi dan bata gane inda yadosaba tunda ba'a hayyacinta take ba"shi kuwa ya d'auka kunya takeji shiyasa tayi shiru"mik'ewa tsaye yayi yana kallon fahad shariff yace"Abokinah dama duk month haka takeyi??"ya d'auki kusan second 5 kafin cike da izzah yace"pls muje Asiyi magani Abata tunda kaji Abinda ke damunta"daga haka yayi shiru yatashi tsaye yanufi k'ofa "Dr Mansoor ya kalleta cikin rashin sa'a suka had'a Ido"murmushi yasakar mata yafita"ita dai sai tayi kwance ta rufe Ido"kimanin shud'ewar mintina 20 baba ladi ta shigo cikin d'akin da ledar magunguna ,harda kwalin cartoon d'in pads"da taimakonta taci Abinci tasha magani"sannan ta sakata tayi wanka"bayan ta fito daga wankan ta kama kuka"waike Amaan meyasa kikeson bama mutane wahala ne?"meya faru kuma kike kuka?"to niba jini na gani ba a inda nakeyin fitsari"tashi zaune baba ladi tayi ta kama hannunta suka zauna gefen bed.....tafi mintina 20 tana yimata bayani yadda zata iya fahimta"sannan ta barta ta shirya ta kwanta bacci....
washe gari yakama friday misalin k'arfe 4:49pm"fahad shariff ne tare da body quards nasa da mus'ab suka shigo cikin had'ad'd'en garden d'in"kasancewar An sanar ma mus'ab ta waya fareedah na wajen itada k'awayenta"zazzafan wanka Shariff ya d'auka bana wasa ba"ya fito cikin suit red colour ta cikin black"agogo da takalmi duk black yasaka"sumar kansa zuwa kyakykyawan b'akin sajensa har walkiya sukeyi sbd gyaran da suka sha"yanata zuba wani irin fitinannan k'amshi,yayi kyau na musammun"shi kansa mus'ab yau ba k'aramin kyau Abokin nasa yayi masa ba"saidai fuskar Nan ta shariff bbu walwala ya d'aureta tamau"dan yau da safe Amaan ta bashi haushi....tunda suka doso wajen Aketa kallonsu"ko wace budurwa tana kallon shariff tana jin inama inama....nadiya tafara hango shigowar tasu shida mutanansa"da sauri ta zunguri fareedah dake zaune gefenta"wacce tayi nisa Atunani tanata zuk'ar sheesha"wanda tunda ta gansa q last time ta rasa nutsuwarta har zuwa yanzun tunaninsa takeyi"wai nadiya meye haka?"kalli can ki gani"da sauri fareedah ta kalli inda take nuna mata"zumbur ta mik'e tsaye! Ina zakije faree?cewar seerat da nadiya Atare"wajen shariff mana nadiya"wlh dakin kwafsa ma kanki"to Amma idan bata jeba kema kinsan dai bata Isa yazo wajen taba tunda MISKILE NE!cewar seerat tana kallon Nadiya"hakane Amma ki d'an zaunah muyi mgn"kinsan dai yanada super markets so nunawa zakiyi kina son zakuyi mgn kije ki siyi kaya da sauransu koba haka ba??"gaskiya Nadiya brain naki naja"cewar fareedah tana gyara zamanta sunata kitsa mata yadda zatayi.... Shariff da mus'ab kuwa daga nesa duk suna lura dasu"harda tashin da fareedah tayi tsaye"tunda Shariff yamata kallo d'aya yaji muguwar tsanarta Aransa" musammun daya lura da irin kayan dake jikinta"sai koma had'e rai yakeyi yana jin bazai ma iya zuwa wajentaba saidai ko yatura mus'ab "yayinda mus'ab d'in ke lura dashi"yana danne dariyarsa yace"Abokinah Ina Amaan shariff?"wani kallo yajefi mus'ab dashi beyi mgn ba "eh mana Amaan shariff"ko kuwa nace Ina Amaan d'in ka rigimammiya?"Ina fatan baba ladi na bata duk Abinda mlm yace?"banza shariff yamasa yak'i mgn"suna zaune Ahaka body quards nasa na tsaye su 4 daga gefe"fareedah ta iso wajen cikin yatsina had'e da kisisinah tayi sallama"mus'ab ne ya Amsa"dan uban gayyar ji yayi muryarta na bashi haushi "zan iya zama ko kuwa na tafi?"well duk yadda ranki yabaki zaki iya"cewar mus'ab yana d'age kafad'a Alamar ko Ajikinsa"sosai taji yabata haushi"sai bata nunaba taja kujera ta zauna"yayinda Shariff keta danne danne Awaya kamarma babu shi Awajen"tana binsa da mayen kallo tace"uhmm yallab'ai dama wajenka nazo Ina son mgn dakai"k'ok'arin sakin fuskarsa shariff yayi yana fad'in okay Ina jinki"murmushi tasaki tana juya idanuwanta tafara k'ora masa bayanin tanaso tazama costomer d'insa yabata contact nashi"card nashi kawai yabata"daga haka be koma mgn ba "pls kad'an bamu waje mana"ta fad'a tana bin mus'ab da kallon raini"shi kuwa wani irin shegen murmushi yasaki Aransa yace"wawuya zaku gane kuranku keda mugun ubanki"Afili sai yace"okay"daga haka ya mik'e tsaye yabasu waje"Ahankali tace"gaskiya naji dad'in yadda ka tarbeni"zuwa gobe da yamma zanje super market naka Ina fatan tunda week end ne zan sameka acan?"ya d'auki kusan second 5 kafin da k'yar yace"okay"Anutse tace"sunana fareedah isah tafashiya! na kammala karatuna a k'asar London"na had'a degree na kan political science"Masha Allah! shine Abinda yafad'a yana fatan Allah yasa daga haka karta koma mgn ta wuce"saidai adduarsa bata karb'uba, sai zuba masa surutu takeyi sama sama cikin sigar jan hankali"be cewa komai saidai ya saurareta koya d'an kalleta ya kauda kai"daga karshe da surutunta yakaisa mak'ura saiya mik'e tsaye yana duba Agogon dake d'aure Adamtsan hannunsa cikin taushin muryansa yace "sai Anjima"to pls zan kiraka da dare"kansa kawai ya gyad'a mata"yana barin wajen cikin tafiyarsa irin ta kas'aitatun mazan da suka Amsa sunansu maza"mus'ab da body quards nasa suka biyosa Abaya"dak'ile yace"mus'ab zan baka k'aramar wayata idan ta kira Anjima ka d'auka Amatsayin nine"kamar yaya?"kamar yadda kaji"yafad'a fuska bbu walwala yana shigewa back sit da'aka bud'e masa"bayan mus'ab yashigo yana kallon sa yace"kasan dai bazai yuyuba nayi waya da ita kasan dare ne Ina tare da noory nah"kuma bayan wannan kasan me iyali irin wannan lokacin yana can yana shan rab'a"irin ku tuzurai ne yaka mata suyi waya a wannan lokacin"yak'are maganar k'asa k'asa yana dariya"sbd yasan yakai Abokin nasa mak'ura "shi kuwa banza yamasa bece komai ba yanata yatsina fuska "yatabbatar bazai juri waya da yarinyar ba shiyasa yace mus'ab ya Amsa"yadda yakejin tsanarta idan yabari suna yawon waya zai iya yimata Abinda zai b'ata musu Aikinsu "da wannan tunanin suka iso office"bayan ya sallami yaransa suka wuce ciki shida mus'ab"wanda da k'yar yasamu mus'ab d'in ya yardabzaibAmshi wayar"Aikuwa yana komawa gida wajen 9 pm takirashi"kansa na saman cinyar matarsa ya d'auka cikin canza murya"fareedah taso taji kamar ba muryar Shariff ba, Amma giyar SO ya hana ta gane"sunfi mintina 30 suna waya daga bisani suka gama"wanda mus'ab ne yadakatar dayin wayar,Amma ita batak'i sun kwana suna waya ba"shi kuwa mus'ab yasan muddin Abinda suke zargi yafaru"Tofa fareedah tata tasameta, dan jinya biyu zatayi"jinyar zuciyarta data rad'ad'in rashin mahaifinta..."saidai be tausaya mata ba, sbd batada kirki akwaita da izgili da wulak'anta mutane....
Chapter 4 · 0% Book details