Sashe 18
Miskili Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
parlourn"matsawa yayi yafara knocking Abakin k'ofar bed room d'in Ammi"jin shiru ba'a yi mgn ba yasaka ya murd'a handle d'in k'ofar ya shigo"d'akin da haske"Amaan na kwance gefenta na dama"ta saka hula ga wacce yabata rik'e A hannunta da Alama wasa takeyi da ita bacci ya kwasheta "tsaye yayi yanata kallonta can ya matsa yatofeta da addua,kafin yaja devut yarufe mata jikinta.....yana d'ago kansa Ammi na fitowa daga bath room"sosai yaji nauyin ganinsa d'akin datayi"saiya basar yana shafa kansa yace"Ammi zanje Abuja da safe insha Allah "Akwai Abinda zanyi ne Acan"Amma ta jirgi zan tafi da k'arfe 8 na safe zan wuce"wani abu zakayi Acan?"gidan mai na dake a can Ake kok'arin rufewa"subahanallahi! to Allah yakare"ya Amsa da Ameen yafita....washe gari da Asuba daya dawo daga masallaci ya shigo gidan"Abin mamaki Amaan na zaune parlourn da dogon hijab Ajikinta "tana ganinsa ta mik'e tsaye tana fad'in hamma ya jikin?"shifa harga Allah yama manta da wani ciwo da yaji saida yaji tayi maganar....hamma dan Allah kamun mgn kodai Asibiti zakaje??"girgiza kansa yayi cikin sanyayyar muryarsa yace"Amaan bakya gajiya da shirme ko?"nifa daga masallaci nake"karki damu tuni na warke"to Ina kwana?"lafiya qlau "kije ki koma kwanciya kiyi bacci....kafin tayi mgn Ammi ta shigo cikin parlourn"shariff yaduk'a ya gaisheta"ta Amsa da kulawa tana kallon Amaan tace"dama nace miki kidena damuwa shida ciwon ke jikinsa kilanma ya manta"ka ganta nan tunda na tasheta taketa faman tambayar ka warke ciwon?"shinefa muna gama sallah tace mun zataje ta gaisheka"shariff dai na duk'e yana sauraren kalaman Ammi"wanda Azahiri zaka d'auka bema damuba"Amma Abad'ini mamakin yadda yarinyar ta damu dashi har haka yakeyi.....tashi muje ki d'an kwanta ko?"muryar ammi ta katse masa tunani"Amaan batayi mgn ba tadai kalli shariff da shima ita yake kallo"saidai shi suna had'a Ido ya d'auke kansa ....shima be zauna a parlourn ba "side nasa ya wuce yafara shiri"sai wajen k'arfe 8:5 am ya sakko down stairs d'in"yana ta zabga daddad'an k'amshin sa me kashe jiki"kallon second 3 yayima parlourn ya lura bbu Amaan Aciki "wanda saida yaji fad'uwar gaba daya tunata"kuma shi kansa besan meyasa yatunata d'in ba"yana sanye da k'ananun kayan da sukayi matuk'ar dacewa da kalar fatar jikinsa "yayi kyau harya gaji"dukda fuskar tasa kamar koda yaushe d'aure take"Ammi dai na kallonsa Aranta tace"mutum har mutum Amma yak'i Ajiye iyali"ita yanzun rashin k'inyin Auren nasa harya fara bata tsoro"koda sadeeq be sanar mata yana soyayya ba ta fahimci shi yafishi kula mata da sunan soyayya....ganin yazo ya zauna yanata danne danne Awaya yak'i yin mgn yasaka ta girgiza kanta kawai tace"kaje kayi break fast mana"No Ammi zanyi Acikin jirgi ne"iya Abinda yafad'a kenan Atak'aice"tasan ba mgn zai komayi ba hakan yasaka tace"Acan zaka kwana ko yau zaka dawo??"idan matsalar batayi yawa ba yau zan dawo"idan kuma da matsala sosai Acan zan kwana"to shikenan Allah ya tsare hanya yabada nassara Ai bama fatan matsala shariff"koda kadawo bamunan muna wajen suna na hafsat(y'ar k'anwarta) kamar bazai tanka ba sai kuma yace" keda waye zakuje?"da Amaan mana"tunda kasan ba skul ko islamiya take zuwa ba"haka nan yaji beson Ammin taje tare da ita"sannan kuma zuciyarsa nason jin Ina Amaan d'in take?Amma miskilancin sa yahanashi ya tambayata"mik'ewa tsaye kawai yayi fuska bbu walwala yace"pls Ammi ki barta gida"zuwanku da ita wasu zasuyita tambayar ita d'in wacece?"daga haka yayi shiru ya nufi k'ofa"kamar tace" ya jira Amaan tazo suyi sallama Amma sanin halinsa tana iya masa mgn yace A k'yale Amaan d'in yasaka ta barsa......lokacin daya iso parking lot harma body quards nasa da driver nasa sun zama on ready"cikin girmamawa Aka bud'e masa back sit yashiga"yana zama kiran mus'ab na shigowa cikin wayarsa"ya d'auka da sallama"Ina tayaka murna Abokinah bisaga nassarar dakayi wajen bincike"kaji dai Alh Isa yau Anyanke masa hukuncin kisa ko?"d'an tab'e baki yayi yace"ban saniba! Okay Ai yau Aka sanar A news d'in safe"okay"pls sheriff dan Allah kaduba lamarin da Dr Mansoor yake ciki game da Amaan ka tausaya masa"wlh yana cikin wani hali game da soyayyar yarinyar nan"sannan bana so na sanar masa ta yadda kasameta sbd idan nayi hakan sai naga kamar na tona Asirin kane......✍️