Sashe 8
Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gyale ko hijabi ki rufe jikinki, na ce tafxijam gidan nan ai gidanmu ne ni da su kuma ‘yan uwan juna ne, ubanmu xaya babu wani wanda zai zo ya saka mana dokoki don kawai yazo cin arziki ya samu shiga. Bai kula ni ba. Ina zaune a falo shima ya fito falon a dalilin shigowar da Sa’adatu tayi ta kawo mana abin karyawa, Mama ce ta aiko ta xan kununa a kofi da qosai guda uku qanana a takarda nashi kuma a wani kyakkyawan food flask an cika shi tam ga yaji a gefe ga kuma kununshi a wani kyakkyawan jug tare da kofin xiba asha, shima mai kyau. Na kawar da kaina gefe na ce hu’un, ai Babana kam kirkinshi yana da yawa, kowa yazo cin arziki gidan shi zai ci ya qoshi. Da sauri ya tambaye ni menene? Alamar bai ji abinda na faxin sosai ba, yana jin na soma kamo bayanin zan maimaita mishi sai kawai naji kau, ya warware hannunshi ya wanke ni da mari, ban tava zaton zai iya yi min hakan ba, don haka a kixime na qurma mishi ihu, yanda Sa’adatu tayi tsalle tayi waje a tsorace tun saukar marin da ta gani haka shima ya miqe ya tsallake komai ya fita ya bar min xakin bai sha kunun ba. Hannu biyu na saka na rungume fuskata tare da shafa inda ‘yan yatsunshi suka kwanta a gefen fuskata, can cikin zuciyata kuma faxi nake yi lalle mutumin nan ba qaramin artabu zamu yi dashi ba. Ya mare ni a gaban qanwata saboda baya tsoron kowa? Tafxijam, na sake jinjina abinda yayin cikin zuciyata, bai wani daxe ba ya dawo fuskarshi a xaure sosai nima na xaure tawa fiye da tashi ya ajiye kayan da ya shigo dasu kayan tea ne da kayayyakin amfani dangin su sabulu da omo da izal gami da detol. Sai kuma wani yaro da ya biyo shi da katon xin ruwan eva ya karvi tare da faxin yauwa Sadiqu ko ba Sadiqu sunanka ba? Yayi tambayar ta hanyar nuna alamar wasa ga yaron, ya buxe food flask xin ya dunbuzo qosai ya cika wa yaron nan hannu dashi sannan ya zauna yana karyawa sai da ya gama ya shiga ya shirya ya yi kwanciyarshi, sannan ya fito. Kwana uku a jere bana magana da Ado, bana ko kallon inda yake shima baya shiga harkata, zaman a haka ya xan fi min daxi da sauqi fiye da ranar kwananmu na farko, don haka na qudurawa raina ci gaba da daina kula shi. Rannan ya dawo da yamma yayi min sallama ban amsa ba, ya nemi wuri ya zauna maimakon yayi abinda yake gabanshi kamar yanda yake yi a sauran kwanakin, sai ya ce min gaba a Musulunci kwana uku ne, in ya wuce haka ya zama haramun, don haka wacce muke yi wa juna yau ta qare, na kawo qarshenta ta hanyar ce miki Assalamu alaikum” nayi shiru ban amsa ba ya ce min ko ki amsa ko kar ki amsa wannan ke ta shafa, ya ci gaba da al’amuranshi. Ganewan da nayi cewar ba zai yarda gabar ta ci gaba ba yasa da aka aiko Baba Qarami ya kawo mana abincin dare don Sa’adatu bata yarda ta sake shigowa gidan ba, tunda taga marin da yayi. Ina buxe abincin naga irin salon da aka yi na buxe baki zan sake jera mishi wasu baqaqen maganganu saboda in samu mu xora akan na da, sai ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min, kina so ki sha wahala kenan, in ki ka ce za ki rinqa gaya min magana ai ba auren ‘yan iska nayi ba, ba kuma auren nayi a bisa wata mummunar manufa ba balle in zuba miki ido ki rinqa zagina, ko ki bari ne girma da arziki ko ki ji a jikinki.” Shiru nayi na kame bakina saboda na gane Inna ce sai na faxi abinda nayi nufin faxan, tolalle kuwa da gaske zan ji a jikin, don ban ga alamar abin zai tsaya ga mari kawai ba. Ban sani ba ko shirun da nayi ne ya xan bashi wata dama ta tambayata xazu naga fura da nono a frizer, a ina ki ka samu? Ban kalle shi ba na ce mai babban allo ne ya bayar aka kawo min, to xan dama min mana insha, yanayin da yayi maganar a ciki yasa na xebo na zo na dama na miqa mishi. Sai da ya kusa shanyewa na tuna ban sa mishi sugar ba, nayi maza naje na xauko kwalbar sugar na kawo mishi tare da gaya mishi cewar kayi haquri ban sa sugar ba, na riga na saba da shan furar mai babban allo, ya ce eh ai hakan ma daxi ne da ita na ce uh na qi yarda maganar ta qara nisa. Rannan na kwana bakwai a gidan Ado, a lissafi ne kawai suke guda bakwai, amma a tsanani sun fi kama da watanni. A daddafe muka kai waxannan kwanakin, shi xin bai yi gaba ba a kaina ba sai dai da gani har shi mun kai wani hali na tsananin wahala da galabaita. Ni dai ina cikin wani hali na tsananin ciwon jiki a dalilin wasan mugunta da wani lokaci yake yi min, ga kuma tsananin ciwon kai saboda rashin samun barci. Yayin da shi kuma Ado yake kwana zirga-zirgar shan kanwa da su andur lever sold. Kwana muke wani yanayi mara daxi, amma gari na wayewa sai ya maiyace ya maida komai ba komai ba ya ci gaba da murmushin shi, ya shirya da safe zai fita har ya gama komai sai ya waiwayo ya kalle ni ya ce min “Anya kina da kirki kuwa Humaira? Nayi maza na ce mishi ba ni da shi, ya ce to da alama kam amma in ban da haka yau kwanaki bakwai a nan gidan ga Hajiyar Giyaxe a cikin gida bata tava shigowa wurinki ba kema ba ki neme ta ba, sannan baki tava xiban ko da ruwan gidanki ne a kofi ki ka aike mata da shi ba. Anya! Bakya lura ki ga kamar sa’a kika yi tayi yawan ran da taga aurenki? Sannan in kika yi sakacinda ta tafi ba ta ci abincinki ba sai yaushe kike ganin zata dawo taci? Yaushe? Jibi ko gata ko baxi? Shiru nayi ban tanka mishi ba, shima bai matsa sai na bashi amsar ba, yasa kai ya fita yana fita sai ga Sa’adatu ta shiga da sauri na tare ta cikin farin ciki ina tambayarta me yasa ba kya shigowa Sa’adatu? Sa’adatu sai yau?” A hankali ta ce, “Inna ce ta hana ni, yanzu ma yaya Ado ne ya ce min kina nemana, da sauri na tambaye ta me yasa Inna zata hana ki zuwa wurina? Ta ce na gaya mata kin zagi Yaya Ado shi kuma ya mare ki, shi ne ya ce to kar in sake shigo muku gidanku.” Nayi kamar in sake tambayarta wani abu sai kuma dai na fasa a dalilin shekarun nata ba wasu masu yawa ba ne tara ne da ita. Na jawo kazar da Ado ya kawo min jiya da daddare ban ci ba, na tura mata tare da kayan tea. “Zuba yanda ya yi miki ki sha Sa’adatu, yi nayi wai don in burge ta in yaso in ta gama sai in ce mata taje ta turo min su Baba Qarami sai ta kalle ni ta ce min, na riga na qoshi. Da sauri na ce mata, naman kaza ne fa Sa’adatu, don nasan ita xin mai kwaxayin naman ne sai ta ce eh na qoshi ai muma muna dashi.” Na ce, “To shi kenan Sa’adatu, ki gaida Innan ko?” na ce mata “To.” Ta tashi ta tafi cikin zuciyata sai murna nake yi, Inna ma al’amura sun fara canza mata, ko a ina take samun kuxi yanzu? Tunda nasan dai duk abinda take dashi ta kashe sai kuma na tuna ai surukaye ne da ita ga Ahmad xan wanta ga Salisusu xan Baba Yahaya na kuma san dukansu zasu ji da ita. Na fito tsakar gida sanye da doguwar shimi a jikina wacce ta xan fara jiqewa kaxan a dalilin wankin kayan su Baba Qarami da na sa aka kawo min nayi shanya na ke yi a igiya yayin da su Baba da Ibrahim suke xakinsu suna sharholiyarsu tare da abokansu, sai ga Ado ya shigo riqe da ledojin sayaiya biyu a hannunshi. Yana ganina fuskarshi ta sauya ban ce miki a tsakar gida kisa gyale ko hijabi ba? Nayi shiru ban amsa mishi ba, ya sake yi min tambaya cikin tsawa, “kina so ne wani ya ganki a haka?” na ce, “A’a, to su waye za su ganni ba yayuna ba ne?” Yayi maza ya cukume ni ya shaqe yana faxin “Har abokansu da suke cikin xakin ma yayunki ne?” nayi shiru ina zaro ido cikin yanayin tsoro yana sakina ya nufi xakin su Baba ya xaga labulen. “Kai duk ku fito nan bana hana ku shigowa gidan nan kuna mana shaye-shayenku ba?” “A’a Kawu, sigari ne kawai.” Abokansu ne masu bashi amsa, daidai suna fitowa suna barin gidan sum-sum ya sake biyo ni xaki bayan ya gama dasu ya same ni kwance a kan katifa ga cefane na kawo ki tashi kiyi girki, na ce ba zan yi ba na riga na fasa, ya ce kije kiyi ta fasawa. Ya juya ya fita. Ado yayi matuqar tasa Baba da Ibrahim tare da abokansu a gaba har sai da Mama tayi mishi magana akan su sai kuma ya sake dawowa kaina da wasu dokokin nashi masu tsananin bi. Rannan ya dawo gida da rana T.V da kafet Plasma tare da rediyo C.D da kafet na tsakiyar xaki alamar dai so yake ya xan gyara falon saboda rashin fasalin shi ya yi yawa, yana barin gidan sai ga Suwaiba ta shigo, bayan tunda aka yi bikinmu bata shigo min ba, amma kullum tana barin unguwar taje gidan Habiba. Ban ji tayi min sallama ba, don haka na ci gaba da kwanciyata akan katifata a xaki ba tare da na tanka mata ba, ta shiga kunne-kunne da jone-jone ina jin ta sai naji qawarta tana ce mata mun shigo gida babu sallama babu gaisuwa mun