Sashe 20
Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta ce a’a wannan ai ba nan za ki kawo ba can xakin Mama za ki kai mishi, ta ce a’a nawa ne bani ya ce yayi in sa a xakinmu in rinqa kallo. Da sauri Inna ta ce a’a shi da yake cikin wannan hali yayi kyauta da kaya mai daraja haka? Na ce, a’a Inna bashi ya bata ba? Ta ce to ina yake yanzu? Ta ce na dai ganshi ya baiwa Yaya Ibrahim makullan gidan ya ce wai yaba Mama shi kuma ya hau mashin ya tafi. Inna ta sake cewa kai wannan al’amari yakai inda yakai, yaron nan yana cikin wani hali kuyi mishi addu’a. Sa’adatu ta ce wa Inna shima ya ce in gaya miki kiyi haquri kuma kiyi mishi addu’a ta ce to ni me yayi min ma? Nan da nan kuma ta shiga jero addu’o’in da yace tayi mishin, zuwa can kuma ban san tunanin da tayi ba sai naji ta ce ni in da zai samu ya kama muku haya a wani wuri ai da nasa an gyara muku gidan ba kaxan ba ta shiga bani labarin irin gadaje da kujerun waje da Alhaji Abba yasa ake kawowa Hajiya Kubra wai don itama ta rinqa juya kuxi a hannunta. Inna tana faxin haka sai zuciyata ta shiga raya min irin qayataccen gidan da zata shirya mana in har Ado ya kama mana haya da zai yi hakan kuwa ko da wane irin daxi zamu ji ni da shi oho? Washegari da safe ne Ado ya sake zuwa unguwar har ya shigo gida sai da ya fara shiga wajen Babana ya gaishe shi sannan ya shiga ya gaida Mama ya fito zai shigo wurinmu ina jin Mama tana ce mishi ai na xauka ba za ka sake shigowa gidan ba ne saboda an qwace maka Inna Majandi, in kuma baka daina shigowa kana shiga wannan xakin ba to zan sa mai gidan ya hana ka shiga mishi gida, ban ji ya ce mata komai ba. Inna ta amsa sallamar da yayi ya shigo suna gaisawa naji tana tambayar shi lafiya dai ko? Ya ce qalau Inna, na xan yi zirga-zirga ne saboda in warware wasu abubuwa wasu kuma in kammala su, na kuma gama shi ne nazo in yi miki bayani, ta ce mishi to, daga ni har ita muka shiga sauraro don mun fi zaton takardar sakin aurena ya kawo min, sai na ji ya ce akwai wasu sharuxxa da kwanaki aka sanya min akan aurena ban sani ba ko rashin cika su ne yasa Baba ya baiwa Humaira umarnin dawowa gidan don haka na tsaya naga na cika su. Inna tayi shiru alamar shi take sauraro shima kuma da yake yasan hakan sai kawai ya ci gaba da yi mata bayani na farko akwai maganar gida cewar in bar shi na biyu akwai jarin Mama da nake juyawa sai na uku shi ne in fita gaba xaya daga cikin kasuwancin Baba. Inna ta ce tow, ya ce to waxannan xin duka na shirya yin su don haka ne ma naje nayi wa Baba Yahaya bayanin komai ya kuma ce min in zo yana zuwa in na zo xin kuma kafin ya iso to in shaidawa Liman da Malam Harisu makwabcinmu don su zo su taya shi zama shaida na zan mayar musu da abinda suka nemi in mayar musu don suma su bani matata da suka karva. Inna ta sake cewa haka ne, ya ce to bayan wannan ma Inna akwai gidajena guda biyu da nake karvar hayarsu da bus da take yi min zirga-zirga ina kuma da shago da ake yin xikin a ciki shi wannan shagon nawa ne da kuxina na gado na saye shi na kuma zuba kekunan, Musa ne yake lura da komai nashi, don shima gwanin tela ne ban kuma tava samun matsala da shi ba, yasan komai nawa na gaya mishi abinda ya saba bani ya rinqa kawo miki ki rinqa sayen sabulun wankin yara, su kuma gidajen da motar zan mayar wa Baba da abinshi don a cikin dukiyarshi na saya. Inna tayi maza ta ce a’ah to in kayi haka kai kuma fa? Ba wahala kayi wa dukiyar ba, ka kuma yi tattali?ya ce eh, amma ban same su ta hanyar da ta dace ba, don haka zan mayar mishi zan je in nemi nawa ni dai in suka yarda muka rabu lafiya dasu suka bani matata na tafi da ita to shi kenan komai mai sauqi ne, sai da tayi tayi mishi addu’a da godiya kan alherin da yayi mata sai ta ce mishi to in ka xauki matarka ina za ku koma? Sai da ya xan yi shiru tanfar dai nauyin abinda zai gaya matan yake ji zuwa can sai naji ya ce mata qauyenmu zan koma, da gudu na fito daga xakin da nake kwance ina riqe da xankwalina a hannuna durqusawa nayi da gwiwoyina biyu a qasa na ce mishi qauye? Bai kalle ni ba bai tsaya amsa maganar da nayi mishi ba sai kawai ya ci gaba da yiwa Inna bayani, dangin mahaifina mutane ne masu karamci da zumunci, na kuma yi miki alqawarin matuqar ina raye cikin lafiyata to ba zan bar Humaira ta shiga cikin matsalar da zata dame ta ba, don haka na roqe ki ki qara yin haquri ki kuma yafe min abubuwan da nayi miki. Cikin wata irin murya mai rauni naji Innan tana ce mishi to amma kai ma na roqe ka kayi haquri ka fara tafiya tukuna in yaso daga baya sai kazo ka xauketa. Maimakon ya ce wa Inna to sai kawai naji ya ce mata a’a Inna, ai in nayi haka ya zama min kenan tanfar na rasa komai bayan kuma don in same ta ita kaxai xinne yasa na bayar da komai xin da nake da shi saboda haka zan tasa ta a gaba ne mu tafi. Ina jin ya faxi haka ban jira amsar da Inna zata bashi ba sai na ce mishi a’a babu wani qauye da zan bika mu tafi, ban tava zuwa qauye nayi kwanakin da suka wuce guda bakwai ba, bana iyawa. Sai kuma haka kawai in bika can in zauna? Ba a can aka haife ni ba mahaifiyata ma ba a qauye aka haife ta ba. Ado ya tashi ya fita saboda jin sallamar Baba Yahaya, ya barni a nan ina durqushe ban gama lissafa mishi abinda na fara ba, yana barin xakin Inna ta kalle ni ta ce qauye kuma? Wannan wace irin fitina ce? Maimakon ta saurari amsar da zan bata tunda naga kamar tayi min tambaya ne sai kawai naga ta rushe da kuka, kuka kuwa mai tsanani irin wanda ban saba ganin tana yi ba. A tsakar gidanmu gaba xaya mutanen da Ado ya nema sun hallara ana zazzaune har da Babana wanda yasha mur sosai don nuna alamar babu wasa, Mama ma tana gefe tun kafin a kira ta ta fito ta zauna. Liman yayi addu’a ta fatan a dace da duk abin da za’ayi ya zaman ya zamo shi ne mafi alheri kuma ayi komai lafiya a tashi lafiya aka shafa da amin. Baba Yahya ya kalli Ado ya ce, to me ya faru ne Ado? Ado ya gyara ya soma rattabo bayani tun farko yanda aka yi Mama tasa shi karvar aurena al’amuran da suka yi ta faruwa bayan auren da sharuxxan da ta sanya mishi na cewar za su faru in har ya ce zai ci gaba da zama da ni da kuma yanda Babana ya kira mu muka zo ya ce ni in shiga xakin uwata shima ya shiga na tashi uwar shi kenan ya raba aure, magana ta qare. Kowa yaje ya riqe tashi. Ya ce, to shi ne nace wataqila rashin cika waxancan sharuxxa da aka gaya min ne yasa aka zartar min da wannan hukunci, don haka na kira ku saboda ku shaida zan cika sharuxxan dan nima a bani matata in tafi da ita, kowa ya yi shiru yana sauraron abin mamakin da Ado ya rattaba yayin da shi kuma Babana ya shiga faxin lalle kai xin nan butulu ne ban sani ba, Mama kuwa kuka ta kama yi tana faxin wai bata tava zaton Ado zai qulla mata sharrin da ya qulla mata ba. Liman ya katse su ta hanyar cewa, to amma wannan lamari da ban mamaki yake, ashe bani da Alhaji Yahaya ba ne muka je ba da haquri don iyayen mijin ‘yar uwarta su barta ta koma xakinta ta zauna suka qi muka dawo muna vacin rai da baqin cikin wulaqancin da aka yi mana na qin yarda ta koma ba? Baba Yahya ya ce eh, to shi ne kuma kai da kanka kake cewa a dawo maka da wannan ka raba auren Alhaji a ina ne uba ya samu ikon qwace ‘yarshi daga wurin mijinta, alhalin ba mijin ne yace baya yi ba, ai daga faxin ka bayar an ce an karva to baka da sauran iko, kai Ado kana son matarka ka kuma shirya cika sharuxxan duk tsananinsu don a baka ita? Cikin ladabi ya ce eh Mallam, to kawo su. Ado ya shiga miqa takardu yana bayani har da na gidajen nashi da motar ya ce ita kamma direban ya ce min ya kawo ta suka ce eh mun ganta bayanin kuxi a banki da na hannun mutane da wanda su kuma ake bin su bashi duk ya bayar. Mallam Harisu ya ce amma Alhaji yanda yaron nan yasan komai na kasuwar nan taka da kuma dawo da wannan dukiya da yayi wacce da can baka san da ita ba baka ga kamar ka yafe mishi ka bashi matarshi suci gaba da zamansu kaima kuci gaba da harkokinku bai fiye maka ba? Tunda kowa ya san shi ya san shi ne a tare da kai babu kuma wanda bai san jarumtakar shi ba yana rabuwa da kai fa wasu a kasuwar a kuma kusa da kai za su qwace maka shi ba kuma zaka ji daxin hakan ba, kan Babana ya buxe baki yayi magana sai Mama tayi caraf ta ce, to ya tafi mana da can da babu shi Alhaji bai nemi kuxinshi ya samu ba? Wannan neman kuxi da yake