Sashe 21
Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yi mishi ma ai neman kuxi ne na kashe mu raba, Baba Yahaya ya ce eh da ki ka sa shi yin hakan ba in ba haka ba a ina ki ka samu wannan dukiya da ya dawo miki da ita? Me ki ke dashi? Ko kina so ne in tuna miki da…da sauri Liman ya ce a’a Alhaji kai kuma me ya kaika yin haka? Baba Yahaya ya ce abin baqin ciki ne da matar nan Mallam, gaba xaya ta hana gidan nan zama lafiya, ka duba yanda aka yi da dalilin da yasa ta qulla wannan aure da kuma abin ya juya ta inda bata zata ba maimakon tayi nadama kan muguntarta tayi ta istigafari sai kuma ta tasa xan uwanta a gaba da masifa, to za ki rasa shi za kuma kiyi kuskure don shi ne komai na hidimar gidanku ke da mijinki. A wurinka ba, kai kake ganin hakan ai ku ku ka shiga tsakanina dashi, Baba Yahya ya ce to ai shi kenan kai Ado a ina ka samu inda zaka koma xin? Ado ya sunkuyar da kai qasa ya ce can nake so in koma wurin dangin ubana, yana faxin haka Mama ta qyalqyale da dariya ta ce qauye kenan? Ai da can xin ku ka fi dacewa. Gaba xaya wurin yayi tsit saboda babu wanda ya zaci Ado qauye zai ce zai kai ni, shiru aka yi na wani lokaci mai tsawo kafin Mallam Harisu ya gyara zama ya ce wa Ado, ka gani Ado in wani abu irin wannan ya faru haquri ake yi a kwantar da hankali a natsu kafin a san kuma inda za’a fuskanta. Kai yaro ne mai natsuwa da girmama na gaba da kai, kowa ya sanka saboda kana da kwarjinin jama’a ka iya zama da su lafiya, kayi karatu.” Baba Yahaya yayi maza ya ce mishi ai digiri biyu ne da shi a yanzu, da sauri Mallam Harisu ya ce to ka gani? Babu wani dalilin da zai sa don wannan abin ya faru ka ce zaka bar birni ka koma qauye. A nan ma za ka yi harkokinka zaka samu kuma abokan harkar. Za kuma ka nemi aiki ai kayi ilimi shi qauyen nan da ka ke gani ka riga ka baro shi da daxewa ba iya zaman cikin shi zaka yi ba, don ka riga ka manta da rayuwar can duk da dai nasan kana yawan zuwa to sannan ita Humaira fa bata san qauye ba kar ka manta da wannan. Gaba xaya aka sake yin shiru na wani tsawon lokaci saboda Ado ya ki tanka maganar da Mallam Harisu yayi mishi, sai Baba Yahaya ya kawar da shirun da tanbayar cewa to ko kuma zaka fara tafiya ne kai kaxai ka barta a nan sai kaje ka gano yanda zaman naku zai yiwu in yaso sai ka dawo ka xauke ta? A hankali ya ce, a’a Baba, nafi so in tafi da ita, nafi so a bani ita, wataqila taurin kan Ado ne ya fusata Babana ko kuma yawan tsakin da Mama ke ja ne oho. Don jin shi kawai aka yi ya kama faxa yana faxin babu in da zaka tafi min da ‘ya ai bamu yi da kai akan in anyi auren qauye za ka xauke ta ka kaita ba, shi kuma Liman ya ce a’a wannan kuma ai ba magana ba ne shi dai a roqe shi cikin biyu yayi xaya, ko dai shi ya fara zuwa kafin ya dawo su tafi tare ko kuma kai Alhaji Yahaya ya yarda ka bashi aron wurin zama da shago a kasuwa tunda mun san duk abinda yake hannunshi ne ya kawo.” Baba Yahaya yayi maza ya ce har kayan zan sa a bashi in yi mishi lamuni ai duk an san shi, da Liman ya waiwayi Ado don jin abinda ya zava sia ya shiga basu haquri yana faxin shi a yanzu zai fi son a bashi matarshi ya tafi da ita wurin dangin ubanshi. Baba Yahaya ya ce to ina ganin tunda yarinyar nan itama tana da hankalinta da wayonta a kira ta tazo nan muji ra’ayinta, in ta yarda zata bi ka qauyen shi kenan, amma in bata yarda ba ba za mu tilastata ba, Babana yayi maza ya ce bin shi kuma yana nufin ta tafi kenan ba za ta sake dawowa ba. Ado ya xaga ido ya kalli Baba Yahya cikin natsuwa da ladabi yayin da tsoro ya baiyana qarara a idonshi ya ce mishi na roqe ka Baba kar ka bata zavi akan aurena, don zata ji tsoron maganar da Baba yayi mata. Baba Yahaya ya ce ba zavi ba ne haqqinta zamu bata in ta ce zata bi ka shi kenan, amma in ta ce ba za ta bi ka ba ba zamu sa ta ba, domin ya kamata ace kaima kayi sassauci akan tafiyar taka tunda mun maka alqawura mun baka zavi mun kuma roqe ka a matsayinmu na waxanda suka haife ka, amma baka yarda ba to hakan ba yana nufin ita xin zamu tirsasata ba ne. Mama tayi dariya tare da gyaxa kai ta ce ai gara dai kuma ku gani wai shi nan a dole shi mai taurin kai ne. Fitowa nayi a xaki a dalilin kiran da aka yi min har kafin fitowar tawa kuma Inna bata daina kukan da take yi ba, tana faxin qauye kuma? Haba wane irin qauyea? Na durqusa a qasa da gwiwoyina duka biyu cikin sauraron abinda Baba Yahya zai gaya min, zuba min ido yayi yana kallona cikin wani yanayi da yake baiyanar da tausayin shi a gare ni, ni baki da lafiya ne ma ko Humaira? Na ce mishi eh Baba, sai da ya qara xaukan wani lokaci mai tsawo cikin nazari da tunani kafin ya daure ya ce min to Humaira kin dai ji duk abinda muke ciki da mijinki, amma a yanzu zavin ya rage naki, za ki bishi ku koma can qauyen nasu? In za ki bishi to babu laifi ba zamu hana ki ba, domin aure ne shi kuma aure babu inda ba ya kai ‘ya mace, sannan mijinki yaron kirki ne jarumi kuma mai neman na kanshi, ni nafi kyautata kyakkyawan zato a gare shi, in kuma ki ka ce ba za ki bishi ba to babu mai sa ki saboda mu xin iyayenki ne zamuyi miki adalci baki san komai ba game da rayuwar qauye a xauke ki a kai ki can ki koma da zama ba zai zamo mai sauqi ba a gare ki. Don haka me ki ka ga ni, za ki ko ba za ki ba? Ya waiwaya wurin sauran jama’ar da suke tare ya ce ko ba haka ba Jama’a? suka yi maza suka ce wannan shi ne gaskiya, ya sake waiwayowa ya kalle ni ya ce, To Humaira zavi yana wurinki, yi maza ki gaya mana wanda ki ka xauka don ki kawo mana qarshen wannan kai kawo kin ga ai tun safe muke wurin nan ko kasuwa ba mu samu mun je ba. Xago ido nayi da nufin baiwa Baba Yahya amsa sai ka rab idanuwana suka haxu da na Ado, ni yake kallo ko qibta idon nashi baya yi saboda tsananta kallon da yayi, maqwalwuyanshi sai kai kawo yake yi alamar tsananin damuwa da alama kuma wata maganar yake son gaya min wataqila da ya san zavin zai zo wurina da yayi hanzarin gaya min ita tausayinshi yayi matuqar kama ni da na tuna kalmomin da ya furtawa Inna cewar tafiya babu ni xin zai zamo mishi tanfar ya rasa komai, gaskiya ne tafiya babu ni tanfar rasa komai ne a wurin Ado, tunda ya bayar da komai nashi to amma kuma anya tausayin hakan ya isa yasa in zavi Ado in bar kaina, da mahaifiyata? Anya tausayin nashi ya isa ya hana ni tausayin kaina da mahaifiyata? Bin Ado qauye kenan yana nufin rayuwata ta shiga wani hali musamman ma da yake nasha jin mawaqanmu na Hausa masu basira suna faxin wai kowa kaga ya bar birni ya koma qauye to wannan zaman duniya tasa ce ta gigita. Ban da wannan ma ni da kaina na sani ba sai an gaya min ba, shigana cikin matsala yana nufin Inna ma tana cikinta tsundum, na kuma sani da ita ce ta samu damar da aka bata irin wannan zavin da aka bani da tuni ta kawo qarshen maganar ta hanyar faxin babu inda zani. Waxannan dalilai sai suka sanya ni cikin wani hali na kai-kawo da bugun zuciya wanne zan zava? Rufe ido zan yi in zavi kaina da kwanciyar hankalin Innata in bar Ado da xan guntun kunyarshi da xan vacin ranshi ya kama hanya yayi tafiyarshi qauyensu ko kuwa? Tunda ai yayi kyakkyawar rayuwa babu ni, gaba xaya son da yake tutiyar yana yi min kwata-kwatanta daga wata uku ne, a baya ni xin ba komai ba ce a wurinshi, sannan dukiyar da yake ikirarin mayar wa don ya same ni na sani jarunta ne yin hakan, to amma kuma ai ta wani vangaren taimakon kanshi yayi tunda dama bata hanyar halal ya same ta ba, tana cikin asarorin qarya da aka yi ta cewa Babana yayi. Sannan ko Ado bai tafi da komai ba zai tafi da iliminshi wanda babu wanda ya isa ya qwace mishi shi digiri biyu kuma ke gare shi, sannan ban da waxannan dalilan duka bani da tabbacin cewar zan samu karvuwa wurin ‘yan uwan Ado da yake ikirarin maida ni cikinsu in suma suka zamo min kamar Mama fa yaya zan yi haka nan shi kanshi Ado wane tabbaci ke gare ni akan shi tunda tun ina ‘yar qaramata nake jin iyayena mata suna faxin wai shi xa namiji ba xan goyo ba ne, to musamman ma kuma wannan da shi da kanshi ne yake yi wa kanshi kirari da cewar shi xin namiji ne. Iyayena kuwa da dangina tuni suna sani zama da su yana nufin zan ci gaba da zamana a cikin gatana musamman Innata wacce nasan babu wani wanda zai cike mata girbina balle ya xebe mata kewata tun daga ranar da ta haife ni take sona kowa kuma ya san hakan, kowa ya bada wannan shaidar cewar Inna bata tava