← Book details Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 22

Sashe 7

Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

maganar kamar ba ki san komai ba?” ta xan yi murmushi tare da tave baki ta ce, “Nasan komai Humaira, amma dai kuma nayi miki sha’awar yaronne very handsome, very gentle.” Na ce, a hakan ko?”ta ce, eh, na ce to sumu-sumu kasau ne kin ji, in kin san abinda ya yi wa Inna da wanda yake yiwa Babana za ki san ko yaya yake ni xin bani da buqatarshi ba kuma zan buqace shi ba. Ta ce, “To shi kenan abinda ki ka gani dai tunda mai xaki ai shi yasan inda ke yi masa yoyo. Amma dai in har kin san baki da buqatarshi xin da gaske to ki riqe budurcinki kar ki bar shi ya tava don shi xin shi ne komai xin mu.” Na ce mata, “To.” Ta tafi tana jaddada min, kar fa in yi sakarcin da zai cuce ni tunda ga abinda uwar goyonshi ma take faxa, cewar auren nasu na kwana casa’in ne, na ce mata yauwa ko nan aka tsaya zaki gane ba wani abin da zan yi dashi, tayi maza ta ce haka to amma fa sai kin yi jarumtaka mai yawa don su xin ba wani kirki ne da su ba, haka nan kunyarsu ma ‘yar qanqanuwa ce, na ce to.” Na juya zuwa can cikin xaki, cikin zuciyata ina tunanin yanda za’ayi Ado ya ce yana son wani abu daga gare ni, kai haba shima ba zai fara ba zai jira ne kawai wa’adin kwana casa’in xin da Mama ta xibar mishi su cika ya sallame ni, shi kenan burinsu ya cika na zama bazawara tunda ma ga irin lalataccen kayan da suka yi min, ba don ayi amfani da shi suka yi ba, abu mai xan fasali da yake cikin gidan to a kicin yake shi ne coler da frich sai ko frizer waxannan kuwa Baba Yahaya ne yayi mana dukkanmu. Abokan ango suka rako angon don sayen baki, kayayyakin sayen baki sosai suka zo da shi, qawaye kuma suna faxin abin da za’a basu na sallamar qawaye suka kawo suka basu bayan an xan yi raha da barkwanci suka sallame su, suka tafi daga baya suma suka yi ‘yan nasihohinsa da addu’o’i, suka shafa. Ado ya yi musu rakiya ya dawo xakin. Yana dawowa ya cire hularshi da babbar rigarshi ya jefar kan kujera guda xaya ga alamar dama ya riga ya gaji da su, ya shiga banxaki ya gama abinda zai yi ya fito cikin natsuwa ya kalle ni. “Xan tashi mana Amarya kiyi alwala don mu gabatar da Sallar nafila.” Lokacin ne na gane bayan wankan da yayi har da alwala ya xauro. Ganin ban tanka mishi ba ya sanya shi tsayawa yi min bayani, akwai alheri mai yawa cikin irin wannan nafilar da aka kwaxaitar da ma’aurata game da samunsu, na ce au haba? Yayi shiru yana kallona sai dai fara’arshi ta xan ragu, a lalace na ce mishi har da auren kwana casa’in cikin irin auren da ake yiwa wannan nafilar? Yana daga tsayen ya ce min, “Ai lokaci ne zai bayyanar da wannan, don haka tashi kiyi alwala muyi sallar.” Na ce to ban yi niyya ba.” Yayi sallar nafila raka’a biyu ya xora shafa’i da wuturi akai ya yi addu’o’in shi ya shafa, sannan ya miqe ya jawo ledar kayan ciye-ciye da suka zo da ita, ya matso kusa da ni. “Sa hannu mu ci ko kin fi so in ba ki?” da sauri na kalle shi na ce mishi, kai kar fa ka ce zaka maida ni wata ‘yar yarinya qarama, yayi maza ya ce haka ne ke a yau ba yarinya qarama ba ce ya ture ledar can gefe ya fasa cin abin da ke ciki ya miqe ya fita sai gashi ya dawo xakin daga shi sai wata lalausar rigar bacci da ya riqe da belt xinta. Gabana yayi mummunan faxuwa, me wannan mutumin yake nufi? Nayi maza na mike tsaye ina ja da baya har na kai ga tava bango, zuba min ido yayi yana kallona kafin ya buxe baki a hankali cikin natsuwa yana tambayata me ki ke yi haka kamar wata qaramar yarinya? Nayi maza na ce mishi kar ka tava ni, kai ma kasan bai dace ka tava ni ba in har kana da gaskiya da adalci. To in ba ni da gaskiya da adalci fa Humaira zan iya tava ki? Kasa bashi amsa nayi yayin da jikina kuma ya xauki rawa sosai saboda tsoratar da nayi dashi, don haka nan take na ji babu abin da nake son yi irin in yi kuka. Kukan da yaga ina yi sosai-sosai ya sanya jikinshi ya xan yi sanyi, ya koma bakin gado da nufin zama yana tava gadon ya valle. Ado ya miqe tsaye ya zuba wa gadon ido ya xaga zanin gadon ya kalli katifar ya ce, “A’a kamar zai yi magana sai kuma naga ya kame bakinshi yayi shiru iyaka dai bai sake yin wani abu ko cewa komai ba sai bayan da ya gama fitar da gadon tare da ‘yar katifar dake kanshi, sannan ya dawo ya jawo katifar da muka kwana akai jiya ya kwantar yayi shimfixa akai sannan ya sake kallona ya ce min. “To zo ki kwanta.” Naci gaba da tsayuwar da nake yi, ya kalle ni ya ce min “Ai in ina so zan zo nan inda kike in xauke ki, don haka zo ki kwanta kawai ba zan tava ki ba, magana kawai zamu yi.” Na xan taho a hankali jikina kuma a takure na xan xofanu gefen katifar yayin da shi kuma ya zauna a tsakiyarta ya baje qafafuwanshi ya zuba min ido yana kallona, menene matsalarki Humaira? Nayi maza na ce mishi bani da ita, ya ce to me yasa ba kya son in tava ki bayan kuma kin sani sarai tun jiya ke xin a matsayin matata kike? Na xago ido na kalle shi wasu sabbin hawayen suka sake zubowa sharrr daga idanuna na ce mishi na roqe ka ko baka tava yiwa kowa adalci ba kayi wa wannan auren adalci, kar ka tava ni tunda kaima kasan komai.” Ya ce, “Ban san komai ba, sai kin gaya min.”Na ce “Kaima kasan ba da gaske kake nufin zaman ba.”Ya ce, “Wannan kuma abinda ya shafe ni ne ni da zuciyata, abinda yake naki guda xaya ne shi ne nayi miki umarni ki amsa, na ce ba zan iya ba.” Ya ce, “To saboda me?” ban san yanda aka yi ba sai kawai naji bakina yana yi mishi lissafi “Saboda baka tava gaida Innata ba, baka tava girmamata ba, baka tava xaga ido ka kalle ta da nufin mutuntata ba, tsawon zaman ka da ita in ban da tattalin vacin ranta ya qaru babu abinda ka rinqa yi. Sai kuma ka tava mata ni?” na sake xago ido na kalle shi hawaye suna gudu a idona shar-shar-shar cikin wani yanayi da yafi kama da na shanye halin da ake ciki, ko voyewa. Ya ce, “To ai na ce miki ni xin namiji ne.” na tambaye shi me ake nufi da namiji? Ya ce min, jarumi, na ce tabbas na yarda kai xin jarumi ne, na miqe na bar mishi katifar na fito falon na hau kan ‘yar kujerar ulun da ke wurin na xan xofanu ban wani yi motsi mai qarfi a kanta ba saboda tsoron kar itama ta wargaje kamar yanda naga gadonta ya yi. Rannan dai kusan kwana nayi idona biyu saboda tsoron Ado da abinda yake shirin yi abinda ban tava tsammanin hakan zai faru ba a tsakaninmu, to sai dai kuma shima Adon da baya cikin tsoron barazanata bana zaton ya runtsa, don ina ta jin motsinshi. Ana kiran Sallar farko ya tashi ya shiga yayi wanka ya yi alwala ya fito falo inda nake “ki shiga kiyi wanka kiyi Sallah.” Ban amsa ba, ban kuma qi yin abin da ya ce in yin ba, saboda ciwon da jikina ke yi ga gajiyar biki ga kuma kwanan takura da nayi, ido kuma biyu da kamar nayi bacci ne ma to da da xan sauqi. Na idar da sallar Asuba na xan kishinfixa gefen katifar ina sauraron shigowar Ado daga Masallaci, ban san yanda aka yi ba sai kawai na farka naga gari ya waye sosai, na miqe na shiga banxaki don in rage nauyin dake marata, lokacin ne naga aikin da Ado ya yi ina bacci jarkoki cike da ruwa ga wata qatuwar randa itama ya cikata da ruwa donni ko kayan aiki ba ayi min ba. Mama ta ce, wai uwa ce mai yin wannan ita kuma Inna bata yi ba, ta ce tunda ba da niyyar a zauna suka yi auren ba to babu abinda zata kai musu sai cin-cin da alkaki da kayan rabon da za’a baiwa iyayenshi wannan kam a wadace aka yi aka kuma basu suka tafi cikin murna.” Ta window nayi leqe saboda jin maganar da Ado keyi shi da Baba ne a tsakar gida wai yatsa yake nunawa Baba alamar kashedi. “Ba fa zan lamunci abinda ku ke yi a cikin gidannan ba kai da Ibrahim, saboda a yanzu ba ni da ku ba ne kawai, matata tana ciki.” Gabana ya yanke ya faxi da qarfi saboda jin yanda ya ambaci matata xin cikin wani yanayi. Haushi da takaici ya kama ni, na yanda yake gwadawa Baba Isa da gadara, bayan kuma gidan ubanshi ne, a zuciyata na ce in ban da su Baba sun zama abin da suka zama yaushe za ace wanda yake zaman cin arziki a gidan ku zai yi muku haka? Ko da dai a matsayin Kawunsu yake ai da sai dai ayi zaman ganin darajar juna da mutuntawa. Tsintsiyar zabori Ado ya saka ya wanke gidan gaba xaya ya gyara duk wani abin da yake buqatar gyarawa, sannan ya shigo xaki bai kalle ni ba ya ce min za ki rinqa gaisawa da Baba da Ibrahim ne a matsayinsu na yayunki, amma ban yarda ki ga wani abokinsu ki gaishe shi ba, ban kuma yarda wani abu ya kai ki xakinsu ba ko menene shi. Matuqar kuma ba wani aiki za ki yi ba, to bana son zamanki a tsakar gida in kuma hakan ya kama to ki sa
Chapter 7 · 0% Book details