← Book details Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 22

Sashe 6

Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fara kuka don ban san me ya faru ba gashi kuma ban ga Babana a cikin gidan ba, sai kawai Zubaida ta ce min ba fa wani abu ba ne maneman Suwaiba ne suka tuiro wai a xaga musu nasu bikin don ba su samu xaki ba, shi ne da aka ce musu a’a bikin ya riga yazo kuma ba ita kaxai ba ce don haka ba zai yiwu ba maganar xagawar shi ne suka ce to sun fasa auren. A zuciyata na ce ina ma ni ce! Duk da irin rashin kyakkyawar mu’amallar da ke tsakanina da su ban ji daxin hakan ba, don haka sai na wuce naje na shiga xakin Mama don in yi magana da Suwaiba, kukan da take yi ya wuce gaban bayani, nayi qoqarin rarrashinta, naga ba za ta gane ma ina magana ba, don haka na haqura na fito cikin zuciyata dai na ji tausayinta don ta riga tasa rai da yawa akan auren. Can cikin zuciyata na ce, oh’oh ko menene mai daxi haka cikin auren da za’ayi mishi irin wannan son? Oho. Ko kwana xaya da faruwar abin bai cika ba sai kawai Mama ta soma yin waya tana gaya wa mutane cewar bikin babu shi kwata-kwata ma ba za ayi ba don ba zai yiwu ayi biki babu Suwaiba a ciki ba. Kan ka ce menene wannan sai ga Babana shima yana qoqarin gamsar da Mahaifiyarshi dalilan da suka sa shi zai xaga bikin zuwa wani lokaci gaba kaxan, ita kuwa ta ce ina! Akan mutum xaya sai a fasa bikin ‘yanmata huxu? Ba zai yiwu ba sai dai ko ita Suwaiba da uwarta su fito da wani mijin kafin ranar don a haxa har da ita ko kuma ayi babu ita. Hakan kuma aka yi ranar xaurin aure yazo an kuma xaura auren ‘yanmata guda huxu babu Suwaiba a ciki, don ita da Mama sun kasa fiddo da wani mijin ko da kuwa cikin ‘ya’yan dangi ne, a zuciyata na ce oh’oh wato Inna dai ba qaramin rufin asiri ke gare ta ba da aka bata wa’adin kwanaki uku in kawo miji aka kuma kawo har guda biyu da aka hana su ni kuma aka ba su qannena suka karva saboda ba donni da qannena dama za su yi auren ba don ita Innan ce sanin halinta da suka yi mutuncinta da kuma haqurinta. Anyi biki irin wanda ba’a zata ba, zan ma iya cewa ba a tava yin irin shi ba a unguwarmu gaba xaya saboda ba Mama da Babana ne kaxai tsaye akan bikin ba, balle don sunyi mishi saki lecece ya kasa yin armashi. Baba Yahaya da Alhaji Maikuxi sunyi wa bikin hidima ta ban mamaki dangin Inna rannan basu wani saurari dokar Babana ta hana su zuwa mishi gida ba, tururuwa kawai suke yi suna shigowa Inna tana can cikin xakinta ko ganinta ba’ayi. Itama Mama danginta da qawayenta sun zo da yawa, to amma kuma ta riga taki bakin sai zage-zage da neme-nemen tashin hankali take yi, Inna Balki ta ce kar wanda ya kulata ai mu ba ma hidimar arziki muyi faxa. Duk wani abin da suke buqata shigo dashi kawai suke yi ko loma xaya na gidan basu nema ba balle aje ana vacin rai. Ni kam nayi kwalliya ko in ce mun yi kwalliya don kuwa Atika da Aliya kayan aure aka yi musu tanfar ba za su qare ba, saboda yawa to amma kuma nima dama Innata da Hajiya Kubra sunyi min tanadin kayan ado masu daraja, don haka ko kallon akwatin da Mama ta bayar guda xaya na kayan aurena da zannuwa biyar a ciki babu wanda ya sake yi. Sai ma da Hajiya ‘Yardubu taga irin wulaqancin da ake yi wa Akwatinne taja shi ta adana tana faxin “Wannan akwati fa ba shi ne auren ba, miji shi ne aure. Gaba xaya aka fara magana shima mijin ai ba auren yake nufi ba, Hajiya ba ki ji abinda suke faxi ba ne cewa a kwana casa’in zai qare? Tayi murmushi ta ce, to ko na kwana bakwai ne in ya zamo mai albarka ai shi kenan, ba dai an xaura ba? Suka ce, “Eh” ta ce to ai shi kenan.” Cikin kwanaki biyun da bikin ya kankama wato Juma’a da Asabar hidimar da aka yi ba qarama ba ce, abin mamaki kuma shima Ado yayi hidima yayi ado yayi gayya, danginshi na uba da abokanshi masu yawa suka zo, qanin Mahaifinshi ne wai ya karvar mishi auren. Ranar Asabar da daddare Amare gaba xaya aka kai su gidan mazajensu, sai dai ni kam fita da ni kawai aka yi daga gidanmu aka sake shiga dani xaya gidan namu. Inna Balki tana zaune a gefena kan wata ‘yar tabarma da muka samu a shimfixe don Mama bata sa anyi jere ba, ta ce sai gobe, sannan gaba xaya kayan alatun da Ado ya kamata wurin shi da su ta kwashe wai sunzama nata tunda yayi aure. Ta xan faki idon mutanen dake cike a xakin ta matso da bakinta kusa da kunnena ta ce min, mijin naki fa xazu na ganshi da yazo angwanci santalelen saurayi ne, ina ganin maimakon fito-na-fito da rashin kirki ko za ki gwada yi mishi kirki ne? nayi maza na ce mata a’a bana son shi ba zan zauna dashi ba, ta gyaxa kai ta ce to shi kenan, amma baki ga kamar…kan ta gama nace mata bar shi kawai Inna ba zan iya zama dashi ba, ta ce to yanda tayi dai muna miki addu’a na ce to na gode. Waxannan suka kawo ni suna barin gidan abokan Ado suka shiga kai-kawo suna tambayar ‘yanmata, abinda suke buqatar a kawo musu. Wata zaqaqura ta ce musu katifa don ba mu ga yanda za’ayi amarya ta kwanta kan wannan tsohuwar tabarma da aka yar a qasa ba, suka ce kin faxi gaskiya ‘yanmata, suka juya suka fita. Jimawa can sai gasu da qatuwar katifar sunbuqa sabuwa dal a cikin ledarta, har bargo shima sabo duniyar kule kan ka ce meye wannan sun wadata wurin da kayayyakin ciye-ciye da shaye-shaye iri-iri. Washegari ranar Lahadi rannan wuni muka yi daga ni sai qawayena sai dangin su Mama da suke shigowa jifa-jifa ganin amarya sai ko ‘ya’yana su dake kai-kawo amma dangin Inna babu wanda ya leqo don su dama sun ce sun gama da gidanmu tun jiya sun dai zo sun sheda xaurin aure, to yau za su yi hidimar su a tsakanin gidajen amaren su Atika da Aliya da kuma gidan mai babban allo, don su a wurin su shima Salisusu xa ne saboda Baba Yahaya. Har bayan Azahar ba a zo aka yi min jere ba, abincin ranar ma ba a kawo ba, wataqila don sun leqo sun ga angwaye sun kawo abin karyawa shi yasa ko suke zaton za su kawo na rana oho. ‘Yanmata suka nemo redio suka shiga sanya kaset suna cashewa, don su xebewa kansu takaicin zaman shiru. Sai bayan La’asar lokacinne naga ana shigowa da wasu katakwaye da ‘yan kujeru waxanda rabon da inga irin su tun a hotunan mutanen da, tunda nasan ko a qauye ba za ayi amfani da waxannan ba yanzun. Nan da nan masu jere suka yi jere suka gama ko awa xaya basu cika ba suka yi tafiyarsu dama kuma ‘yan uwan Maman ne masu jeren. Wajen qarfe shida saura kwata na yamma sai ga Anti Ramla ta shigo tasha kwalliya tayi matuqar yin kyau da kyar maganar take fitowa ga alama ba qaramin jiki ta ji ba a bikin, menene wannan? Ta shiga waige-waige tana qara kallon xakin na ce mata kayan xaki ne ta kwashe da dariya ta ce, kanta kayi wa kamata ta muzanta tunda shi ne zai hau kai ya kwanta ko kuwa na ce mata eh. Ta ce, kai baki ga gidan su Aliya ba da Atika, nayi murmushi na ce sun yi kyau ko? Ta ce ai ba a magana, Salisusu yana faxamar mada na ce sabon gidan Baba Yahaya kenan, ta ce eh to ita kuma Atika tana C.B.N Quarters, Alhaji Abba ya baiwa Ahmad vari xaya amaryar shi shima tana xaya, na ce kai sun more gidaje, ta ce eh an kuma yi musu kaya, don ban da na Alhaji Abba shima Alhaji Babba yayi musu wasu gadaje da kujerun a zuciyata na ce Alhaji Maikuxi kenan. Labari sosai ta bani na irin hidimar da aka yi na bikin Atika da Aliya, nayi murna sosai don nasan Inna tana cikin farin ciki. Daga baya ne kuma na ji tausayi, sai dai maimakon in ji tausayin kaina tausayin Babana ne ya kama ni. Gaba xaya abokanshi a yanzu arzikinsu ya zarce nashi, saboda suna da tsayayyun ‘ya’yan da suka tallabawa neman arzikin su a lokacin da suka soma buqatar hakan saboda shekaru sun soma yi musu yawa. Shi kuwa bai samu nashin sun kintsa ba, balle shima suyi mishi irin wannan taimakon sai Ado. Ado kuwa ta’adin da suke yi mishi shi da Mama yawanshi ba kaxan ba ne. “Tashi kiyi kwalliya ga waxannan kayan Hajiya Kubra ta ce in zo miki da su.” Na ce mata “To.” Sai da na sake wanka na zauna na sake shafa mai tana taya ni don mun riga munyi matuqar shaquwa da ita, sannan na sanya sabbin under wears waxanda suma a cikin kayan tazo dasu na sanya kayana tare da ‘yankunne da abin wuya tare da wasu banguls xin a hannuna su zobuna sai sheqi nake yi ina xaukan ido tanfar dai wata amaryar gaske. Sai da ta gama feshe ni da turare ta ko’ina sannan ta kalle ni tayi murmushin gamsuwa ta miqe tsaye da nufin tafiya nima na miqe tsaye da nufin yi mata taku zuwa qofar xaki, waiwayowa tayi cikin natsuwa kafin ta ce min “Kai kin yi kyau Humaira, kuma ke xin amarya ce ta sosai da sosai, sannan angon ki ma ango ne na gaske abu guda xaya da ya rage ku shi ne baku da haxaxxen gida baku kuma da kayan alatu amma wannan duk ba komai ba ne in har kun yarda zaku mallakawa junanku kawunanku zaku more aurenku a haka.” Nayi maza na ce, “Haba Anti Ramla, yaya kike irin wannan
Chapter 6 · 0% Book details