Sashe 13
Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta sake faxin babu inda za ni ai gidan mijina ne in naga dama na ce a nan xakin zan kwana kana da yanda zaka yi dani ne? A hankali cikin natsuwa ya ce mata babu, ya waiwayo ya kalle ni a inda nake takure ya ce min shiga ciki. Nayi maza na tashi na shige cikin na bar shi a nan don yin hakan ya fiye min sauqi akan zaman da nake yi a cikinsu, ina ganin abinda ke faruwa. Ina so tabar min gidan a yanzu tunda na mijina ne, ya ce ai na ji Mama, amma na roqi arzikin ki xan yi haquri kaxan ki xan saurare ni ba wani lokaci mai tsawo zata xauka a cikin gidan ba. Mama tasa kai ta fita, shima Ado ya koma ya zauna akan kujera, ni kuma ina can cikin xaki maqure wuri xaya, qirjina sai faman bugawa yake yi val-val-val saboda ban tava ganin abinda ya firgita ni irin na jiya da yau ba, Ado da Mama suna kace-nace bayan kowa yasan kullum Ado akan bin umarnin Mama yake. Wajen qarfe takwas da rabi na ganshi yana shiri kamar in tambaye shi ina za shi? Sai kuma na fasa, saboda yanda fuskarshi take xaure gashi kuma dama ban saba yi mishi irin waxannan tambayoyin ba. Yana fita daga gidan na koma can cikin xaki na zauna ina tunanin in yanzu Mama ta shigo ko ya ya zan yi da ita? Oho. Sai kawai naji sallamar Hajiyar Giyaxe da sauri na fita naje na tare ta, tana riqe da food flask xin da aka kai mata abinci a hannunta, nasa hannu na karvi food flask xin tare da faxin, gani ga ki amma ba ki tava shigowa ba sai yau, don na kai miki tuwo kin ji miyar amayar mai zaqi shi ne ki ka kawo min food flasks? To bari yau ma zan sake aiko miki da wani tuwon don gobe ma ki sake shigowa ki kawo min kwanon. Tayi murmushi ta ce, oh’oh-oh’oh, ni ba don kwanonki na shigo ba, zuwa nayi don maigidan ya ce min in zo in zauna mishi a gidan kafin ya dawo.” Cikin zuciyata na gane abinda yasa Ado yin hakan, shima tsoro yake kar bayan shi Mama ta shigo ta same ni ni kaxai. Muna zaune da Hajiyar Giyaxe mu biyu hira muke yi bayan nayi mata abin karyawa ta karya ta qoshi, sai sakucen haqoranta take yi da tsinken sakace a dalilin farfesun kaza da tasha, sanin da nayi cewar tun asalin dama can Hajiyar Giyaxe tana son Innata tana kuma matuqar sona ya sani sakin jiki da ita sosai, har na kwashe bayanin duk abin da ke tsakanina da Ado, da abin da ya faru daren jiya da abinda yasa ya turo ta taya ni hira duk na gaya mata, don kuwa neman abokin magana nake yi saboda damuwa tayi min yawa. Hajiyar Giyaxe tayi min wani lalataccen kallo ta ce, to abinda ya rinqa yi wa uwarki ba sa shi aka yi ba? Yanzu ma kuma za’a sa shi yayi ne? ba gashi nan ba a yanzu kullum yana kai-kawo a tsakani kuma da ban sani ba ai nasan ba da gangan yake yin abinda yake yin ba, to kuma in ban da shirmenki da kayi cuta ka cuci abokin zamanka ai gara shi ya cuce ka, tunda babu wani abin da ba ayin sakayya akanshi musamman ma ace shi wannan abin kan lamarin aure ne. yanzu ace Innarku bata soma ganin sakayya ba? Innarku fa surukaye uku tayi rana xaya, wane arziki ne ya wuce wannan? Kuma kana ganinta ma a cikin gidan ai kasan walwalarta ma ta xan sauya jinin jikinta ma ya soma dawo mata saboda wahalarta ta soma raguwa, gashi yanzu kullum zaka ganta a wadace cikin harka ni a zatona ma na ce ko mijinki ne oho, na ce anya shi ne kuwa surukayen nata waxancan xin ai dukansu ‘ya’yanta ne, ta gyaxa kai ta ce oho ban sani ba, amma ina ganin mijinki ma yana cikin aini ba yarinya ba ce nace haka ne Hajiya. Hajiyar Giyaxe ta gyara zama ta ce, to ko wannan tijara da ja’irar yarinyar nan mara kunya tayi wa Babanki da wannan mata shekaran jiya in ban da alhakin Innarku da ya kama su me ya kawo hakan? Nayi maza na vallo varin goro na miqa wa Hajiyar Giyaxe ta shiga goga shi a magogin goronta tana watsa shi a bakinta, ni kuma na qara mannewa da jikinta kafin na qara tambayarta ni me ya haxa su ne Hajiya? Ta ce, uhun in ban da iya shege menene wai kama su tayi suna yin wani abu ranar girkinta bayan kuma dama da nata girkin da natan duk ita kaxai aka haxawa, na sunkuyar da kaina qasa cikin yanayin jin kunya, cikin zuciyata dai cewa nake yi lalle yarinyar nan da kafirin iya shege take, yanzunnan Babana ta yiwa irin wannan iya shegen? Ita kuwa Hajiyar Giyaxe babu ruwanta, sai bayanin ta take yi amma da maganar tazo wurina na gaya musu dukansu ita mijin nata na gaya musu dama gulma da munafurci ne ya saku yin hakan, don ku cutar da Binta, to gashi nan abin ya koma kanku. Ni kam ban yarda na tofa cikin wannan zancen ba, illa iyaka dai na amsa sallamar Hajiya ‘Yar dubu, itama riqe take da food flask xina a hannunta na kalle ta nayi dariya nace, kema kwanona ki ka kawo min? ta ce, oh’oh, wane kwano ne zai fiddo ni a ruwan nan? Uwarki ce tayi wa Mallam waya ta ce mishi wai mijinki babu lafiya, gabana ya yanke ya faxi me Inna ke nufi da wannan wayar da tayi kar dai itama zafina take ji? Ina yake yanzu, ko yana ciki ne a kwance? Tayi tambayar bayan sun gama gaisawa da Hajiyar Giyaxe, sun yiwa juna ban gajiyar biki har tana faxin ai ban san kina nan ba Hajiya da na zo miki hira, Hajiyar Giyaxe ta ji daxin hakan da ta gaya mata ta kwashe zance duka ta yi wa Hajiya ‘Yar dubu, har da yiwa bayanin kwaskwarima na ce ah Hajiya…kan in faxi abinda zan faxa Hajiya ‘Yar dubu ta daka min tsawa ke tafi can ki baiwa mutane wuri akan zai tava ki ne ki ka kwantara mishi qarfe kina neman kashe shi? To zauna ya bar ki ba shi kenan ba sai ki rinqa jiqawa kina sha ko ki kai inda za ki kai. Hajiyar Giyaxe ta ji takaicin maganar, ta ce a’a Hajiya wannan ai ba zancen da za ki yiwa yarinya ba ne, sai kiyi mata faxa kawai irin wanda ya dace da ita. Rannan cikin dare na yi wa Inna waya don in gaisheta, bata xauka ba kamar yanda dama kullum nake mata washegari ma da sassafe na kira ta bata amsa ba, gashi kuma ina ji ta bugo waya ta gaida Ado da jikinshi, a zuciyata na ce ha’a to me na yi wa Inna? Me babban allo yazo gaida Ado wai da jiki, ya gaya mishi gani nan zuwa zai turo ni don in gaishe shi amma naje zauren shima ban same shi ba ya tafi. Na dawo xaki na zauna zuciyata takai matuqa wajen vaci, me nayi musu? Me nayi kowa yake fushi da ni? Ban san yanda aka yi ba kawai naji hawaye suna zuba a idona, kuka na soma yi sosai. Ado ya juyo ya kalle ni, me ya same ki Humaira? Me ya saki kuka kuma yanzu? Ko kuma kin tuna da irin takurawar da nake yi miki ne? rarrashin da yake yi min ya sanya ni buxe baki na ce mishi ban san dalili ba ne kowa sai jin haushina yake yi. A hankali ya ce min haba Humaira, kowa fa kika ce, kenan har da ni cikin masu jin haushin naki? Na gyaxa kaina nuna alamar eh har dashi. Ya ce, uh’uh ni bana jin haushin ki,ina dai so ne kawai in xan rinqa danne zuciyata ina yin haquri kar in rinqa yawan sakin jikina ta yanda zan yi tasa rai a kanki ina matsa miki tunda na gane da gaske kike yi ba kya son haka xin. Ban tankawa zancen nashi ba, iyaka dai na riga na sawa zuciyata wani al’amari tunda na gane har da Inna cikin masu fushi da ni akan Ado, bata lura da irin tasa Ado a gaba da Mama tayi ba kan sai lalle Adon ya sake ni. Kwana wajen huxu a jere daga wurin Inna ake kawowa Ado abincin dare na kuwa gane hakanne a dalilin Sa’adatu da ke kawowa da ganin irin kwanukan da ake zubo mishin kuma kasan ba qaramin girma Adon yake dashi ba a wurinshi, yana gama cin abincin in ya gama abin da zai yi zai duqunqune kan ‘yar kujerar da ke falon yayi kwanciyarshi iyaka dai bai cika yin wani barci ba, bini-bini kuma zan gan shi yana jiqa jar kanwa ko andre lever sold yana sha. Rannan cikin dare ruwan sama mai qarfi ne yake sauka kamar da bakin qwarya, ina kwance can cikin xaki akan katifata bayan na shafe jikina da mayuka masu qamshi da qara laushin jiki sai da na feshe jikina sosai da turare mai sansanyar qanshi, sannan na shige cikin bargona na ruhu. Ina jin yanda ruwa ke sauka da kuma sauraron tsawar da aka yi ina mai karanto addu’o’in da ake yi lokacin saukan ruwa, ko kuma tsawa. Ni kin kawar min da kofin da kanwar nan ke ciki ne? a hankali na ce mishi eh, ai ban san kana so ba ne ya ce ina so mana Humarai, ai kema kin san ina da buqatarta, gashi yanzu ruwan sama yayi qarfi yaya zanyi in je kicin in samo wata? Na ce to ko in zo in kawo maka wata, ya ce bar ta kawai zan yi haquri tunda ga ruwa yayi qarfi. Kwanaki kusan tara a jere babu abinda ban yi ba, wanda zan sa Ado ya tanka min na jan hankali da hila don dai in samu in sallama mishi kaina tunda na gane abinda nayi mishin ne ya sanya Inna har yanzu bata xaukan wayata, amma ya qi. Yana ganina a kusa