← Book details Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 22

Sashe 15

Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zuwa, ya xan yi murmushi kaxan ya ce bana fita yawo Humaira, hira nake zuwa shagon Sani mai shayi, wurin taruwar samari ne mu xan yi hira in xan ji xan sauqin zuciyata, kema in bar ki ki xan sake. Ba zan iya zama dake shiru ba in yi ta zuba miki ido ban kula ki ba, gashi kuma a yanzu ina cikin wani hali na canka-cakare, ban san abinda nake ciki ba a yau, ban kuma san abinda zan fuskanta ba, iyaka dai kawai nasan ina cikin wani irin ruxani da ban tava shiga ba, wanda kuma na shige shi ne a sanadin aurenki da nayi. Hausawa suna faxin wai tsalle xaya mai jefa mutum rijiya, ya kuma yi dubu bai fito ba. Wani lokaci naka yin tunani in ce da dai ace na sani to da naji kashedin da kika yi min na cewar kar in karvi aurenki in nayi wannan tunanin sai in ce da nayi hakan wataqila da ban samu kaina cikin halin da nake ciki ba, wataqila da rayuwata bata canza ba daga yanda take wataqila da yanzu ina nan ina zamana lafiya ina tafiyar da harkokina cikin kwanciyar hankali da gamsuwa. A duk lokacin da tunani ya tsananta gare ni na rasa yanda zanyi in warware wa kaina matsalolin da na samu kaina a ciki, sai in ce wa kaina to in sauwaqe miki auren mana in zauna lafiya tunda dama ba da wata kyakkyawar manufa aka karvi auren ba, to in kuma nayi wannan tunanin sai kuma in samu kaina da tambayar kaina, in na yi hakan zan koma kamar yanda da xin nake? Zan iya fidda ke cikin raina, in koma walwala da nishaxi kamar da? In zan yaudari kowa ba zan yaudari kaina ba, ina son zama dake sai dai kuma abubuwan da nake ciki da barazanar da nake fuskanta za su bar mu mu zauna tare? To in ina cikin wannan barazanar me ya kamata in yi? Shine haquri, haqurin kuma yana nufin dole sia na rinqa yin nesa dake saboda kar in aikata miki abinda zai zamo rashin adalci in tilasta ki yin abinda bakya so duk da nayi qoqarin yi miki hakan a baya dalilai biyu ne ko uku suka ingiza ni yin hakan. Na farko dai tsananin matsuwar da nayi a ikanki na biyu jin hirar ku da nayi da Ramla sia na gane har da ita ke zuga ki na uku kuma shine ban hango abinda na hango ba a yanzu, ban ce mishi komai ba, ban kuma tsaya tambayar shi abinda ya han go ba, iyaka dai kawai na miqe na shiga banxaki nayi wanka na fito xaure da farin tawul a qirjina, har lokacin yana zaune a inda na bar shi can cikin xaki na wuce na zauna a bakin katifa bayan na ajiye kayan shafana kusa da ni. Ko ba ka ce kana sona ba ma ya riga ya zama min dole in baka kyautar kaina tunda abinda Inna take so kenan, zuciyata ce tayi min waxannan kalaman. Ina magana ne na xan xaga murya kaxan na gaya mishi bai vata lokaci ba ya shigo, kallo xaya yayi min ya kawar da kanshi gefe me ki ke so in yi miki Humaira? Ban kalle shi ba na ce mishi mai zaka shafa min, ya sake kallona da xan guntun tawul xin da ke jikina ya durqusa a gabana yana faxin ba shafa man ba ne matsalar Humaira, abinda nake tunani shine kanwa ko andre lever sold ba za su yi min wani amfani ba, na ce to shi kenan nasa hannu na lakato man zan shafawa kaina, sai kawai naga ya karve man ya xaga hannayen naw aya sagala akan kafaxar shi wai don ya ji daxin shafa min man sosai. Har Asuba tayi ban iya daina kukan da nake yi ba, saboda dalilai guda biyu, na farko dai in ma Mama taci galaba a kan Ado ta tilasta shi sakina in zama qaramar bazawara kamar yanda dama can tayi buri tunda nasan tana da qarfi akan al’amarinshi, ko kuma aurena dashi ya ci gaba kamar yanda ya kwana yana yi min alqawarin in kwantar da hankalina in saki zuciyata muyi zamanmu lafiya babu abinda zai samu aurenmu. Babu mai sa shi ya rabu dani ya kuma godewa Inna da ta sanya ni nayi mishi alherin da nayi mishi, to in auren namu ya ci gaba da akan son ran Mama ba tunda nasan ba za ta tava son zamana da xan uwanta tunda tun asali ma ba don a zaunan ta sa shi yin auren ba, zan samu zaman lafiya da kwanciyar hankalin da nake buqatar samu a rayuwar aure na ko kuwa na rinqa zama cikin fitinar Mama kenan tayi min ta yi wa mahaifiyata? Shi kuwa Ado wanda ya kwana cikin matsanancin farin ciki gani yake yi tanfar matsananciyar wahalar da na gamu da ita a wurin shi ne ta sanya ni kukan da nima na kwana ina yi, don haka ya kwana yana rarrashi da ban baki da faxin kalamai masu nauyi tare da alqawarin zai tabbatar min da cewar shi xin namiji ne. Na idar da Sallah kenan sai ga Hajiyar Giyaxe ta shigo, na tabbatar Ado ne ya turo ta, kai lalle Ado namiji ne ko ya ya aka yi yaje gaban Hajiya yayi mata wannan bayanin? Oho. Cikin zuciyata ne kawai nayi wannan tunanin, oh’oh sannu Humaira sannu kin ji? Sannu Aishatu sannu da haquri kin ji? Allah dai yayi miki albarka, ya kuma qara rufa wa uwarku asiri ku dukanku ukun, haka aka yi haka nan aka same ku lafiya lafiya sai alheri.” Sunkuyar da kaina qasa nayi ban iya ce mata komai ba, saboda tsananin kunya ai ma kin yi qoqari kin taimaki kanki kin yi abin da ya dace ayi miki, to amma duk da haka sake shiga ki qara wani wankan don ki qara gasa jikinki sosai, ban yi musu da ita ba. Ado ya shiga kai-kawo da hidimomi iri-iri ko kunyar su Hajiyar Giyaxe da Hajiya ‘Yar dubu da suka zo gidan baya yi, wai har hira yake yi da su Hajiya ‘Yardubu ta kalle ni ina makure wuri xaya saboda zuciyata ta qi yi min daxi, ta qi yarda da cewar in sake ta tayi walwala taji daxin al’amuranta, musamman da yake na jiwo maganganun da Mama ta gayawa Ado sanda ya shiga wurinta da safe bayan Hajiyar Giyaxe tazo wurina saboda akwai haxakar bango tsakanin cikin xakina da nata. Amma wai sai Hajiya ‘yardubu ta kalle ni ta ce min oh’oh mahaqurci dai mawadaci, wannan fa shine wai komai wayon amarya a sha manta, to yau dai Adamu ya zama miji qarya kuma ta qare. Kuka sosai na kama yi ita kuwa Hajiyar Giyaxe ta soma yi mata magana Hajiya ke dai munin nan naki bai da wani daxi, zo ki tafi gidanki kije wurin naki mijin ki bar min Aishana ta huta, qaryarta bata wani qare ba me akai kuma da maza, da za ki ce mata wani qarya ya qare?” To haka al’amarin ya zama, shiryawata da Ado sai ta haifar da al’amura masu yawa a ta vangarena dashi dai sai nake ganin tanfar ba a tava son wata ‘ya mace kwatankwacin irin son da Ado ke nuna yana yi min ba, ko kuma don ban tava sanin yanda son yake ba ne, ban kuma tava yin dacen ganin wacce ake son ba ne? oho. A tsakaninshi da Mama kuma abin ya qara cavewa har ya shiga zullumin shiga cikin gida da dai ace yasan in bai shiga ba ita ba zata zo ba to da ya rinqa daxewa bai shiga don maganganun ba su da daxi, to qa’ida ne kullum sai ta shigo da safe da daddare sannan a gabana ma gaya mishi take yi ba fa a kanta muka soma ganin yarinya takai budurcinta ba, duk ‘ya’yan xakina da kake gani ‘yanmata aka same su yauwa ba sabon ba ka tava mace ka haukace. To wannan ma har wata mata ce da za’a ruxe akanta? Yayin da itama Mama take wannan tashin hankali itama Inna nata sha’anin take yi, aike biyu tayi tana tambayar Ado ya bada lokacin da ya ga ya dace azo ayi min jere a sanya min kayana don mu ma mu ji daxin zama a inda muke, shi kuwa sai yayi murmushi ya ce a gayawa Inna tayi haquri kawai ta huta ai shi xin mace ya nema ya kuma samu an bashi, don haka ya gode da alherin da aka yi mishi maganar kaya kuwa a bar su ba shi da buqatarsu waxanda aka kawo mishi sanda aka kawo mishi matar shi sun ishe shi. Kusan sati biyu ne da faruwar abin da ya faru a tsakanina da Ado tun lokacin nan kuwa ban sake yarda ya tava ni ba, tun yana haqurin har dai na qure haqurin nashi, don haka akan dole jiya da daddare na haqura na qyale shi yayi yanda yaso, wanda ba ni da na ji a jikina ba shima yasan ba qaramin takura nayi ba. Amma duk da haka da gari ya waye na fito na kama ayyukana na gida, don dai in samar mishi da kwanciyar hankalin cewar bai qware ni ba, duk da ni kam nasan ya qware nin, ina sunkuye ina qarasa wanke wurin da nayi wanke-wanke ban san hawa ba ban san sauka ba kamar daga sama sai kawai naji saukar bulala a jikina da iyakacin qarfina na qurma ihu. Ina xaga ido naga Mama ne mai dukan, kuma na yanka da gudu na nufi xakina saboda neman mafaka, da saurinta ta biyo ni tana faxin “Ja’ira mai gadon raba zumunci, ai ni ba za a kawo min wannan iya shegen ba, a hanya muka gamu da Ado ya fito daga xakin cikin sauri daga shi sai gajeran wando Boxers fari sol, hannu ya saka ya tare ni ya hana ni shiga xakin ya maida ni bayan shi na tsaya, me ya faru Mama?” yayi tambayar cikin natsuwa duk da dai fuskarshi ta riga ta baiyanar da motsuwar zuciyarshi. “Kaga ja’iri mara kunya, a gabana ka ke tava ta?” tayi maza ta sake xaga hannu zata sharvo min bulalar ya tare
Chapter 15 · 0% Book details