Sashe 10
Mijin Ta Ce Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
aikawa kakata Mahaifiyar Baba abincina don kar ta tafi bata tava cin girkina saboda na yarda da maganar da Ado ya gaya min cewar yawan rai ne ya sata ganin auren nawa, don shekaru tamanin da huxu ke gare ta, bai kamata in bari ta tafi bata xanxani girkin nawa ba, tun da ban san randa zata sake zuwa ba. Na fara shirye-shiryen xora girkin kenan bayan na gama tsabtace wurin, sai Ado ya leqo cikin natsuwa ya ce min ko za ki yi ne har da mai babban allo? Ban tanka ba ya juya ya tafi, ga dukkan alamu dai ya ji daxin ganina a kicin xin, shawarar da ya bayar ta sanya ni faxaxa girkin sosai. Tuwon semovita nayi miyar kuka don a sanina tuwo shi ne abincin da yafi daxi yafi sauqin ci a wurin Hajiyar Giyaxe, to ko shima mai babban allon yasha gaya min cewar a dole yake cin wani abinci matuqar ba tuwo ba ne. Na kammala komai ya kuma yi daxi sosai, don wadatattun kaji na zuba a cikin miyar ina tunanin Inna gama in aika a gayawa Inna ta bani inda zan zuba abincin sai ga Ado ya shigo da su food flask har guda uku da wasu kwanukan silver masu murfi masu kyau set biyu da dinner set guda xaya. Nasa hannu na karvi wasu, wasu kuma shi da kanshi ya shigo ya ajiye su ya kuma koma gefe ya tsaya yana kallon yanda nake malmala tuwon ina naxe shi cikin leda ina ajiyewa cikin food flask da kwanukan da ya kawo. Wannan na waye? Ya buqaci sani ba tare da na kalle shi ba na ce mishi nasu Yaya Ibrahim, to wannan fa? Ya sake nuna wani, na gaya mishi na ce na Baba ga na Hajiyar Giyaxe da na gidan mai babban allo da ka ce a sa. To na Inna da Mama fa? Na ce ai wannan da na ce na Baba ne malmalar ciki na da yawa duk mai so sai ya xiba, ya ce to ya yi ina gama zuba miya nasa manshanu da yaji, Ado ya juya zai kira Yaya Ibrahim ya xaukan musu nayi maza nace mishi a’a bari shi zan je in kai musu jin haka da yayi ya sa shi xiban kwanukan a hannunshi yaje har xakinsu ya kai musu. Cikin zuciyata ni kam ina jin takaicin yanda Ado ke tafiyar da su Ibrahim duk da dai shi xin qanin mahaifiyarsu ne, to amma kuma na sani in banda su xin sun lalata kansu da shaye-shaye da qin karatu da zaman rashin sana’a babu yanda za’ayi ya rinqa yi musu haka. Koda yake akwai adawa mai yawa a gidanmu tsakanin ‘ya’yan wannan xakin da na wannan wanda nake ganin kamar Mama ce tayi dalilin aukuwar hakan, ko da yake dai Maman da kuma Babana suna faxin cewa wai Inna ta ce tayi sanadin faruwar komai to amma kuma hakan ba zai hana zuciyata sa min cewar Baba da Ibrahim dama duk wani xa da Mama ta haifa ‘yan uwana ne ba don haka ina jin ciwon rashin kintsuwarsu musamman da yake ‘ya’yan abokan Babana da yawa sun yi gaba sun bar su na kuma san Babana baya jin daxin hakan, iyaka dai ya kama bakinshi ya yi shiru ya zuba ido kamar yanda nasan shima Adon a farkon al’amarin nasu bai xauki al’amarin nasu da sauqi ba. Na sha jin shi yana kai qararsu wajen Baba kan suna shan wani abu bayan sigari, don haka ayi bincike a san abinda suke ciki don a san matakin da za’a xauka tun kafin abin yakai ga lalacewa. Daga ranar da na ji Mama tana tambayarshi ne a’a har da kai ma Ado da nake ganin kamar kai nawa ne zaka tsaya ka taya ni faxa da masu neman qulla musu sharri don su haxa su da mahaifinshi kuma kaima zaka shiga cikinsu? Ai ba a haka, ai ban kawo ka don kai ka samu shiga a wurin ubansu su kuma ka shiga tsakaninsu dashi ka vata ba, matsayinka daban nasu ma daban su ‘ya’ya ne, ya ce haka ne Mama nayi kuskure kiyi haquri daga ranar ne nasan ban sake jin bakin Ado yana magana kan abin da suke yi ba tun daga shaye-shayen, qin zuwa Makaranta, tarkacen abokai da kuma ‘yanmatan da suke kwasowa sai dai kuma a yanzu kam nasan ba ni kaxai ce na gane matsayin da Ado ya ajiye su ba, nasan Mama ma ta gane na kuma tabbatar ta fini jin zafin hakan to amma kuma ban san yanda aka yi ba taja bakinta tayi shiru tana kallo. Maimakon a wancan lokacin ne ya kamata tayi shiru ta bar Ado ya taya Babana sa ido akan ‘ya’yan nashi. Ado ya sake shigowa kicin xin yana tashe da Sa’adatu, “Nuna mata na Hajiyar Giyaxe in yaso na Baba da na mai babban allo sai ni in kai musu.” Na ce, “A’a in ka bar shi ma sai ta kai musu duka.”ya ce, “To bari ni da kaina in tambaye ta don kar ki xora mata abin da ba za ta iya ba, za ki iya Sa’adatu?” tayi murmushi tare da gyaxa mishi kai alamar tasan wasa yake mata, cikin zuciyata nace kai yaro kenan, wai har ta saki jiki da Ado bayan tsawon rayuwarta bata tava ganin yana wata mu’amalla da ita ba in ban da a ‘yan kwanakin nan. Sai da ta kai na Hajiyar Giyaxe ta dawo sannan na tambaye ta Babanmu yana ina ne ta ce xakin Mama, na ce to can za ki kai mishi, ta ce to. Na kammala komai nayi wanka tare da yin kwalliya mai kyau ta hanyar gyaran jikina sosai, sai dai ban sanya wasu kaya masu yawa ba, doguwar riga ce kawai baqa sai dai bata da nauyi ko kaxan, duk abinda nake yi Ado bina kawai yake yi da kallo sai da yaga ya gama komai har na nufi katifata ina shirin kwanciya shi ne ya tambaye ni. “Mu namu abincin fa, ba ki kawo mana ba kuma kina shirin kwanciya?’ na ce, ai ba ka ce in yi da mu ba, waxanda ka ce in yi wa girkin su na yi wa.” Ya ce, to babu laifi.” Na hau katifata na kwanta na jawo bargona mai laushi na ruhu yayin da Ado ke zaune kan kujerar ukun dake falo wacce a kwanakinnan, nan ya mayar wurin kwanciyarshi, ina jin shi yana daidaita tashar talabijin ta hanyar yin amfani da rimot kafin ya ji fitarshi kusan minti talatin kafin ya sake shigowa. “Humaira!” sau biyu ya kira ni kafin ya soma tambaya “Na dai san idonki biyu ba wani bacci kike yi ba, tunda da za ki ji motsina firgigit zaki yi ki tashi, ki fito nan muyi magana.” Na bi umarnin da ya bayar xin ba tare da na yi magana ba, gasasshiyar kaza na samu ajiye a gabanshi. “Zauna mu ci tunda ai ba zai yiwu ki kwana da yunwa ba ko?” na ce “Ai na qoshi.” Ya yi maza ya xago kai ya kalle ni, kina nufin ke kin ci tuwon kenan ni kaxai ne ba ki baiwa ba?’ na ce, a’a ban ci ba, ya ce zauna muci. Yasa wuqa ya raba kazar biyu ya turo min tawa yaja tashi nasa hannu zan xauka in tafi kamar yanda na saba yayi maza ya kama hannuna ya zaunar dani tare da faxin zauna a nan kici. Ai magana na ce miki zamu yi ina zaune ina kallon shi yana cin tashi kazar har ya gama ya xora robar ruwan swan ya tashi yaje ya wanke hanunshi yayi brush sannan ya dawo ya zauna yana hamdala sai da ya xan xauki lokaci kaxan kafin ya ce min ban fa shirya yin wasa da aurena ba Humaira, don haka ina ganin bai dace ace kina ta cutar da ni ba. Cikin natsuwa na tambaye shi, cutarwar me nake yi maka? Ban wani tsaya dogon bayani ba sai ya ce min, kina cutar da ni mana, ai kema kinsan komai tunda ke ba yarinya ba ce ‘yar qanqanuwa kin san abin da kike yi sarai, ban kalle shi ba na ce mishi to in ina cu tar da kai ba sai ka maida ni in da ka xauko ni ba? Ko kuma na menene damuwar? Kaima dama auren kwana casa’in aka ce maka kayi, to in kayi na kwanaki sha tara ai ka kyautata baka yi ta wahalar da ni ba balle in yi ta cutar da kai tunda itama mai auren dama ta ce maka tuni ya riga ya ishe ta.” A natse ya ce min, auren ai nawa ne kuma tun kwanakin baya sai na roqe ki cewar in muna magana to ta rinqa tsayawa a tsakaninmu mu biyu kar ta rinqa shafar ko da na qasa damu ne, balle na sama damu, na ce to a ma daina yin magana mana a rinqa qirgen kwanakin kawai zuwa lissafin casa’in xin.” Ya ce, a’a ba zan iya ba ba zai yiwu in yi ta zama da ke ina zuba miki ido kina zaune a gidana, nayi maza na xaga ido na kalle shi na ce mishi gidanka? Yayi maza ya ce min eh, gidana ne, na yamutsa fuska na ce, wai….bai bari na gama maganar ba yayi maza ya katse ni ta hanyar tambayata wai me? Faxi in ji qarasa abinda ki ke son faxan in dai har ke xin mara kunyar gaske ce.” Ban iya qarasawan ba ta hanyar furta kalma sai dai kuma ban bar shi haka ba murguxa mishi baki nayi, yayi maza ya cafke bakin nawa ya riqe da ‘yan yatsunshi ya matse tare da faxin mara kunya kawai wacce bata san rarrashi da ban baki ba tafi gane ayi tsiya-tsiya da ita tukuna. Washegari da sassafe ina zaune a tsakar gida ni kaxai duk da matsanancin hadarin dake haxuwa a garin wanda yayi dalilin tasowar iska mai tsanani cikin zuciyata tunani nake yi irin abinda ya faru tsakanina da Ado jiya da daddare, abin da na tabbatar kawia shi ne in ban da al’adar da ya gananwa idonshi a zahiri da babu abin da zai tsare shi daga yin abinda ya shirya xin.